Tattaunawa

Dalilina na kawo sauyi a Babban Asibitin Lafiya – Dr. Hassan

Dalilina na kawo sauyi a Babban Asibitin Lafiya – Dr. Hassan

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Dokta Hassan Ikrama shi ne babban Daraktan babban asibitin gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira asibitin ƙwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya, babban birnin jihar. A tattaunawarsa da wakilin mu ya bayyana yadda shirye-shiryen gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ke kawo ci gaba mai ma’ana a asibitin da sauran hukumomin kiwon lafiya a jihar da nasarori da kuma ƙalubalen da ake fuskanta a asibitin da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Yaya za ka kwatanta shirye-shiryen Gwamna Abdullahi Sule ta yadda suka shafi kiwon lafiya musamman a asibitin nan?Idan ana batun shirye-shiryen gwamnatin…
Read More
Tattaunawa ta musamman da Shugaban SMEDAN, Dr Dikko Umar Radda

Tattaunawa ta musamman da Shugaban SMEDAN, Dr Dikko Umar Radda

Mutum ne haziƙI wanda duk wanda ka tambaya shaida a kansa abu biyu yake faɗa na farko, mutum ne mai tsoron Allah sai kuma tausayi. Ya jima yana gwagwarmaya kan tallafawa al’umma da siyasa ba a iya Katsina ba a duk arewacin Nijeriya ba inda ba a ji da ganin tallafin Gwagware foundation ba. Jaridar Manhaja ta tattauna da Dr Dikko Umar Raɗɗa don jin me ne sirrin nasararsa da kuma abin da ya sa a gaba yanzu. Taƙaitaccen Tarihinka.Dr Dikko Umar Raɗɗa Gwagwaren Katsina shugaban ƙananan da matsakaitan masana’antu na ƙasa kuma shugaba na Gwagware Foundation wanda wannan gwagware…
Read More
Zan kai APC tudun-mun-tsira a 2023 – Yari

Zan kai APC tudun-mun-tsira a 2023 – Yari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhaji Abdul’aziz Abubakar Yari, wanda ya kasance jajirtacce ɗan siyasar Nijeriya ne kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, kuma tsohon shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya. Alhaji Yari ya kasace ɗan siyasa mai hangen nesa ne wanda ya sadaukar da kansa don inganta rayuwar mutanensa. A makon da ya gabata ya yi wata tattaunawa da wasu kafofin yaxa labarai a kan tsayawarsa takarar Shugabancin jam'iyyar APC mai mulki. A cikin wannan tattaunawar, Abdulaziz Yari ya bayyana aniyarsa ta gudanar da shugabanci mai ingancin, inda ya sha alwashin kai jam'iyyar ga tudun mun-tsira a zaɓukan 2023…
Read More
Har mai sayayya a yanar gizo na da damar kai ƙorafi hukumar kula da haƙƙin kwastoma a Kano – Hon. Nasiru Na’ibawa

Har mai sayayya a yanar gizo na da damar kai ƙorafi hukumar kula da haƙƙin kwastoma a Kano – Hon. Nasiru Na’ibawa

Hon. Nasiru Usman Na’ibawa shi ne Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kano na Musamman kan yadda hukumar Karota da Kwanzuma ke ciki a fagen yin ceto rayuwar al’umma daga halaka tun daga abin da za su ci ko su yi mu’amala zuwa titinan da suke zirga-zirgar yau da kullum. Ga yadda tattaunawarsa da Wakiliyar Manhaja, Bilkisu Yusuf Ali, ta kasance: Me za ka fara da shi game da Hukumar Karota ta Jihar Kano?Ita wannan hukumar ta Karota hukuma ce da aka kafa ta bisa doka tun a tsohuwar gwamnatin Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso wadda aka kafa ta kan raguwar…
Read More
Tsoffin hafsoshin Nijeriya: Ba ritaya ba ce, kora ce – Shehu Sani

Tsoffin hafsoshin Nijeriya: Ba ritaya ba ce, kora ce – Shehu Sani

Daga AISHA ASAS Sanata Kwamared Shehu Sani, tsohon ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta takwas, mutum ne wanda ya yi suna wajen faɗa wa gwamnati gaskiya komai ɗacin ta tun lokacin da sojoji ke mulkin ƙasar nan. Kuma ɗan gwagwarmaya ne sannan shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam, CRC. A wannan hirar da Manhaja ta yi da shi, ya nuna illolin da ciwo bashi kan iya jawowa, da kuma yin gugar zana ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan batun ritayar da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan su ka yi bayan yekuwar da jama’ar ƙasar…
Read More
Sarautar Dan Buran Gobir da aka ba ni gadon gidanmu ce – Aminu Alan Waka

