Zan kai APC tudun-mun-tsira a 2023 – Yari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alhaji Abdul’aziz Abubakar Yari, wanda ya kasance jajirtacce ɗan siyasar Nijeriya ne kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, kuma tsohon shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya. Alhaji Yari ya kasace ɗan siyasa mai hangen nesa ne wanda ya sadaukar da kansa don inganta rayuwar mutanensa. A makon da ya gabata ya yi wata tattaunawa da wasu kafofin yaxa labarai a kan tsayawarsa takarar Shugabancin jam’iyyar APC mai mulki. A cikin wannan tattaunawar, Abdulaziz Yari ya bayyana aniyarsa ta gudanar da shugabanci mai ingancin, inda ya sha alwashin kai jam’iyyar ga tudun mun-tsira a zaɓukan 2023 mai zuwa. Akwai bayanai masu ilimantarwa a siyasance cikin wannan tattauanwa.  Ga cikakkiyar tattaunawar nan kamar yadda Wakilinmu Mahdi M. Muhammad, ya rubuto mana. 

Bayan kasancewarka mamba na Majalisar Wakilai, shugaban jam’iyya na jiha kuma tsohon gwamna, me ya sa ka ke da tabbacin cewa gogewarka da gaske a siyasance zai ba ka damar tsayawa takarar Shugabancin Jam’iyyar APC?
Bari na fara da yin godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki wanda ya ba ni damar hidimtawa mutane ta fuskoki daban-daban. Na ɗaya, tun kafin a kafa jam’iyyar APP, AD da sauran jam’iyyun siyasa, ma’ana, a lokacin rusasshiyar jam’iyyun UNCP da DPP, na yi takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar DPN don zama mamban Majalisar. Kun san yadda sojoji suka yi a lokacin. Ba a kammala zavuvvuka ba kafin jam’iyyun suka ruguje nan take inda Janar Abdulsalami Abubakar ya hau mulki kuma yana da shirin miqa mulki wanda ya ci gaba tsawon watanni tara har ya kai ga miqa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Bayan haka, ɓangarori biyu sun fito kuma ni na kasance cikin tattaunawar kafa APP. Na shiga taron duk da ƙarancin shekaruna, kuma muna daga cikin gwagwarmayar da aka yi har zuwa lokacin da aka fice daga Kudu maso Yamma ta hanyar tasirin soja saboda sun san cewa idan Kudu maso Yamma a wancan lokacin da qungiyar arewa sun haɗu a matsayin ƙungiyar siyasa, tabbas PDP ba za ta sami damar kafa shugabanci ba. Gwamnatin wancan lokacin da sojoji sun yanke shawara game da abin da suke son yi don abin da ake kira kwanciyar hankali na ƙasar, inda suka ce za su ba da shugabancin ga wani yanki na yankin wanda shi ne Kudu maso Yamma. Ba wai kawai game da sauya mulki zuwa Kudu maso Yamma ba, amma ga wani mutum mai suba Cif Olusegun Obasanjo kuma wannan bai yi mana daidai ba. Mun yi ƙoƙarin ganin mun yi iya ƙoƙarinmu don ganawa da manyanmu kamar Cif Alani Bankole, Cif Bode George da sauransu a Kudu maso Yamma, don su san cewa akwai wani wasa da ake bugawa. Hatta marigayi tsohon Gwamnan jihar Oyo kuma tsohon Ministan wutar lantarki, Cif Bola Ige, ma mun gaya musu cewa sojoji suna wasa, suna yin tasiri a zukatan mutane da yawa kuma kada mu nace kan sanya buƙatarsu ta tikitin takarar shugaban ƙasa a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyya. Wannan buƙatar, da dabara ta ƙarfafa a bayan fage, ya zama abin da ya kawo rarrabuwa wanda ya haifar da ficewar shugabannin AD daga APP. Ƙungiyar shugabannin arewa sun amince da cewa eh ɗan takarar Shugaban ƙasa na APP na zuwa ne daga Kudu amma abin da Kudu maso Yamma wanda daga baya ya zama ƙungiyar AD ke nema, ya kasance bayyanannen taƙaddara bayyananniya cewa me ya kamata ya kasance a cikin kundin tsarin mulkin wannan jam’iyyar shi ne fadar Shugaban ƙasa tana zuwa Kudu Maso Yamma.

