Barkan mu da sallah!

Daga NASIR S. GWANGWAZO
 
A cikin wannan satin, wato ranar Talatar da ta gabata, 20 ga Yuli, 2021, ne ɗaukacin al’ummar Musulmai da ke a faɗin duniya su ka gudanar da shagulgula na bikin Babbar Sallah, wato Sallar Layya, inda masu hali su ka yanka ragunansu na layya.

Layyar an gudanar da ita ne a don tuna wa da Annabi Ibrahim (AS) a lokacin da Allah ya umarce shi ya yanka ɗansa, Annabi Isma’il (AS), a Dutsen Arafat, don bin umarnin da Allah ya ba shi.

Don bin umarnin na Allah (SWT) Annabi Ibrahim (AS) da ɗan nasa, Annbai Isma’il (AS), sai dukkansu su ka bi umarnin na Allah, amma daga baya sai Allah (SWT) ya fanshi ran Annabi Isma’il da rago, inda tun daga wancan lokacin zuwa yau al’ummar Musulmai da ke faɗin duniya su ke yanka rago, don yin layya.

Musulmai da su ke da hali, Allah ya umarce su da su dinga yin layya da rago ko raƙumi ko shanu ko akuyoyi, don samun ladan ranar ta Babbar Sallah. Wato dai an kuma kasa dabbobin da za a yi layyar da su kashi daban-daban; ya daganta ga halin mutum.

A na raba naman layyar ga ’yan uwa, abokai da kuma maƙwabta, sannan kuma a na bai wa marasa hali ko waɗanda ba su da ƙarfin yin layyar, wato talakawa kenan. Haka nan kuma iyalin mai layyar ma su na yin amfani da naman, don buƙatun kansu.

Har ila yau, al’ummar Musulmai a lokacin shagulgulan Babbar Sallar su na yin iyaka ƙoƙarinsu wajen taimaka wa talakawa marasa ƙarfi, don su ma su samu sukunin yin sallar a cikin walwala.

Manyyan darussan da a ka koya a cikin biki ko hidmar sallar su ne, nuna juriya da ƙara ƙarfin imani da Allah, don biyan su a nan duniya da ko ma gobe ƙiyama. Bugu da ƙari, a saboda haka a na shawartar Muslimai da su yi riƙo da wannan umarnin, don samun albarka mai ɗorewa daga Allah.

Addinin Musulunci Allah ne ya turo fiyayyen hallita, Annabi Muhammdu (SAW), da shi zuwa ga ɗaukacin bil adama da ke faɗin duniya kuma babu wani zaɓi da Musulmai su ke da shi na ƙin karɓar umarnin na Allah. A yayin da alhazai waɗanda su ka fito daga Ƙasar Saudiyya (sakamakon annobar Cutar Korona) su ka gudanar da aikin hajji, wato ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, sauran ɗaukacin Musulmai a faɗin duniya su kuma su na gudanar da bukukuwan Babbar Sallah ne a ƙasashensu.

Sauran darussan sallar sun haɗa ne da cewa, dole ne su kasance masu miƙa wuya ga Allah (SWT) ta hanyar bayar da sadaka da kuma nuna ƙauna ga maƙwabta.

Asali dai, sallar idi, al’ummar Musulmai ne su ke gudanar da ita, inda su ke yanka raguna don neman yardar Allah (SWT), ba wai lallai, don cin naman na layya ba, inda kuma su ke haɗawa da ciyar da abinci da sauran kyaututtuka. Haka kuma, kiran sunan Allah a lokacin da za a  yanka raguna ya na da mahimmaci matuƙa. Dukkan yin ayyuka masu kyau da a ka yi, don Allah, a na samun lada kuma za a samu ribar yin hakan a duniya da kuma a lahira.

Babbar Sallar ba ta da iyaka a rayuwar Musulmai, domin ta na nuna cin nasarar Musulmai kuma ta na kasancewa rana mai mahimmancin gaske a rayuwarsu. Matuƙar Muslmai su ka samu irin waɗannan yanayi, za a iya cewa sun samu cin nasara a rayuwarsu.  A na kuma buqatar Musumai su kasance masu yin biyayya ga umarnin Allah (SWT) gabaɗaya ba tare da wata tantama ba a ɗaukacin rayuwarsu.

Asalin Babbar Sallar ta na koyar da darussa da sadaukar da kai rabar da kyaututtuka da sauransu. A yanzu fiye da a baya, a na buƙatar aiwatar da waɗannan kyawawan darusan da mu ka koya a lokacin sallar da kuma bayanta.

Idan a ka yi la’akari da ƙalubalen rashin tsaro daban-daban da a Nijeriya da cin hanci da rashawa da ya yi wa ƙasar ɗaurin butar Malam da sauransu, hakan ya na shafar tattalin arziki. Hakan ya na kuma sanya rashin yarda, inda ya ke haifar da rashin jituwa a tsakanin ƙabilun ƙasar da kuma sauran mabiya addinai a ƙasar.

Haƙiƙa matsin tattalin arziki ya rage armashin bukukuwan sallar, inda da dama ke ƙorafin yadda cewa, sun kasa aiwatar da abubuwan da suka saba yi duk shekara. Yayin da wasu sun kasa yin layya, wasu kuwa ma ko tuwon sallah sun kasa yi.

Ko ma dai mene ne, a  yayin da ɗaukacin Musulman duniya su ke gudanar da shagulgulan sallar, mu na kira a gare su gudanar da bikin a cikin kwanciyar hankali da rungumar son zaman lafiya da kuma taimaka wa marasa ƙarfi, yadda za a ƙara ciyar da Nijeriya gaba.

A taqaice, abinda mu ke buƙata shi ne, yin adalci da bin umarnin Allah (SWT), kamar yadda Annabi  Ibrahim (AS) ya yi a lokacin rayuwarsa. Hakan zai tabbatar da kawo ƙarshen dukkan ƙalubalen da a ke fuskanta a ƙasar, inda idan a ka yi hakan, za a samu cikakkiyar zaman lafiya mai xorewa a Nijeriya.