Kisan ‘ya’yan miji tsagwaron rashin imani ne

Daga SADIYA GARBA YAKASAI
 
Ga mu kamar kullum yau ma ɗauke da shirinmu mai albarka.
Yana da kyau mu taɓa wannan matsala da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa. Duba da yadda abubuwan ke ƙara bunƙasa, maimakon a samu sauƙi, sai ga shi mata suna daɗa bazama a kan rayukan yaran abokiyar zamansu ko na ce yaran mijinsu. Wannan rashin imani yana neman zama wani abu. Kamar a ce mace ce da aka sani da son yara da tausayawa, amma sai yanzu idanunsu ya rufe su manta da tarbiyyar da iyaye suka ba da.

Imani:
Imani wani abu ne da duk Musulmin arziki yake tutiya da shi, kuma imaninmu ba ya cika sai ka so wa ɗanuwanka abinda ka so wa kan|ka. Me ya sa ba ma tunanin mutuwa ne? Me ya sa muka saka son zuciya da rashin imani a zukatanmu, muke ɗaukan ran yaran da ba su san komai ba? Don me za ki ɗauki ƙiyayyar da kike wa uwarsu ki ɗora a kan yaran mijinki? Anya masu wannan ɗabi’a ɗin kuwa suna tuna mutuwa da hisabi?

Mazaje suna ina ne ake girbe yaransu da sunan kishi? Wannan abun da ya kamata hukuma ta sa baki ta dinga ɗaukan manyan horo a kan duk macen da ta kuma irin wannan rashin imanin.

Kishi:
Halitta ce da Allah ya ɗora wa mace, amma ba irin wannan na dabbaci ba. Ba irin wannan na mugunta ba. Tunda ke ba za ki iya kashe naki yaran ba, amma za ki iya kashe na wata ya zama mugunta. Yana da kyau ki tuna Allah ne Ya halicci kowa. Ba mu da hurumin tsara wa kowa rayuwa idan ba Allah ba. Rashin ilimi ne ke sa wannan abun da rashin tunani. Ka iya zuwa ka sayi guba ka zuba wa yaran da ba su san komai ba, su mutu. Ko ki ɗauki makami ki kashe su,  kamar babu zuciya a jikinki, wannan masifa har ina?

Akwai tausayi, akwai abin kunya. Yanzu shin mu mata a kan ɗa namiji mu iya aikata irin wannan rashin imani? Abun takaici ne a gurinmu mata. Ta yaya za mu dinga manta sunanmu na iyaye abun koyi, muna cusa aikin shaiɗan cikin zuciyarmu muna aikata ɓarna. Su yaran wai meye nasu a ciki? Ki yi wa mijinki kowacce aka aura mana. Ki ga idan za ki ci riba. Wallahi mu ji tsoron Allah, mu sake yaƙin rayuwa, rai fa ba abin wasa ba ne. Yadda muke jin daɗinsa, bai kamata ki raba wani da nasa ba.

Haƙuri:
Wani abin koyi ne da tun zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yake, kuma shi ya ce mu yi koyi da shi. Bai ce mu kashe ba, haka matansa sun yi kishi amma ba irin namu ba. Nasu mai tsafta ne, nasu abun koyi ne ta yadda kowacce za ta burge mijinta. Haka ya zo kan kakanninmu da iyayenmu, sun san yadda suke kishinsu. Amma mu son rai ya sa mun manta komai ya kai da kisa. Wa’iyazubillahi mata don Allah me yake samun mu ne haka? Ba wanda ya ce kishi kar mu yi. Amma na nutsuwa ba irin wannan na hauka ba.
Kashe yaran miji ba haƙƙinsu, a kashe mazaje ba haƙƙin su, kawai don sun yi abinda aka halatta musu. Ina za ki kai.

zunubin kanki?
Ita dai rayuwa ƙalilan ce, ba kuma mun zo ta mu yi yadda muke so ba ne. Idan haka ne, da ba a mutu ba, kwata-kwata. Muke fahimtar rayuwarmu kaɗan ce. Ba mu san sanda za mu mutu ba. Don ba a rubutawa ka gani. Da ana yi, da kowa ba zai aikata abin mugunta ba, saboda sanin abinda za mu tadda. Kowa burinsa yanzu yadda zai samu duniya, ba yadda zai samu lahira ba. Da za mu ga abinda ke jiran mu, da kowa ya bar aikata mugun abu. To ina! Allah ya yi alƙawarin kowa sai ya girbe abinda ya shuka. mai kyau da mara kyau. Don haka, mu ji tsoron Allah, mu tuba.