Amma ba za ku iya yin siyasa kamar haka ba, ƙungiyar Arewa ba za ta so ta fara da irin waɗannan bayyanannun alamomin da za su iya karya lagon mabiya ba kuma su haifar da ji ko zato a Arewa, tun daga farko cewa mutane kawai ake tarawa don yin wasa na biyu. Babban namu, Marafan Sokoto da sauransu sun yi jayayya kuma sun yi jayayya har ta kai ga sun cimma matsaya. Ƙungiyoyin Kudu maso Yamma sun fita inda sula kafa jam’iyyar AD washegari. Dole ne muyi taron mu kuma mu gabatar da APP akan gaba wanda aka samu nasarar hakan saboda shirye-shiryen sun ɗauki lokaci mai yawa da kuma taruka da dama. Wasu daga cikinsu sun yarda, mutane kamar Alani Bankole, Cif Olabode George sun yarda su zauna tare da mu wasu kuma sun tafi su zauna tare da AD.

Duk a cikin waɗannan, gogewa da kuma darussan da na koya game da haɗa kawunan maslaha don haɗin kan ƙasa da nasarar jam’iyya suna da matuƙar muhimmanci, kuma ban yi karatu a matsayin mai hangen nesa ba, amma a matsayin wani wanda ya kasance wani vangare na haƙiƙanin abin da ya haifar da mulkin dimokiraɗiyya a halin yanzu a Nijeriya. Ina jin an ba ni iko da yawa don jagorantar maslaha ta ƙasa kuma in jagoranci jam’iyya ta ƙasa da gaske zuwa gagarumar nasara a duk faɗin ƙasar.

Kana da ƙuruciya sosai, ƙasa da shekara 30 lokacin da aka ba ka damar taka muhimmiyar rawa yayin kafuwar ƙungiyoyin siyasa daban-daban tun kafin lokacin mulkin dimokiraɗiyya na yanzu ya fara. Yanzu, ina kuka tsaya dangane da kururuwar neman ƙarin matasa da ake yi a harkokin mulki?
Abu mai mahimmanci, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka cancanci mutum don neman matsayin shugaban ƙasa a cikin jam’iyyar siyasa shi ne gogewar ƙwarewa, kuma a matsayin wanda ya yi sa’a ya fara samun irin wannan awarewa a shekaruna na 20, da zuciya ɗaya nake goyon bayan hannun matasa a siyasa. Na ba da tarihin yadda muka fara haɗa kan siyasa, tun kafin mu fara neman muƙami. Lokacin ina ƙasa da shekaru 30 ne, kuma batun abin da za ku iya yi ne. Ala kulli halin, da yawa daga cikin gwamnonin wancan lokacin (1999) sun kasance a shekaru 30 ne, saboda haka ba ainihin shekaru ns ke da muhimmanci ba, amma abin da za ka iya kawowa.

