Tsoffin hafsoshin Nijeriya: Ba ritaya ba ce, kora ce – Shehu Sani

Daga AISHA ASAS

Sanata Kwamared Shehu Sani, tsohon ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta takwas, mutum ne wanda ya yi suna wajen faɗa wa gwamnati gaskiya komai ɗacin ta tun lokacin da sojoji ke mulkin ƙasar nan. Kuma ɗan gwagwarmaya ne sannan shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam, CRC. A wannan hirar da Manhaja ta yi da shi, ya nuna illolin da ciwo bashi kan iya jawowa, da kuma yin gugar zana ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan batun ritayar da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan su ka yi bayan yekuwar da jama’ar ƙasar su ka yi tun tuni cewa ya wartake su.

Ran ka ya daɗe Nijeriya za ta ciyo bashi daga waje da kuma a nan cikin gida domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2021, wanda gabaɗaya kuɗin ya haura Naira Tiriliyan biyar. Shin a matsayin ka na shugaban kwamitin karɓar bashi a tsohuwar majalisar dattawa ta takwas, yaya ka ke ganin irin wannan ɗumbin bashin da gwamnatoci su ke tara wa Nijeriya, ka na ganin ba zai kawo wa ƙasar cikas ba nan gaba? A ɓangare guda kuma wasu daga cikin talakawa su na kukan ba sa gani a ƙasa.
Bismillahir-rahmanir-raheem. Na farko dai cin bashi babu matsala idan akwai wasu sharuɗɗa guda uku zuwa huɗu: Sharaɗi na farko shi ne mai za a yi da bashin kuɗin idan aka ciwo. Na biyu wane sharaɗoɗi ne ke ɗauke da bashin, misali kuɗin ruwan da aka ɗora wa shi bashin. Na uku kuma yaushe za a biya wannan bashin. Sai na huɗu shi ne ya ya za a yi a biya bashin ba tare da ƙuntata wa jama’a ba ta hanyar yi musu coge wajen biyan albashin su da sauran wasu ayyuka da biyan ‘yan kwangila.

To a halin yanzu Nijeriya ta samu kan ta a cikin wani hali na amso bashi a wurare daban-daban; an amsa daga China, an amsa daga bankin Musulunci na Saudiyya, an amsa daga babban Bankin Duniya, an amsa daga Brazil, sannan yanzu an koma za a ranto a kuɗaɗen da su ke ajiye na ‘yan fansho domin a yi amfani da su. Batu na gaskiya dole ne a yi hattara, don bai wuce shekaru goma sha shida da suka wuce ba Gwamnatin Obasanjo ta fitar da Nijeriya daga cikin ƙangin bashi, Nijeriya ta biya wasu kuɗaɗen, wasu kuma aka yafe mana gabaɗaya. To amma yanzu idan ya kasance bashin ya taru mana da yawa, zai yi matuƙar wahala mu iya biya ganin halin da mu ke ciki na karyewar man fetur kuma ga buƙatu da yawa da Gwamnati ta ke son ta yi da kuɗi.

Ran ka ya daɗe kamar yadda ka ambata cewa za a ara daga irin kuɗaɗen ‘yan fansho domin cike giɓin kasafin kuɗin 2021. Shin ka na ganin yin hakan ba zai cutar da su kansu masu amsan fansho ɗin ba?
To su dai kuɗin fansho kuɗi ne da su ka jiɓanci rayuwa ta mutanen da su ka bautata wa ƙasa; kuɗin abincin su da lafiyar su da kula da iyalan su da tafiye-tafiyen su da kuma sauran abubuwan da za su kashe na yau da kullum, duk sun ta’allaƙa ne a wannan kuɗi na fansho da su ke amsa. To abin tsoro shi ne a ranci kuɗi a kasa biya, lokacin da ya kasance za a biya ɗan fansho a nemi kuɗi a rasa. Kwanan nan ma tsofaffin sojoji su ka yi zanga-zanga akan maganar kuɗin fansho; to kin ga idan aka cigaba da irin wannan rance akwai matsala. Ka da mu manta kuɗin da ke shigowa Nijeriya kashi biyu ne: Akwai kuɗin da ke shigowa idan mu ka sayar da man fetur ko wasu kayayyaki da kuma kuɗin cikin gida waɗanda ake samu ta ɓangaren haraji. To idan ya kasance mun zo mu na cin bashin da zai hana mu biyan albashi da hana mu yin wasu ayyuka na qasa, kin ga akwai matsala nan ma. Idan ka amshi bashin ƙasar waje ba ka biya ba babu wanda zai magana, idan ka amshi na bankin Musulunci na Saudiyya ba ka biya ba babu talakan da zai magana, idan ba ka biya na Bankin Duniya ba babu wanda zai yi magana. Amma da zarar ba ka biya ‘yan fansho ba dole a yi magana domin rayuwar su za ta iya kasancewa cikin wani hali.