Sarautar Dan Buran Gobir da aka ba ni gadon gidanmu ce – Aminu Alan Waka

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A farkon shekarar nan ne ta 2021 Sarkin Gobir Alhaji Isah uhammad Bawa ya nada shahararren mawaki Alhaji Dakta Aminu Ladan Abubakar Ala, a matsayin Dan Buran Gobir, wanda aka yi wani kasaitaccen bikin nadin sarautar a can Masarautar ta Gobir, kuma jama’a da dama sun halarci bikin.Bayan kammala shagalin bikin nadin mun tattauna da Aminu Ladan Abubakar Ala, domin jin yadda ya samu sarautar da kuma alakar sa da Masarautar Gobir in da ya fara da bayyana mana cewar: To yadda abin ya samo asali dai shi ne, ina da nasaba da Gobirawa, kuma…
Read More
Hanyoyin da gwamnati za ta inganta tattalin arziki da magance fatara – Shugaban Bankin Jaiz

Hanyoyin da gwamnati za ta inganta tattalin arziki da magance fatara – Shugaban Bankin Jaiz

Daga UMAR M. GOMBE ALHAJI HASSAN USMAN shi ne Babban Manajan Darakta na Bankin Musulunci na farko a Nijeriya, wato Bankin Jaiz. A wannan hirar da Mataimakin Editan Manhaja, UMAR MOHAMMED GOMBE ya yi da shi, qwararren masanin tattalin arzikin ya bayyana abubuwa da dama da suka hada da koma-bayan tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta da hanyoyin da za a magance su. Haka kuma ya yi tsokaci kan alfanun bayar da zakka da kuma gudunmawar da bankuna ke bayar wa ta fuskar inganta tattalin arziki, musamman bankunan Musulunci. MANHAJA: Ran ka ya dade, a matsayin ka na qwararre a…
Read More
Kalubalen da na fuskanta a aikin jarida – Madina Dauda Nadabo

Kalubalen da na fuskanta a aikin jarida – Madina Dauda Nadabo

Daga AYSHA ASAS HAJIYA MADINA DAUDA NADABO gogaggiyar ‘yar jarida ce wacce ta dade tana bayar da gagarumar gudummawa wajen dauko rahotanni da watsawa a sassan duniya, kuma qwararriyar ‘yar jarida wadda take nuna qwarewar aiki wajen gabatar da shirye-shirye masu ilimantarwa, nishadantarwa gami da zaburarwa. Manhajata yi hira da ita don jin gwagwarmayar ta a fannin aikin jarida kamar haka: Hajiya duk da ke ba boyayya ba ce wajen mutane, amma za mu so jin taqaitaccen tarihinki a taqaice. To, Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Madina Dauda Nadabo. An haife ni a Unguwar Shanu da ke cikin…
Read More
Babban buri na kafin in bar duniya… – Aunty Bilkisu Funtua

Babban buri na kafin in bar duniya… – Aunty Bilkisu Funtua

Daga Aysha Asas Wadanda suka dade da fara karance-karancen littattafan Adabin Kasuwar Kano tun wuraren 1993 ba shakka zan iya cewa sun sha cin karo da littattafan Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, wadda ake kira Aunty Bilki Funtua, domin ta kasance a sahun farko kuma tauraruwar da littattafanta ke ja a wancan lokacin. Saboda haka a tashin farko muka samu nasarar shigo muku da ita cikin wannan fili don jin wace ce ita, mene ne kuma burinta a halin yanzu sakamakon rashin jin duriyar littattafan ta a kasuwa na dogon lokaci. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance: Masu karatu…
Read More
Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Rashin tsaro na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya a yau. Abin ya kasance har kusan kowa ya sadaqar, an kasa kamo bakin zaren. A yayin da shugabannin yankin suke ta laluben yadda za a magance matsalar, da yawa kuma sun naxe hannu, sun haqura. Shin menene abin yi? Daya daga cikin dattijan Arewa da suke kwana suna tashi cikin tunanin yadda za a shawo kan al’amarin shi ne tsohon Gwamnan Jihar  Sokoto, kuma tsohon xan takarar zama shugaban qasa, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto), wanda har qasida ya tava gabatarwa ga takwarorin sa manyan yankin…
Read More