Dalilina na kawo sauyi a Babban Asibitin Lafiya – Dr. Hassan

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Dokta Hassan Ikrama shi ne babban Daraktan babban asibitin gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira asibitin ƙwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya, babban birnin jihar. A tattaunawarsa da wakilin mu ya bayyana yadda shirye-shiryen gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ke kawo ci gaba mai ma’ana a asibitin da sauran hukumomin kiwon lafiya a jihar da nasarori da kuma ƙalubalen da ake fuskanta a asibitin da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Yaya za ka kwatanta shirye-shiryen Gwamna Abdullahi Sule ta yadda suka shafi kiwon lafiya musamman a asibitin nan?
Idan ana batun shirye-shiryen gwamnatin jihar nan a fannin kiwon lafiya ne zan iya cewa ba shakka Maigirma Gwamna Abdullahi Sule yana tabbatar ya aiwatar da shirin gwamnatin tarayya a fannin kiwon lafiya ne anan jihar Nasarawa. Kuma yana da kyakkyawan shiri a vangaren. Kuma haƙƙi ne da ya rataya a wuyanmu a matsayinmu na muƙarraban sa, mu tabbatar mun aiwatar da waɗannan shirye-shirye. A wasu lokuta gwamnatin jiha takan yi koyi ne da shirin gwamnatin tarayya a fannin kiwon lafiya, a wasu lokuta kuma takan ƙirƙiro da nata shirye-shirye ne ta yadda ya dace da jihar nan da sauransu. Abinda gwamnati ke yi kenan a yanzu musamman ta fannin kiwon lafiya na sha-ka-tafi da gidanka da sauran manyan hukumomin kiwon lafiyar mu da sauransu a jihar nan baki ɗaya. Amma babban shirin gwamnati shi ne ya tabbatar an samu ingantaccen kiwon lafiya a kuma farashi mai sauƙi wa al’ummar jihar nan bakiɗaya, don bai kamata a ce jama’a ba sa iya samun ingantaccen kiwon lafiya saboda rashin kuɗi ba. Haka kuma a nan asibitin ƙwararru na Dalhatu Araf muna ƙoƙari ne wajen yin koyi da abinda mai girma gwamnan ke yi a fannin don jama’a su samu kiwon lafiya ingantacce a kuma farashi mai sauƙi. Kuma muna inganta  ayyukan kiwon lafiya anan ta tsarin gwamnatin jihar nan. A da idan an fuskanci matsalar rashin lafiya mai tsanani akan tura babban asibitin ƙasa ne da sauransu. Amma a yanzu muna ƙoƙari ne mu canja lamarin tunda muka zo musamman ta inganta kayayyakin mu anan da ma’aikatanmu da sauransu. Muna kuma rage almubazzaranci kuma zan iya cewa muna samun ci gaba matuƙa a ɓangaren kawo yanzu.

Waɗanne irin ƙalubale kuke fuskanta a asibitin nan tun zuwan ka?
Kamar yadda ka sani wani abu mai wuya a rayuwar nan shine canji, mutane sukan ƙin amincewa da canji a koyaushe. Misali idan suka saba da wani abu sai ka zo ka ce za ka canja wannan abu, ka ga dole ne a samu matsala ta haka. A da ana gudanar da harkokin asibitin nan ba bisa ƙa’ida ba amma a yanzu muna ƙoƙarin canja lamarin ne ta yadda ya dace. Misali halin ma’aikatan mu ga marasa lafiya shine babban ƙalubale da muke fuskanta. Mutum zai zo ba shi da lafiya sai ka zo kana masa ihu baka biya masa buƙata ba maimakon haka sai kana cin masa mutunci. Hakan yana ƙara masa damuwa ne maimakon magance shi. Muna tabbatar mun canja ra’ayin ma’aikatan mu a wannan ɓangare. Muna so su fahimci cewa mara lafiya tamkar sarki ne da ke buqatar kulawarsu a iya zamansa anan. Saboda sanadiyyarsu ne ake biyanmu albashi da sauransu. Abu na biyu kuma shi ne batun rashin nuna gaskiya da riƙon amana da batun almubazzaranci da cin hanci da rashawa da sauransu. Akan haka ne ma ya sa da zuwana na ƙirƙiro da wani shiri na musamman wato na yin amfani da wata na’ura ta musamman da ke rakodin duka abubuwa da ma’aikacin asibitin nan ke yi a duka ɓangarorinmu a nan inda ake gudanar da ayyuka ba bisa ƙa’ida ba. Kodayake yawancin ma’aikatanmu suna gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana, amma akwai wasu ɓatagari ƙalilan cikinsu da ke hana ruwa gudu. Ire-irensu muke ƙoƙari mu daƙile ayyukan don samun ci gaba a asibitin nan kamar yadda ake buƙata. Saboda haka a taqaice babban qalubale da muke fuskanta anan kenan wato rashin aminci ko rungumar canji daga waɗanda suka saba da ayyukan ta’asa a asibitin nan. Amma a hankali muna shawo kan lamarin.

