Makomar Arewa ta fi 2023, inji Gwamna Matawalle

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ’yan Arewa za su dawo su yi wa kansu karatun ta-natsu, a ajiye ƙiyayya da hassada da kwa]ayi da tsoro tsakanin juna, a fuskanci babba barazanar da ke ƙara raba makomar yankin na Arewa; wato sha’anin tsaro, talauci da lalaci, ba wai batun manyan zaɓukan 2023 ba da ba su zo ba.

Haka nan ya ce, dattawan Arewa da masu riƙe da madafun iko da ke ganin su ne sitiyarin samar da ci gaba ko makoma ga ’yan Arewa suna da ƙalubalen da ke gabansu na gaya wa junansu gaskiya akan sun kasa riƙe amanar da na gabansu, irinsu Sardauna, suka bar musu a kan makomar ’yan Arewa da Nijeriya bakiɗaya.

Matawalle, wanda ya ke bayani ta cikin wata sanarwar manema labarai, wacce ya sanya wa hannu a Gusau, Babban Birnin jihar tasa, ya lara da cewa, “lokaci ya yi da za a zauna a yi wa juna gafara a haɗa kai, don ganin an ceto ’yan ƙasa da ke fuskantar ƙalubalen tashin hankali na kisan gilla, hare-haren cin amana da ƙone dukiya da ake yi a Arewa ba gaira ba dalili.

“Zancen makomar Arewa a 2023 ba shine abin bayar da fiffiko ba, muhimman abu shine fuskantar waɗanan ƙalubalen da ke da mummuna illa ga rayuwa da dukiyar al’umma da ta sanya taɓarɓarewar tsaro, ilimi da kasuwanci a kusan ko’ina na Arewa, musamman Arewa maso Yamma da noma ya zama tashin hankali ga jama’a.

“Sai mu shugabani mun zauna tare mun amince da a zuciyoyinmu za mu sanya tsoron Allah, mu yafi juna, mu ajiye hassada da kwaɗayin mulki da son rai, sa’ilin za a iya samun nasara ga lamarin da zai taimaka a kawo sauƙi ga waɗannan matsalolin.

“Akwai hatsari mai yawa wasu ’yan ƙalilan, don sun ga suna da wata mafita har su yi ko oho ga bayar da ha]in kai a fuskanci wannan barazana. Lokaci ne a yanzu da ake buƙatar haɗin kai, ajiye ra’ayin ni ɗan jam’iyyar APC ko PDP ko APGA ko dai wacece don hadin kai a samu nasara. Muddin wasu ko wani ke ganin, idan babu shi Arewa ba za ta cimma wannan burin ba; tabbata wannan matsalar ba za ta kai ƙarshe da sauƙi ba.

“Duk ɗan Arewa yana da haƙƙi ga ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin. Don haka lokaci ya yi da za ajiye ra’ayin siyasa, a manta da ƙabilanci na harshe ko addini a dawo ga gina ƙasa a samar wa jama’a kwanciyar hankali da zaman lafiya, don inganta musu rayuwa da samar da makoma ta gari.

“Shugabani su mayar da adalci da gaskiya tare da samarwa al’umma hanyoyin sauƙi ga tafiyar rayuwa da inganta musu ababen more rayuwa. Al’umma su haɗa kai, don bai wa gwamnati goyon baya da taimaka wa jami’an tsaro akan yaƙi da ta’addanci da kisan gilla na ba gaira ba dalili.

“Babu wani da zai zo daga waje ya gyara mana makomarmu ko inganta mana hanyoyin rayuwa muddin ba mu mayar da hankali ga wannan lamari a tsakaninmu ba.”