
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Harkokin Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ce akwai Dala miliyan 11.16 akan ƙasashen Togo, Nijar da Benin da Nijeriya ke bin su na bashin wutar lantarkin da kamfanonin raba lantarki na (GenCos) suka raba musu a shekarar 2025.
A rahotonta na shekara-shekara, hukumar ta ce sashen gudanar da kasuwanci (MO) ya gabatar da takardun biyan kuɗaɗen lantarki ga ƙasashen na jimillar Dala miliyan 73.91, amma Dala 62.75 ne kaɗai aka biya.
Rahotanni sun bayyana cewa, NERC ta zayyano ƙasashen a matsayin abokan hulɗar lantarki, waɗanda suka biya kaso 84.90 na ainihin kuɗaɗen lantarkin da aka raba musu. A cewar, hukumar kwastomomin kamfanonin sun biya jimillar Naira tiriliyan 12.75 a madadin tiriliyan N13.20 da sashen kasuwancin ya fitar na adadin kuɗin da ya kamata su biya na lantarkin shekarar.
Haka kuma, NERC ta ce kamfanin Ajaokuta Steel Co. Ltd da yankinsa ba su biya komai ba daga biliyan N4.96 da aka da kamfanin Nigeria Bulk Electricity Trading (NBET) ya tsara za su biya da kuma na takardar biyan miliyan N500 da MO ya fitar a lokacin.
A cewar NERC, jimillar wutar lantarki da kamfanonin DisCos suka samu a 2025 shi ne GWh31,251.77 yayin jimillar wadda aka raba kuma ya tsayu a GWh25,867.86.
