Shekaru 61 da ‘yancin kan Nijeriya: Na ji daɗin tuƙa Sardauna – inji direbansa, Aliyu Shehu Maradun

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD

Alhaji Aliyu Shehu Maradun ɗan uwa kuma direban Marigayi Alhaji Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), ya zanta da Manhaja dangane da gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Alhaji Aliyu Shehu Maradun yana daga cikin Direbobin Sardauna kuma shi ma jinin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne. Amma sunan mahaifinsa shi ne Ahmadu Marafa Makwashe ya yi hakimcin Maradun tsohuwa. Don hake me yake yin amfani da sunn mariƙinsa, kuma kawunsa. Ya yi makaranta a Maradun da kuma Ƙwatarkwashi.

Sarkin Musulmi Abubakar Atiku ne ya tura ɗansa Sarkin ‘Kayan-Maradun Muhammadu Mu’alaidi don ya yi sarkin garin. Sarauta ce mai daraja ta ɗaya a jihar Zamfara. Dalilin da ake cewa ‘Kayan-Maradun shine da ‘Kaya sarki yake kafin aka mayar da shi Maradun. Kuma Sarkin ‘Kaya Muhammadu Moyi kakana ne, sannan wanda ake yi wa waqa ana cewa, “…Jikan Moyi Iro ɗan Mamman…” Amma Mahaifina ya yi hakimcin tsohuwar Maradun. Bani da sarauta a Maradun, amma na nemi Ɗan-Galadiman Magamin-Diddi amma ban samu ba.

Alhaji Sani Dingyaɗi ya rubuta wa Jami’in ilmi na lardin Sokoto, Alhaji Ismaila Ahmed, Dallatun Zazzau suka yi jarabawar tantancewa mu 75. An ɗauke shi da Abdulkadir Ƙaura aka kai su gidan Gwamnati da ke Sokoto. Aka sa wani Direba mai suna Na-Ma-Dawo ya kaisu Kaduna.

Sun yada zango suka kwana a Gusau, da ƙarfe bakwai daga garin Maska ba kwalta har Funtua sai ƙarfe biyu washe gari suka isa Kaduna. Watau sun kwashe awanni ashirin da huɗu ko kuma kwana zuwa Kaduna a tafiyar mota da tuƙi da hankali irin na Direbobin da.

Bayan watanni huɗu nacci jarrabawa na sami lasisi, sannan aka kaini koton gyaran Mota inda nayi wata huɗu sannan aka ban mota na fara tuƙi a Gidan Sardauna a ƙarƙashin Marigayi Ali Kwarbai, Sarkin Motan Sardauna.
Aka yanka min albashi fam goma sha ɗaya da sule goma.

Dattijon ya ce, “a Lokacin rangaɗi, Sardauna na son ya zauna a fili yana ganawa da jama’a. Ba zan manta ba, watarana a Gusau akwai filin ’yan doka inda suke fareti, nan aka shimfiɗa masa dadduma da kujeru, mu kuma muka zauna a kusa da shi.

“Kafin mu nufi gonarsa da ke Bakura, sai Sarkin Ƙayan Maradun, Muhammadu Tambari sa ganni kusa da Sardauna, ya ce yana son gani na.

“A wannan zamani, Sarakuna na garin da zai bi suna yin tarba a farkon ƙasarsu, sannan su yi sallama a iyaka.

“A gonar Bakura be Sarkin Kaya ya shaida wa Sardauna cewa ni jikansa ne, kafin nan ni ban sani ba sam-sam. Sai ya ce wa Ali Sarkin Mota ka kula dashi a matsayin ɗanka, ya ce, ka lura da shi in ta kama ka ladabtar da shi.”
Alhaji Maradun ya fara aiki da Sardauna a 1964, ya zama ɗan cikin gida sosai.

Bayan an kafa gwamnati, manyan ‘yan jam’iyar NPC suna taro a Kaduna, sai Sardauna ya dawo rai a ɓace, sai na tambayi Ɗanmagyazo, Direban Mamman Nasir Galadiman Katsina, Ministan shari’a ya ce, Ministan Tsaro Muhammadu Ribadu ne ya rasu a Ikko, watau Legas.

A lokacin Firayi-Minista Abukakar Tafawa Balewa yana Kaduna wurin taron, sai Sardauna ya hau jirgi zuwa Legas don ɗauko gawar Ribadu. Ina falon gidan Sardauna sai Alhaji Tafawa Balewa ya iso, na buɗe masa ƙofa, ya tambaye shin ko Sardauna ya dawo, sai nace a’a, sai ya koma masaukinsa a daf da Unguwan Shanu, inda ya zama ofishin Jama’atu Nasril Islam wanda ke tsakanin Ma’aikatar Ƙasa ko KAGIS da ginin KIFC a Kaduna.

Dattijon ya ƙara da cewa, Sarduana ya dawo daga Umura a kasar Saudiya, sai a cikin azumi ya sauka ranar Laraba a Kano inda Ali Sarkin Mota, da Saidu Bidda da ni muka je ɗauko shi.

