Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarautu kwaskwarima bayan shan kiraye-kiraye kan a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi, wanda tsohuwar gwamnatin Umar Ganduje ta tsige.

Majalisar ta yanke shawarar yi wa dokar kwaskwarima ne bayan da Shugaban Masu Rinjaye, Hussien Dala, mai wakiltar Mazaɓar Dala, ya miƙa ƙorafinsa yayin zaman majalisar a ranar Talata.

An fara yi wa wannan doka kwaskwarima ne a 2019 bayan da ruwa ya yi tsami tsakanin gwamnan jihar na wancan loakci, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 14, Sunusi.

Sakamakon gayaran da aka yi wa dokar a wancan lokaci hakan ya haifar da samun masarautu biyar a Kano inda aka ƙirƙiro masarautun Rano da Karaye da Gaya da kuma Bichi.

Amma da yake dawo da tsigaggen sarkin kan kagara na ɗaya daga cikin alƙauran da Gwamna Abba Kabir ya yi wa Kanawa a lokacin da yake neman ƙuri’unsu, hakn ya sa ƙungiyoyi da dama a jihar suka jaddada kira kan a maido da Sarki Sanusi kan kujerar sarauta.

Idan za a iya tunawa, wata guda gabanin Gwamna ya shiga ofis, an jiwo shugaban jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na cewa za sake waiwayar batun masarautun jihar.