Ya za ta kaya a shari’ar zaɓen gwamnan Kano?

*Yau Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke hukunci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta saka yau Juma’a, 17 ga Nuwamba, 2023, a matsayin ranar yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnan Jihar Kano ya ɗaukaka, inda yake ƙalubalantar soke nasarar zaɓensa da kotun zaɓen jihar ta yi kwanakin baya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya garzaya gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ne bayan kotun ƙorafin zave ta Jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba ta rushe nasarar da ya samu a babban zaɓen 2023, inda ta ce abokin takararsa na Jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen.

Kotun dai ta kafa hujjar hukuncin da ta yanke ne a kan ƙuri’u sama da 165,000 da ta soke daga cikin waɗanda Abba na NNPP ya samu ne, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zaɓe.

Jam’iyyar APC, ita kuwa ta roqi kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Gwamna Abba Kabir ya yi kuma ta tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun.

Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar na zuwa ne kwana 10 cif bayan alƙalan kotun da ke zama a Abuja sun saurari ba’asin dukkan ɓangarorin da ke cikin shari’ar tare da sanya hukuncinsu a mala, sannan suka ce za su sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.

Yanzu dai alƙalan sun tabbatar da cewa, a yau Juma’a ne za su bayyana hukuncin da suka yanke.

Wannan hukunci ba zai zamo na ƙarshe ba, domin duk wanda bai yi wa daɗi ba yana da damar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙolin Nijeriya, wacce hukuncinta shine na qƙarshe a matakin shari’a a Nijeriya.