Bayanan da suka iso mana yanzu daga jihar Filato sun ce, ‘yan bindiga sun kai ƙazamin hari ƙauyen Zurak da ke Gundumar Bashar District cikin ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40.
A cewar mazauna yankin lamarin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma yayin da jama’a ke gudanar da harkokinsu.
Sun ƙara da cewa, ba su samau damar sanar da abin da ya auku d wuri ba ne sakamakon rashin kyawun sabis a yankin.
Wani shugaban matasan yankin mai suna Sahpi’i Sambo, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar Daily Trust.
Inada ya ce, maharan sun dira ƙauyen ne a kan babura ɗauke da manyan bindigogi, sannan suka shiga harbi kan mai uwa dawabi.
Ya ƙara da cewa, “Sama da mutum 40 sun mutu, yayin da dama sun jikkata. Haka nan, nazauna yankin sun tsere don neman mafaka a maƙwaftan ƙauyuka,” in ji Sambo.
Sai ya dai, har zuwa kammala haɗa wannan rahoto, Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai ce komai kan batun ba.