Wani lokaci a 1999, na zama sakataren jam’iyya a jiha ta kuma munyi aiki tuƙuru, muna shirin zaɓe amma lokacin da muke da zaɓe abin ya ba mu mamaki saboda tunaninmu ko lissafinmu ya dogara ne da kasancewar mun kasance a ƙasa amma tasirin da bamu za ta ba da sauran abubuwan sun sanya mu ƙarasa raba ƙananan hukumomin daidai, tare da bakwai kowannensu. Binciken da muka yi a baya ya sa ba mu yi tsammanin PDP za ta ci fiye da ƙananan hukumomi uku ba. Abin ya ba da mamaki. Mun gano ƙananan hukumomi biyu ko uku inda PDP za ta iya yin tasiri amma kash bamu san yadda suka yi ba duk da goyon bayan da muke da shi. Kwatsam, mun rasa majalisun da yawa fiye da yadda muke tsammani amma mun fito da ratar ƙuri’a babba. Idan waccan ƙaramar hukumar da aka yi a 1998 ta zama gwamna, da mun samu yadda muke so amma ta haka ne ta faru. Sun ɗauki bakwai kuma mun ɗauki bakwai, amma lokacin da ya zo ga gwamnati, mun ɗauki jagorancin da muka yi aiki tuƙuru dominsa, saboda haka, a zaɓen majalisar ƙasa da ta biyo baya, mun ɗauki dukkan kujerun majalisar dattijai uku sannan mun ɗauki kujerun majalisar wakilai biyar, mun rasa mazavar Tarayya ta Anka, amma Shinkafi da Zurmi mun share ta, Birnin-Magaji, mun share Maru da Bungudu, mun share Gumi da Bukkuyum, mun share Gusau da Tsafe, duk a shekarar 1998. Lokacin da aka zo zaɓen gwamnoni, mun kai jam’iyyarmu ga cin nasara a ƙananan hukumomi 19 cikin 24 na jihar Zamfara. Biyar daga cikinsu ‘yan PDP ne, a can ne muka kasance har 2003.

Shin, ba ka tunanin cewa jagorancin jam’iyya zuwa ga babban zaven ƙasa ya ƙunshi manyan ayyuka masu nauyi fiye da kasancewa saurayi, ɗan siyasa mai sa’a?
A 2003, na zama Sakataren jam’iyya a jiha ta, ni ne Babban Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da na yaƙin neman zaven Yerima da na kowane mutum da ke takara a ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar ANPP. Mun lashe kujerun Majalisar Dokoki ta Jiha da Majalisar qasa ɗari bisa ɗari kuma mun ci kujerar gwamna. A 2004, na zama Shugaban Jam’iyyar na Jiha kuma labaran ci gabanmu ya ci gaba. Duk da cewa akwai kiraye-kiraye masu ƙarfi daga mutane suna kira na in fito takarar kujerar gwamna kuma in gaji Gwamna Ahmad Sani, akwai wani dalili na hankali da yasa ba za a yi hakan ba, domin na fahimci hangen nesan gwamnan cewa tunda kusan mun fito daga qaramar hukuma ɗaya ne, shi ɗan Bakura ne ni kuma ɗan Talatan Mafara ne, saboda haka, yana da kyau tikitin takarar ya ci gaba da kasancewa a wannan tsarin. Idan za ku tuna, an samar da Bakura ne daga ƙaramar hukumar Talatan Mafara, saboda haka a fasaha, daga ƙaramar hukumar muke. Gwamnan na wancan lokacin ya ce a’a, bari mu ɗauke shi zuwa wani yankin domin mu sami damar sayensu, ta yadda za ka zama Mataimakin Gwamna. Akwai rashin fahimta don haka na yanke shawarar ba zan nemi matsayin Mataimakin Gwamna ba, kuma ya zo Majalisar Wakilai ne bayan na gama wa’adi na a matsayin shugaban jam’iyya. Na kasance a majalisar wakilai lokacin da gwamna na wancan lokacin, Aliyu Shinkafi ya sauya sheƙa zuwa PDP kuma mun kasance a cikin ANPP.
PDP na da komai, Shugaba Goodluck Jonathan, kuɗin mai da ikon tarayya amma Allah ya ƙaddara makomar cewa zan ci kuma zan zama gwamnan jihar zamfara a 2011. Na zama gwamna sannan na zo tsarin haɗewa don kafa APC . A lokacin muna gwamnoni 11, Borno, Yobe, Zamfara, Nasarawa, Edo, Osun, Lagos, Oyo, Ekiti, kusan mu goma sha ɗaya ne ciki har da ɗaya daga APGA. A haka muka fara aikin haɗewa. Mun so zama masu ci gaba ta yadda muke son kawo dukkan adawa a cikin jirgin. Ondo ɗan jam’iyyar Labour ne, Anambra APGA ce, amma Anambra da Ondo sun koma PDP a ƙarshe sannan mun ci gaba da zama 11. A nan ne muka fara wannan gwagwarmayar har zuwa 2013 lokacin da PDP ta gudanar da taronta kuma mun sanya sabuwar PDP ta bi mu, tare da Jihohi huɗu, Jihohin Kwara, Ribas, Kano da Sokoto kuma mun zama 14. Mun fara wannan tsarin haɗewar sannan kuma a zaɓen 2015, mun lashe dukkan kujerun jihar a Majalisar Dokoki ta ƙasa sannan kuma, jam’iyyarmu, APC ta lashe Shugabancin.

