Ganawar Kannywood da Hukumar NDLEA faɗuwa ce ta zo daidai da zama – Dr. Sarari

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Masana’antar fina-finai ta Kannywood a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN, sun tsara wani haɗin gwiwa da Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi domin magance matsalar da ta ke yaɗuwa a tsakanin matasa a ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar ta MOPPAN Dakta Ahmad Sarari ne ya bayyana hakan ga wakilin mu bayan wata ganawa da ‘yan fim ɗin su ka yi da Shugaban Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin na ƙasa, Janar Muhammad Buba mairitaya.

Dakta Ahmad Sarari ya bayyana mana cewar, “zaman da muka yi da shugaban wannan Hukumar, lamari ne da za mu iya cewa faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama, saboda a wannan lokacin dai hajar Kannywood ta shiga kowanne gida kuma ta na yawo a kan kowace waya, wanda kuma a dai-dai wannan lokacin ne kuma yanayin shaye-shaye na miyagun ƙwayoyi da abubuwan maye su ka ta’azzara.

“Don haka shi kuma wannan shugaban Hukumar ya ga ya kamata a haɗa da harkar nishaɗi wajen wayar da kan mutane dangane da abin da ya shafi faɗakarwa a kan wannan aiki na hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. Wannan ya sa muka zauna da shi don tsara yadda za mu taimaka wa tafiyar.”

Ya kara da cewar “Abu ne mai muhimmanci mu shiga wannan fafutukar domin harkar mu ta matasa ce, kuma kamar yadda shi Janar Buba Marwa ya yi bayani a gidan gwamnati, ya ce kusan duk mutum ɗaya daga cikin mutane shida na mutanen Jihar Kano ya na shan ƙwaya.

To ka ga kusan a kowanne gida kenan akwai mai shan ƙwaya, in kuma haka ne mu kuma muna nan a kowanne gida, don haka za mu haɗa kai domin magance matsalar, mun sani Malamai suna iya na su ƙoƙarin, amma ba kamar yadda su jaruman fim za su yi ba, don su za su shigar da saƙon su ta hanyar waƙoƙin su da fim ɗin su, wanda ya shiga kowanne gida.

Don haka ta wannan ɓangaren mu ke ganin za mu samu haɗin kai ga su matasan, kuma in sha Allahu za mu sake zama da ita hukumar domin gabatar da kwamitin da muka tsara, wanda shi shugaban hukumar ya ce mu samar da kuma rubutun da za a yi amfani da shi wajen isar da saƙon, wanda kuma zai samar da abin yi ga su ‘yan masana’antar.

Kuma a yanzu kowa ya san harkokin mu na isar da saƙo sun ƙara faɗaɗa ne, domin akwai fina-finan da mu ke yi na gidajen Talbijin da na ‘YouTube’ da kuma hanyoyin ‘Facebook’ da sauran su. Yanzu idan ka ɗauki fina-finai masu dogon zango da a ke yi waɗanda a ke sakawa a ‘YouTube’ kamar ‘Izzar so’, ‘A duniya’, :Labarina’, to ka ga duk hanyoyi ne na isar da saƙo ga matasa, don haka su za mu yi amfani da su mu rinƙa saka saƙo a ciki wanda kuma saƙon ba sai ya fito ƙuru-ƙuru ba, don haka mu na da hanyoyin isar da saƙo masu yawa da jama’a su ke kallo wanda za mu iya isar da kowanne saƙo.

Mutane su gane masana’antar fina-finai ta Kannywood, babbar masana’anta ce da za ta iya wayar da kan jama’a da faɗakar da su a duk wasu fannoni na rayuwa, don haka duk wanda ya ke ganin ya na da wata haja da ya ke son duniya ta sani to ƙofar mu a buɗe take wajen isar da saƙon, amma za mu so samun haɗin kai da gwamnonin jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya domin samar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar mu.

Don haka muna fatan wannan haɗaka da muka yi za ta samar da yanayi mai kyau da zai kawo ƙarshen matsalar shaye-shaye, musamman a tsakanin matasan mu.”