Wani matashi ya halaka mahaifiyarsa saboda abinci

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan kimanin shekara 25 a duniya, Solomon Ochadi, a gaban kotun majistire da ke zamanta a Ibadan, bisa zarginsa da halaka mahaifiyarsa, Elizabeth Ochadi.

Rahotanni sun nuna cewa, rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da manomin matashin ne kan zargi ɗaya tacal, na kisan kai. Ƙaramin sufetan ‘yan sanda, mai gabatar da ƙara, Opeyemi Olagunju, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin ya ingiza mahaifiyar tasa ne cikin rijiya.

Ya ƙara da cewa, hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matar ‘yar kimanin shekara 50, wacce take uwa a gare shi, a cikin rijiya.
Da yake faɗa wa kotu yadda lamarin ya faru, mai gabatar da ƙara na rundunar ‘yan sanda ya ce, wanda ake zargin ya nemi abincinsa daga mahaifiyar tasa ne bayan ya dawo daga gona.

Ya ce, “Matar ta shaida masa cewa babu abinci a gidan. Ba zato sai ya ingizata cikin rijiya saboda fushi da amsar da ta ba shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.”

Olagunju, ya ci gaba da shaida wa kotu cewa, bayan ya kashe ta, Solomon ya nemi wuri a bayan gidansu ya yi wa gawarta qabari. Ƙannen matashin, da suka ganewa idonsu abinda ya faru, su ne suka sanar da ‘yan sanda, kuma aka cafke wanda ake zargin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Majistire Olaide Hamzat, ya ce, kotu ba ta da hurumin yanke hukunci kai tsaye, domin akwai buƙatar a gudanar da bincike. Bisa haka ne ya bada umarnin a kai fayil ɗin da kuma shaidu zuwa hukumar zartar da hukunci domin shawarwari kuma ya ɗage zaman zuwa 23 ga watan Nuwamba.