Buhari ya tsumu da ta’azzarar watsi da filayen noma a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar jajiberen Babbar Sallah, wato Litinin ɗin da ta gabata, ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana tsumuwarsa da mamakinsa ga yadda aka bar filayen noma baja-baja ba tare da an nome su ba a faɗin ƙasar. A cewar Shugaban, kimanin kashi biyu da rabi kacal ce a cikin ɗari na ƙasar Najeriya aka nome.

Shugaban ya bayyana hakan ne a gidansa da ke garin Daura na Jihar Katsina.  jim kaɗan bayan saukowa daga idin babbar sallar nan. Shugaban ya ƙara da kira ga al’ummar Najeriya da su ƙara ƙanƙame sana’ar noma hannu bi-biyu.

Babban mai ba wa Shugaban ƙasa shawara a kan hulɗa da jama’a da watsa labarai, Garba Shehu shi ya bayyana haka a ranar Talatar nan. Inda ya ce, Shugaban ya samu bayanin waɗannan alƙalumma ne daga hukumar ba wa shugaban ƙasa shawara a kan tattalin arziki na ƙasar nan. Inda suka bayyana cewa ɗan ƙanƙanin kaso ne kawai na ƙasar noma a Nigeriya aka yi amfani da ita wajen noma. Inda hukumar suka yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kyautata alaƙarsu da mutanen gari domin manoman su ji daɗin aiwatar da ayyukansu.

A yayin tattaunawarsa da manema labarai a gidansa da ke Daura ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen samar da zaman lafiya a ƙasar nan. Sannan su nemi haɗin kan al’ummar gari don samun bayanan da za su taimaka musu.

Shugaban ya bayyana cewa, a yanzu haka dai sha’anin tsaro ya ƙara samuwa sosai a Arewa maso gabacin ƙasar nan, da Kudu maso kudancin ƙasar nan, kuma a yanzu haka ana ta ƙoƙari don samar da tsaro a Arewa ta tsakiya da kuma arewa maso yammacin ƙasar nan. Inda ya ba da tabbacin cewa, za a binciko dukkan masu hannu a cikin tayar da hankalin ‘yan ƙasar  nan da ma ƙasar kanta.

Gabanin wannan tattaunawar ne, shi kuma Sarkin Daura, Umar Faruk ya yi kira a Masallacin idin. Inda ya yi kira ga ‘yan ƙasar nan da su zama masu mara wa shugaba Buhari baya. Hakan a cewar Sarkin, shi zai taimaka wa shugaban ya cimma burikansa na samar da tsaro da kuma haɓakar arziki a ƙasar nan.

 Ya ƙara da cewa, tunda Buhari ya hau kan mulkin ƙasar nan suke samun cigaba a ƙasar nan. Sarkin ya ƙarƙare bayaninsa da yi wa shugaban addu’ar samun lafiya da ƙwarin gwiwa don samar da zaman lafiya. Inda ya ƙara da cewa da ma Allah ne yake riƙe da ƙasar Najeriya kuma ya san Allah ba zai kunyata ta ba.