Babbar Sallah: Sarkin Musulmi da sauran jagorori sun yi tambihi

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar nan ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga shuwagabanni a Nijeriya da su kasance masu tsoron Allah, su fitar da talakawansu daga ƙangin rayuwa.

Alhaji Abubakar III ya bayyana haka ne a a jawabin saƙon sallah, wanda ya gabatar ranar Talatar nan a Jihar Sokoto. Inda ya ƙara da cewa, yananyin ƙangin rayuwar da al’ummar ƙasar nan ke ciki, abin dubawa ne. Kuma abu ne da yake buƙatar a ɗauki wasu matakai don ganin an daƙile shi.

A cewar sa, dole shugabanni su zage damatsa don magance matsalolin tsaro da talauci  domin samar da ha]in kai da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa, magana ta gaskiya, a halin da ake ciki al’ummar Najeriya suna buƙatar jajircewar shugabanni don ganin an magance matsalolin tsaro da zafin talauci da  yunwa da sauran matsaloli da suke addabar su.

Sarkin ya ƙara da cewa, a don haka yake kira ga shuwagabanni da su ji tsoron Allah su sauke nauyin al’umma da ya rataya a wuyansu. Domin a ƙara kyautata rayuwa a ƙasar nan.

Shi ma a nasa jawabin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi kira ga shuwagabanni da su tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma ba tare da la’akari da nuna banbance-banbancen ƙabila, ko addini ko kuma ra’ayin siyayasa ba. Domin a cewarsa dole a samar da haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasa. Domin ba ƙasar da za ta cigaba alhali tana fama da  rashin haɗin kai da rigingimu a tsakanin al’ummar ƙasar. Domin sai da haɗin kansu gwamnati za t a iya fuskantar matsalolin tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Daga Kano kuma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi kira ga musulmi da su yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya, da haɗin kai da kuma cigaba. Haka gwamnan ya nemi ‘yan ƙasa da su yi addu’a game da ta’addanci, da masu satar mutane, ,da sauran ayyukan ɓata- gari a ƙasar nan.

Sannan su kuma su ma al’umma su zama masu riƙe gaskiya.  Sannan ya ƙarƙare jawabinsa da yi wa sarakunan masarautun Kano guda biyar barka da Sallah. Sannan ya yi kira da al’umma su bi dokokin kare kawunansu daga sabuwar cutar Kwarona da ta ɓullo.

A ɗaya ɓangaren kuma,  shi ma Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, ya yi kira ga musulmi da su yi wa ƙasar nan addu’a sannan su yi amfani da lokacin bukukuwan idi domin ƙara ɗabbaƙa ‘yanuwantaka da zaman lafiya a tsakanin ‘yanuwansu musulmi. Sannan kuma su kiyaye dokokin kare kai daga cutar Kwarona yayin shagulgulan Sallar.

Kimanin miliyoyin Musulmi ne dai manya da yara suka yi cikar kwari a birane, don gabatar da shagulgulan Babbar Sallah.