Wannan shi ne inda muke a yau kuma a lokaci guda a cikin shekarar 2015, gwamnonin abokiyar aikina gaba ɗaya suka karɓe ni in zama shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Idan ka duba abin da muka aikata a baya da kuma abin da ke ƙasa a yanzu, batun ko nauyin shugabanci ba zai kasance min wani aiki mai wahala ba domin na san shi saboda na san maɓallan da suka dace na matsa don haɗa kan mutane da cin nasara zaɓe.

Yallabai, ka ce yin takarar shugabancin jam’iyya ko jagorancin jam’iyyarka bai kamata ya zama abu mai wahala ba amma mutum ya lura cewa ana faɗin abubuwa game da kai, gami da zargin da aka bugawa makonnin da suka gabata da wani sanannen gidan yanar gizo na intanet ya wallafa cewa ana zarginka da Naira biliyan 8 na gwal an kuma ƙwace sandunan mallakarka a filin jirgin saman Kotoka na ƙasa da ƙasa a Accra. Yaya ka ke ji da wannan?
Yaɗa shirme na iya sanya wawa cikin babbar matsala yayin da wanda aka yi wa ɓatanci ya yanke shawarar kai ƙara. Ban taɓa sanin kowa a wannan wurin ba kuma haka nima nake ta jin jita-jitar mutane, ban taɓa samun irin wannan zinariya ba. Zargin da ba shi da tushe ya kasance mai saurin bayyana ne saboda wallafe-wallafe na gaske waɗanda suke da abokan aiki da sauran abokan hulɗa a Ghana sun gano cewa babu wata ma’ana a ciki. Da kyau, wasu mutane na iya qirqirar ƙarya, amma a ƙarshen ranar, gaskiya za ta yi halinta. Akwai sauran abubuwa da yawa da suka faɗa waɗanda kawai ƙagaggiyar ƙaryar ce da nufin ƙoƙarin ɓata wa mutumin kirki suna, amma ba za su taɓa yin nasara ba. Sun yaɗa jita-jita cewa na samu kuɗi daga London Paris Club, kaza, kaza, zaka, cewa na saci jihar kuma na yi wannan da wancan amma na ƙalubalanci kowa ko dai a cikin ƙungiyar Gwamnoni ko a jihar.

