Tinubu ya gana da shugaban EFCC da ministan gine-gine kan kadarorin da aka ƙwace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya karɓi ba’asi daga Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, Ola Olukoyede da Ministan Gine-gine da Raya Birane, Muttaqa Rabe Darma a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, ganawar ta mayar da hankali ne kan gudanarwa da soke amfanin gidaje da EFCC ta ƙwace a faɗin Nijeriya, kuma ita ce ta farko tsakanin Tinubu da Olukoyede tun bayan da shugaban ya soke hukuncin hukumar na sanya wa asusun gwamnatin Jihar Osun takunkumi.

Ofishin yaɗa labaran fadar ne ya fitar da saƙonnin da ganawar ta ƙunsa a wata takarda a ranar Talatar da kuma fitar da hoton zaman daga bisani a ranar. A cewar sanarwar, an gudanar da zaman ne bisa la’akari da kuma ƙoƙarin kiyaye ƙa’idojin tsare gaskiya da adalci, kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

Wannan na zuwa ne bayan cece-kucen takunkumin, wanda Tinubu ya gaggauta ba wa hukumar umarnin sokewa bisa la’akari da lokacin da aka aiwatar da ita na ana gab da zaɓen gwamnan jihar.

Ita dai EFCC a nata ɓangaren ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon zargin almundahanar zirga-zirgar wasu kuɗaɗen tallafi da na Kasafin Asusun Tarayya da adadinsu ya kai kusan Naira biliyan 11 a cikin asusun. Amma ita gwamnatin jihar ta ƙalubalanci matakin a wata takardar ƙorafi da ta gabatar wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ta soke hukuncin EFCCn da kuma biyan t diyyar Naira biliyan 2 na dameji.

A cewar Shugaba Tinubu, ya ƙi tsoma baki a harkokin EFCC a baya saboda kiyaye Hukunce-hukuncen doka, amma kuma tare da haka ba zai bar aikin wata cibiyar gwamnati ba ya yi mummunan tasiri akan sakamakon wani zaɓe ba.

Daga bisani, Gwamna Ademola Adeleke na jihar ya sake lashe zaɓen a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar AP, bayan doke Bola Oyebamiji na APC.

Zaman na ranar Talata tsakanin Tinubu, Shugaban EFCC da Ministan Gine-ginen na zuwa ne kwanaki uku da Adeleke ya sake lashe zaɓen Osun da kuma matakin janye ƙarar da gwamnatin jihar ta yi kan hukumar yaƙi da rashawan.

By Babaji

Leave a Reply