Duniya mai abun mamaki ruɗunta na da yawa. Dubban mata da yawa suna afkawa  halaka. Idan ba ki son mijinki ya yi aure, nemi sallama mana, ba sai kin ɗibar wa kanki abin fa]a ba. Har yaranki da iyayenki, kin wa kanki baƙin fenti da ba zai goge ba, har lahira. Gwara kin fita, kin bar shi da yaransa.

Ba mu da rayuwa ne mata sai ta kisan yaran miji, ko mazan kansu. Wacce riba ce za ki samu ne idan kin kashe kishiyar ki ko yaranta? Ke meye taki makomar don Allah. Shi dai aure ba abin wasa ba ne. Kuma abu ne da Allah ya halatta, ya ce a yi. Don me mu mata za mu haramta. Yanzu idan da mata muna da tunanin yadda komai na rayuwa ya canza, wallahi za mu yi karatun ta-nutsu mu nemi sana’a ba mu zauna muna haukan kishi ba.

Mu tuna su ma Allah ne ya halicce su. Kuma yadda kika yi aure, su ma Allah ne ya ba su dama, don me ke za ki haramta?

Maza don Allah ku sa ido a kan yaranku da kuka saki iyayensu, kuka bar su a hannun matanku na baya. Yanzu fa ba kowacce mace ce take da imanin riƙe yaran kishiya ba, sai mai imanin gaske.

Shi sakin ma in bai zama dole ba a haƙura mana, a bar yara da iyayensu mata su ma su ji da]in iyayensu. A  bar yara da kishiyoyin iyaye suna gana musu azaba, daga baya su kashe su ina dalilin wannan masifa ne?

Shi ɗa da ba’a san wa zai more shi ba. Don me yanzu iyaye maza suka cika saurin fushi ne? Abu bai kai ya kawo ba, sai a auna mace gida. Ba a duba yaran da ta bari. kawai burin namiji ya saki, ya kawo wata. Kuma shi bai san wanne irin zama yaran suke yi da matar ba. Wata ma mugunta za ta tafka wa yaran, amma da uban ya dawo, za ta katantane ta zabga sharri, ta ce yaran suka yi shi. Shi kuma mai mata, sai ya hau kai ya zauna. Ya rufe yara da bugu ko masifa, ya kora su waje ko cikin ɗaki, da sunan hukunci. Bai san ya daɗa ba wa matar damar cusguna musu yake ba. Da me yaran za su ji? bai duba ma sun ci abinci ko ba su ci ba, kawai shi abun da matar ta faɗa, shi ne daidai.

Wani sa’in ma mazan na da laifi, naci, da son iyawa. Ka faɗa wa mace za ka yi aure, daga take-takenta za ka san idan za ta iya. Wata ma da kanta za ta gaya maka gaskiyar abun da za ta yi. Sai ka yi wasarairai da abun har abu ya zo ya ɓaci.

Ta haka ake samun yara baragurbi su zama ‘yan shaye-shaye, ba karatun boko, ba islamiyya, ta yaya rayuwa za ta fara maka dai-dai? Wanda ka haifa ba ka ba su kulawa ba, kuma ka koma ka sake wani auren. Ita ma wasu yaran za ta kwantsamo maka. Iyaye muna da da aiki a gabanmu, wallahi. Gwara mu farka daga nauyayyan baccin da muke ciki.

Allah ya sa mu gane kuma Allah ya tsare mu da imaninmu. Mu haɗu sati na gaba. Ma’assallam.