A matsayina na gwamna, mene ne aikina? Ya kasance don amfani da albarkatu, kashe kuɗi don amfanin mutanena, wanda wannan shi ne aikin da aka bani. Ɗaukar kasafin kuɗi da tsare-tsare zuwa Majalisar dokoki, zartar da doka da aiwatar da ayyuka. Saboda haka, idan bada kwangila don ayyukan ci gaba yana nufin cewa na kashe kuɗi a kan kwangila don samun kuɗi, bari gwamnan yanzu ya ba da ƙarin kwangila kuma ya sami kuɗi. Akwai abubuwa masu sauƙi, masu sauƙin fahimta waɗanda wasu masu ɓarna suke ƙoƙarin fassarawa da gangan, misali, yanzu muna da kwantiragin hanyoyi na miliyoyi a Abuja-Kaduna-Kano wanda aka fara sashi zuwa wasu ɓangarori. Yanzu, an bayar da dukkan abin da aka shimfiɗa gaba ɗaya amma shin suna cewa Shugaba Buhari ya bayar da wannan kwangilar ne don neman kuɗi? Ko kuwa kuna ƙoƙarin faɗa min cewa duk ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, Buhari yana ba su saboda yana son samun kuɗi ne? Yanayi ne mara kyau sosai yin ƙarya, wannan ba daidai bane. Amma idan kuna da wani zargi game da wani, yi amfani da gaskiya. Waɗannan su ne hujjojina.

Shin za ka iya kawar da fargabar magoya bayanka game da ƙarar da EFCC ke yi a kanka?
Babu wani abin damuwa. Babu abin damuwa. Abin da ake faɗa yanzu shi ne cewa akwai wata ƙungiyar ‘yan daba a yankin Arewa maso Yamma ta hanyar mutanen da ke sha’awar lamba ta biyu kuma wannan ne ya sa Yari ya zama dole kawar da shi ta kowace hanya.

Me ka ke nufi da ‘kawarwa’?
Cewa akwai wata ajanda da wasu ‘yan jam’iyyar a yankin Arewa maso Yamma suke da shi na rage fata ga kujerar shugabancin jam’iyyar saboda idan ka samu, hakan zai vata lissafin su na takarar kujerar Shugaban ƙasa na 2023. Na ji haka kuma. Wani ya gaya min cewa wasu abokan aikina da tsoffin abokan aikina suna da sha’awar lamba ta ɗaya da lamba biyu saboda haka, idan kujerar Shugabancin ƙasa ta koma yankin Arewa maso Yamma, babu abinda za su samu, don haka suka haɗa kai don kashe Yari. Idan Allah ya ƙaddara hakan ta kasance, hakan za ta kasance. Mutane na iya motsawa da yin kowane irin lissafi amma ba za su yi nasara ba. Abin da kawai na sani shi ne, Ina da ƙarfin jagorancin wannan jam’iyyar kuma sun san abin da zan iya yi.

Babu damuwa irin uzurin da suke bayarwa, ya fito daga yanki ɗaya tare da Shugaban ƙasa, a’a. Lissafin mu a yanzu ya kusan 2023 ba 2019. Sai kawai lokacin da kuka sami jam’iyya, jam’iyya mai ƙarfi, sannan za ku fara tunanin dubu biyu da ashirin da uku kuma duk halin da ake ciki, ƙarfin da zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasarar zaɓe shine abu mafi muhimmanci. Wannan babban yanki ne wanda na yi imanin ina da ɗan ilimi kaɗan amma mai muhimmanci game da yadda ake aiwatar da shi.

Idan ana maganar jagorantar jam’iyyar, da yawa sun san cewa ba wai kai kaɗai ka ke shugabanta ba harma da waɗanda ka ke jagoranta a duk faɗin Zamfara. Don haka, lokacin da sanarwa ta fito daga Shugaban riƙon Shugaban ƙasa na ƙasa yana cewa Gwamnan na yanzu da ya sauya sheƙa yanzu shi ne shugaban jam’iyyar a jihar Zamfara, me za ka ce game da hakan?
Kun ga wancan, ba ni da abin cewa da yawa. Duk abin da nake ba su shawara su yi, duk abin da na roƙe su shi ne a duk abin da suke son yi, to su bi tsarin mulkin jam’iyya su yi aiki da shi. Bari su kalli kundin tsarin mulkinsu da kyau su jagoranci daga can. Ba na takarar kowane shugabanci. Mutane ne suka sa na zama shugabansu kuma za su ci gaba da kira na a matsayin shugaba muddin ina raye. Ba batun APC bane, suna kirana shugaba. Lokacin da na ke gwamna ban taɓa kiran kaina shugaba ba. Ko a matsayin gwamna mai ci, akwai wani da nake magana da shi a matsayin shugaba kuma ya sani, Ina kiransa Jagora. Jagora jagora ne, ina kiran sa, duk lokacin da ya kasance, na kan kira shi shugaba. Duk lokacin da na gabatar da jawabi ga jama’a, na kan yi masa jawabi a matsayin jagora. Ban taɓa yin magana da kaina a matsayin jagora ba, Na yi gwamna, wannan shi ne abin da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba ni kuma wannan shi ne abin da Allah ya yanke shawarar yi ni.