Aliyu Shehu Maradun ya ce, a waƙar da Alhaji Musa Ɗan Kwairo Maradun yayi wa Sarkin ‘Kayan Maradun, yana cewa, ” Ahmadu ya zo Hausa…” Watau Kaduna, watau bayan ya baro Rigachikun aka kawo Alƙur’anai da carbi da atamfofi da kuma alawayyo aka raba wa masu shiga musulunci da sauran jama’a.

Bayan mu koma an rufe Tafsiri a masallacin Rigachikun inda yake yin sallar Juma’a kafin a gina Masallcin Sultan Bello a Unguwar Sarkin Musulmi sai Samuel Akintola Gwamnan jihar Yamma ya bugo masa waya, ya ce, akwai magana da yake son yi masa amma muhimmiya ba ta waya ba, zai zo Kaduna, ya aiko masa da mota gobe washegari da safe Juma’a a ɗauke shi a filin jirgin sama na Kaduna.

Alhaji Hassan Lemu ya jagorance mu zuwa tarbo shi Amma wata Mota kirar Land Rover na bin mu ɗauke da Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu. Akintola ya shaida wa Sardauna cewa za a yi juyin mulki kuma za a kashe su, su gudu, Sardauna ya ce ba inda za shi, sai dai a kashe shi.

Ashe Sardauna ya sami takarda cewa za a kashe shi ran juma’a. Alhaji Maradun ya ce, bayan sallar Magriba ya je yin barka da shan ruwan da fadanci, sai mutane huɗu suka shigo da Ali Akilu, M.D. Yusuf, Birgediya Ademulegun da Yusuf Balanta.

Ya ce, da ƙarfe 2 matarsa ta tashe shi ta ce an yi harbi, sai na fara jin harbi, da safe Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya je ya cewa Chukwuma Kaduna Nzeogwu ya ce, suna son yi jana’izarsa, da kyar ya yarda aka yi sallar jana’izarsa da Matarsa Hafsatu a ƙofar gidan Sarkin Argungu bayannan aka binne shi a gidan Sultan da ke Unguwar Sarkin Musulmi a Kaduna.

Wane wasiyya ya bari?
Ya bar wasiyyar in ya rasu a binne shi a garin Wurno bayan kabarin kakansa Sarkin Musulmi Muhmamdu Bello daga yamma, amma da ya ke gari ba lafiya, sai aka binne shi a Kaduna.
Ban san ɗan tawaye Nzeogwu ba, amma Sarkin Mota ya san shi, domin Sardauna ya sanya shi cikin aikin soja amma ya ci amanarsa. Inda shi Nzeogwu ya mutu a wulaƙance.
An mayar da ni aiki a Gidan gwamnati da ke kawo, ‘yan watanni, sai muka koma ‘state house’ da ke Kawo, sannan aka mayar da ni Ma’aikatar sadarwa aka koya min yin majigi, sannan na koma aiki da gwamntin jihar Sokoto ran 19 ga watan octoba a 1989, da aka kafa jihar Zamfara, sai Maradun ta faɗa jihar Zamfara, sai na koma can. Na yi ritaya a 1991.
Adireshin gidan shine lamba G11, layin G, Polo Club layout, Sokoto, rukunin gidaje 54. Ana son a sayar da gidan ne kan Naira miliyan biyu da rabi a biya cikin watanni. Ina da fansho Naira dubu shida da ɗari bakwai da biyar da kuma kobo shida ko wane wata (N = 6,705:06).

Ko kana da alaƙa da iyalin marigayi Sardauna da na Abubakar Tafawa Balewa?
Ƙwarai don muna zumunci da Goggo Aisha, ɗiyar Sardauna, ita ta haifi Magajin Garin Sokoto, da Hajiya Lubba wacce ta na ciki wata biyar ya rasu, matar Marafan Sokoto, Alhaji Umaru Shinkafi, da jikoki kamar su Hajiyayye, ‘yar Sarkin Bichi kuma Wamban Kano da ta auri marigayi Shehu Kangiwa, da Yakubu Tafawa Balewa, da Binta Tafawa Balewa. Idan na je bauchi, a gidan Tafawa Balewa na ke kwana mu yi ta fira ana juyayi.
Abin takaici shi ne an so a wulaƙanta ni matuƙa, domin an so a tashe ni daga Gidan da na ke wai ni ba ɗan jihar Sokoto ba ne, Amma Allah ya sa wata ta biya kuɗin Gidan saura kimanin dabunnai ya zama mallaki na.
Alhaji Maradun ya ce, “Mutuwar Baba Alhaji Ali Kwarbai, Sarkin Motan Sardauna ya kaɗa ni matuƙa, don ya ɗauke ni kamar ɗansa. Kuma har yanzu muna zumunci da Hajiya Binta Abubakar Tafawa Balewa, ɗiyar marigayi aminin Sardauna.”


Shawarata ga ‘yan baya shi ne su riƙe gaskiya, komin daɗewa za su yi nasara. Su kuma masu jagorancin jama’a su ɗauki halin dattako irin ta marigayi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto. Ina addua’ar Allah ya yi gafara ga magabatanmu da mu baki ɗaya. Amin.