Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan Jihar Zamfara, a matsayin wanda ‘bai kammala ba’.

A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari’a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaɓen Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.

Ta ce, kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Jihar Zamfara, ba ta yi la’akari da hujjojin da masu ƙara suka gabatar ba, wato jam’iyyar APC.

Kotun ta kuma yi watsi da sakamakon da jam’iyyar APC da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC suka bayar na Ƙaramar Hukumar Maradun.

Don haka ta umarci hukumar INEC ta gudanar da sabon zaɓe a ƙananan hukumomin uku, inda ba a gudanar da zaɓe ba a baya, ko kuma ba a ƙidaya sakamakon wasu tashoshin zaɓe ba.

Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen watan Maris, Bello Matawalle ne sake ƙalubalantar hukuncin da karamar kotun zaven jihar Zamfara ta yanke, wanda ta kori shari’arsa bisa hujjar cewa ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji.

Tsohon gwamnan na Jihar Zamfara kuma Ƙaramin Ministan Tsaro, Matawalle, yana neman wa’adin mulki na biyu ne bayan ƙarewar mulkinsa na tsawon shekara huɗu.