A ƙarshe, ta yaya za ka tantance damar da APC za ta samu a shekarar 2023 idan aka yi la’akari da abin da jam’iyyar ta yi alƙawari a shekarar 2015, amma da alama ba za ta iya kawowa ba, game da rashin tsaro, yaƙi da rashawa da tattalin arziki?
Bari mu sanya ƙungiya a wuri na farko. Idan muka sanya ƙungiyar da za ta iya sarrafa APC yadda ya kamata, ta haka ne za mu san tasirin. Ba waɗannan kawai ba, eh sun kasance suna daga cikin alƙawuran yaƙin neman zaɓenmu kuma mun san akwai wasu matsaloli a cikin tattalin arziki kuma me kuke da shi. Akwai wasu batutuwa a can amma ba abin da ya munana har ya zama ba za a iya ganin abin da muke yi ko cimma nasara ba. Haka zalika, akwai batutuwa da yawa a bayan damar a APC 2023 ko akasin haka. Da yawa ya dogara da yadda muke yin lissafinmu, da yawa ya dogara da inda muka fitar da shugabanci zuwa, wanda duk irin waɗancan abubuwa gaskiya ne da ya kamata mu yi la’akari da su.

Abin da kawai zan ce shi ne idan ka kalli haɗakarmu, daga arewa da shiyyoyin da muka ɗauka don tafiya tare, Kudu maso Yamma musamman. Idan ka dube shi sosai kuma ka kalli abin da ya faru, daga can ne za mu iya ɗaukar matakin mu ce daidai, wannan shi ne abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na jam’iyya ko kuma wannan shi ne abin da bai kamata mu yi a matsayinmu na jam’iyya ba kuma a hankali mu kalli wasu kurakurai mun yi a cikin shekaru shida da suka gabata kuma ga yadda za mu iya matsawa da sauri a matsayin jam’iyya da kuma a matsayin gwamnati don ganin yadda za mu iya rufe kusan 30, 40 bisa ɗari sannan mu shawo kan mutane kuma mu tambaye su, mun yi alƙawarin abubuwa da yawa da za mu ba zasu cuku ba saboda mun sami abubuwa da yawa waɗanda ba su saito ba. Dangane da batun tattalin arziki, muna sa ran samun farashin mai a dala 100-120 kan kowace ganga amma ya sauka zuwa dala 27 kan kowace ganga kuma yanzu ba zai wuce 70 ba. Akwai abubuwa da yawa da za mu tattauna game da, ba wai kawai tsaro ba, rashin aikin yi da sauransu. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu duba, yankunan da muke yin iya ƙoƙarinmu. Akwai abubuwa da yawa da za a duba cikin tsarin, musamman tsakanin yanzu zuwa shekara mai zuwa.

Meye amsarka ga ihun sauya sheƙa zuwa Kudu?
To, ba ni da wani matsayi na ƙashin kaina da ya wuce matsayin jamiyyar a hukumance. Idan manyan shugabannin APC sun yi alƙawarin cewa mulki ya koma kowane wuri, ya kamata mu girmama shi. Ba za mu sami dalili ba don tilastawa. Amma ya kamata mu kalli wannan da sauran abubuwan da kyau domin APC ta ci gaba da samun nasara zuwa gaba.