Direban jirgin da ’yan bindiga suka harbo a Zamfara ya yi basaja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu bayanai da ke fitowa game da jirgin Sojin Saman Nijeriya (NAF) da ’yan bindiga suka yi wa varin wuta har ya faɗo, inda matuƙin jirgin ya tsira da rayuwar sa a jihar Zamfara.

Sojin Saman Nijeriya a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne suka bayyana yadda matuƙin jirgin saman su ya tsira da rayuwarsa a lokacin da ‘yan bindiga suka ɓaro jirgin daga sama a iyakar jihar Zamfara da kuma Kaduna.

Ko da yake, jaridar Daily Trust ta haɗa rahoton yadda matuƙin jirgin ya sha da kyar, inda ta haƙaito cewa matuƙin jirgin ya yi basaja ne zuwa wani ƙauye da ke kusa da inda jirgin ya faɗo.

Wani mazaunin ƙauyen da ya buƙaci da a ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce bayan da ‘yan bindigar suka ɓaro jirgin, sai matuƙin jirgin ya duro daga sama, sannan ya tsere zuwa wani ƙauye mafi kusa.

Ya ce tserewar matuƙin jirgin ke da wuya daga wajen da abun ya faru, sai ‘yan bindigar suka isa wajen don ganin ko akwai mutanen da suka tsira a ciki.

“Matuƙin jirgin ya duro daga saman jirgin da irin rigar su ta durowa daga sama jirgi, nan da nan sai ya tsere zuwa wata unguwa da ke kusa. Da ya bayyana wa jama’a abin da ke faruwa da shi sai mutanen ƙauyen suka ɓoye shi.”

“Sai ‘yan bindigar kuma suka zo wajen da jirgin ya faɗo, watakila ko suna duddubawa ne ko akwai wani da ya tsira don su kama shi ko kuma su kashe shi.

“To sai ‘yan ƙauyen suka ce wa matuƙin jirgin ya yi basaja ya sanya kaya kamar wani cikakken ɗan ƙauye, gona-gona, inda daga nan sai suka tafi da shi wajen mai unguwar garin.

“Da safiyar ranar Alhamis jiragen sojojin sama guda biyu masu saukar ungulu suka zo suka ɗauki matuƙin jirgin da ya tsira. Jirgin ya sauka kusa da sakandaren garin, yayin da ‘yan ƙauyen suka damƙa wa sojojin sama shi”, inji mazaunin garin.

Sai dai kuma ita Rundunar Sojin Saman Nijeriya a ta bakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya ce sun samu matuƙin jirgin ne a hanyar sa ta zuwa wasu ƙauyuka da ke kusa.

To sai dai kuma wani abu mai kama da ruɗani a cikin bayanan shi ne, yadda wasu rahotanni suke nuna cewa sojojin sun samu Dairo ne a kan hanyar sa ta zuwa wani wuri da sojoji suke zama.

“Matuƙin jirgin ya yi amfani da basirarsa duk da ɓarin wutar da ‘yan bindigar ke yi, amma haka ya samu ya tsere zuwa wata unguwa da ke kusa don neman mafaka, ya jira gari ya waye.

“Haka ya yi amfani da cocilar waya yana ɗan haska gaban sa, Laftanal Dairo ya dinga kauce wa rukunin ‘yan bindigar domin ya isa dandalin da Sojin Nijeriya ke zama, inda a nan ne ya tsira,” a cewar Gabkwet.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta tabbatar da faɗuwar jirgin samanta (Alpha Jet) a Zamfara wanda aka ce yana kan hanyar sa ta dawowa daga aikin shawo kan matsalar tsaro a tsakanin iyakokin Zamfara da jihar Kaduna ƙaddara ta faɗa masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *