Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Kwamishinan ƙananan hukumomi da cigaban al’umma na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya buƙaci sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 11 da na yankunan cigaban ƙananan hukumomi (LCDA) 13 da su mayar da hankali kan muhimman buƙatun al’ummominsu domin samar da ci gaba mai ma’ana a yankunansu.
Kwamishinan ya yi wannan kiran ne a Bauchi a lokacin da yake yi wa shugabannin ƙananan hukumomin ƙarin haske kan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.
Ya ce ya kamata kowane shugaban ƙaramar hukuma ya fahimci abubuwan da al’ummarsa suka fi buƙata, sannan ya gabatar da su ga ma’aikatar ƙananan hukumomi domin a duba yadda za a samar da su.
A cewarsa, ya kamata shugabannin su fi mayar da hankali kan ayyukan da suke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a, musamman samar da makarantu, ruwan sha mai tsafta da kuma wutar lantarki.
“Ya kamata ku san abin da jama’ar ku suka fi buƙata, domin ku gabatar da shi ga ma’aikatar domin a duba yadda za a aiwatar da shi,” in ji shi.
Haruna ya yi wannan bayani ne gabanin gabatar da wata takarda da babban daraktan hukumar hadin gwiwar ayyukan gwamnati, Mahmoud Yusuf, ya gabatar kan tsarin haɗin gwiwar ayyuka tsakanin hukumomi da ƙananan hukumomi, wato Joint Project.
Kwamishinan ya shawarci shugabannin da cewa idan akwai wani muhimmin aiki da ya shafi rayuwar al’umma kai tsaye, za su iya miƙa buƙatar ga hukumar Joint Project ko gwamna, yayin da ma’aikatar za ta bibiyi lamarin domin tabbatar da an aiwatar da muhimman ayyukan.
Da yake gabatar da nasa jawabin, babban daraktan hukumar, Mahmoud Yusuf, ya bayyana cewa haɗin gwiwar hukumar da ƙananan hukumomi ba dole ba ne idan shugaban ƙaramar hukuma yana da damar gudanar da aikin da kansa.
Ya ba da misalin aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ake yi a ƙaramar hukumar Balanga, inda ya ce shugaban ƙaramar hukumar ne ya daɗe yana kai ƙorafin rashin wutar lantarki a yankin.
Ya ce sakamakon ƙoƙarin da aka yi, an fara aikin samar da wutar lantarkin, wanda yanzu ya kai wani mataki mai nisa.
Sai dai Mahmoud ya ƙarfafa wa shugabannin gwiwa da su rungumi haɗin gwiwa da hukumar, yana mai cewa hakan na ba ƙananan hukumomi damar aiwatar da manyan ayyukan da ba za su iya gudanarwa da kansu ba.
