Daga AISHA ASAS
Fitacciyar jarumar finafinan Kannywood Mansura Isah ta kai qarar Hukumar Hisbah ta Kano da kwamishinan ‘yan sandan Kano, inda ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke jihar.
Mansura wadda ta samu wakilcin lauyanta Barista Ibrahim Abdullahi Chedi, ya ce, ƙarar Mansura ta zo ne a matsayin mayar da martani kan zargin da ake mata na cin zarafin wata ƙaramar yarinya a wata makarantar firamare da ke jihar ta Kano, wanda ta bayyana ta dandalinta na sada zumunta, inda ta yi kira don gwamnati ta shiga tsakani.
Sai dai gwamnatin Jihar Kano, ta bakin Kwamishinan Ilimi Umar Doguwa, ta ƙaryata iƙirarin jaruma Mansurah, inda ta jaddada muhimmancin bibiyar al’amura ta kafafen yaɗa labarai maimakon kafafen sada zumunta.
Doguwa ya ja hankalin jama’a da su yi hulɗa da gwamnati kai tsaye, domin suna da damar da za su magance irin waɗannan matsaloli.
Game da kamun da Hukumar Hisbah da ‘yan sandan jihar za su yi, jaruma Mansura Isa ta gaggauta neman kotu, inda ta samu umarnin kotu da ya hana dukkanin ɓangarorin biyu kama ta har sai an warware karar da ake yi.
A martanin da babban daraktan hukumar Hisbah ta Kano ya mayar, ya ƙaryata zargin da Mansurah ta yi mata, inda ya bayyana cewa an gano iƙirarin nata na ƙarya ne bayan da hukumar ta gayyace ta domin yi mata tambayoyi.