Waɗanne nasarori kuma asibitin nan ta cimma a shugabancin ka?
Ba shakka mun samu ɗimbin nasarori kawo yanzu da zuwa na da suka haɗa da ƙarin ingantaccen kayayyakin aiki da yawansu a duka ɓangarorin kiwon lafiyar mu anan. Sauran sun haca da kayayyakin fannin aikin tiyata da hakan kan rage lokaci da marasa lafiya ke jira likita da sauransu. A yanzu muna da likitoci da ke kula da cututtuka da suka shafi zuciya da a da ba su da mashinan da ke kula da su, ba su kuma da isassun likitocin. Muna da isassun kayayyakin kuma a ɓangaren yara ƙanana akwai na’urori na musamman da muka sayo musu a fannin don kula da musamman jarirai da aka haifa cikin kwanaki ƙalilan. Na zo na taras da kayayyakin ba sa aiki, amma a yanzu suna yi kuma mun sayo sabbi. Za a iya zagaya da kai idan kana da lokaci don ka ganewa idanunka waɗannan abubuwa da nake bayyana maka. Kuma a yanzu muna da kimanin na’urorin gwaje-gwaje na zamani guda 6 a shiyyoyi 6 anan. Kuma a yanzu asibiticin ƙasar nan da ke da ire-irensu ba su da yawa. Saboda haka tunda na zo kawo yanzu zan iya cewa mun kawo canji a kusan duka shiyyoyinmu yadda ake buƙata kuma za mu ci gaba da yin haka har sai haƙarmu da burin gwamnatin Injiniya Abudullahi Sule na samar da ingantaccen kiwon lafiya a ɗimbin al’ummar jihar nan a kuma farashi mai sauƙi ya cimma ruwa.

Ko ka na da wani saƙo na musamman ga al’ummar jihar nan bakiɗaya?
Ka san wani lokaci idan kana so ka kawo canji sai a hankali kamar dai yadda na bayyana a baya. Kamar yaro ne ƙarami idan kana matsa masa maruru zai yi masa zafi a lokacin amma idan ka gama zai samu sauƙi. Saboda haka jama’a su yi haƙuri su bi mu a hankali don muna ƙoƙarin inganta harkokin asibitin nan ne ta yadda za su more shi. Shi ya sa a wasu lokuta sabbin shirye-shiryenmu suna da wuya ga al’umma da ma wasu ma’aikatanmu a yanzu, amma a ƙarshe kowa zai amfana da su ba shakka. Kuma mun sha alwashin inganta harkokin asibitin nan fiye da yadda muka tarar da shi. Ina kuma so in yi amfani da damar nan in sanar wa al’ummar jihar nan da duniya bakiɗaya cewa a yanzu mun kuma fara horar da ma’aikatan mu na musamman don su zama masu ba da shawarwari na musamman akan batuttuwa da suka shafi kiwon lafiya da sauransu. Kuma kafin ka iya yin haka dole sai hukumomi da ke tantance waɗannan shiyyoyinmu sun tantance ka. Kuma tuni muka gayyace su sun zo sun tantance duka shiyyoyinmu kafin muka fara gudanar da horarwar. Na gode.