Me za ka ce game da ritayar manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan bayan tsayin lokaci da ake ganin sun kasa har akai ta kiraye-kiraye ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sallame su ya ɗora waɗansu?
To a halin gaskiya rashin canja su da wuri illa ce ga tsaron ƙasa Nijeriya bakiɗaya, saboda na farko dai sun gaza, na biyu kuma lokacin su ya wuce na zama wannan matsayi da su ke a kai; cire su da aka yi yanzu shi ne daidai, domin fitar su daga wannan matsayi zai taimaka wajen ba sababbin jini damar su zo su bayar da irin tasu gudummuwar, kuma su nuna irin tasu basirar wurin ƙoƙarin kawo ƙarshen sace-sace da kashe-kashen jama’a da garkuwa da su da ake yi tare da nemo mafita ga taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya gabaɗaya. Saboda haka cire su da aka yi wata dama ce da aka ba sababbin domin su nuna ƙwarewar su wajen daƙile matsalar tsaron da ta addabi Arewa Maso-Gabas da Arewa Maso-Yammaci da kuma kudancin Nijeriya bakiɗaya.

To ranka ya daxe ka na ganin yin ritayar da su ka yi da kansu ba tare da an sauke su ba zai iya haifar wa al’ummar ƙasa ɗa mai ido ko kuwa dai su ma su na kallon gazawar tasu ne?
Batun gaskiya duk wanda ya san halin da ake ciki zai iya fahimtar wani abu. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne kawai ya ke masu ɗan rufa-rufa cewa ba korar su ya yi ba gabaɗaya, amma kowa ya sani cewa shi ya sauke su. Tun da abu na farko ma zaman su a wannan wuri ba kan ƙa’ida ya ke ba. Na biyu kuma sun gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya, kuma an matsa wa Shugaban Ƙasa lamba fiye da shekara biyu da su ka wuce cewar ya wartake su. Ina ganin kawaici ne kawai ya yi ba wai ritaya ya yi masu ba, ya dai sallame su ne.

A shekarun baya ‘yan Arewa su na ta addu’o’i da fatan Allah ya maido da mulki a hannun su, domin su na ganin za su sami sauƙin rayuwa da dawwamammen tsaro a yankin idan nasu ke mulkin ƙasar, sai ga shi wasu su na cewa ana zargin wuta ne maƙera sai ga ta a masaƙa. Shin ka na ganin irin wannan siyasar da mutane ke yi ta naka-naka ne ko naka sai naka ta na da alaƙa da samun tsaro da kuma samun abubuwan more rayuwa a yankin da gwamnati ke mulki ta fito?

To ai ɗaya daga cikin abubuwan da ake fuskanta ke nan a ƙasar nan wato siyasa da ƙabilanci. Ko su kudanci a lokacin da Jonathan ke kan mulki duk abin da Jonathan ya yi ‘yan ɓangaren sa ba sa ganin laifin shi, to ‘yan Arewa su sai su ka juya su ka ga ba haka ya kamata su yi ba. Ɗaya daga cikin dalilin da ya sa mutane su ka cutu kenan, su na ganin idan naka ya hau kan mulki duk laifin da ya yi ko duk gazawar da ya yi sai ka ƙi fitowa ka ce ga laifin shi ga gazawar shi don a yi gyara. Shi ya sa Arewa ta daɗe ta na mulki amma babu abin da za ka fito ka nuna ka ce ga abin da Arewa ta amfana da shi; masana’antun mu sun mutu, makarantun mu na Gwamnati sun lalace, harkar noma an watsar da ita an koma wa man fetur, tsaro ya tavarɓare.

To idan aka duba waɗannan abubuwan gabaɗaya sai a ga cewa wannan ya na da nasaba da rashin faɗa wa shuwagabanni gaskiya saboda ko dai addinin ku ɗaya ko kuma qabila ɗaya. To wannan ya na ɗaya daga cikin matsalar da ake fuskanta kuma ya na da kyau a canja a dinga faɗawa shuwagannin gaskiya. Idan wannan mulkin ya kuɓuce a hannun ‘yan Arewa to dawowan sa kuma sai dai Allah. Ya kamata idan naka na a waje tun kafin ya bar wajen a tilasta masa sai ya yi abin da ya dace. Ba wai ɗora ɗan Arewa shi ne kawai ba, a’a ya na da kyau ya kasance an yi wa mutane aiki su gani yadda kowa zai amfana da shi.

Kamar yadda talauci ya yi yawa a ƙasar nan, talakawa su ka shiga halin-ha’ula’i a wannan lokaci, wani ba shi da abincin da zai ci har ka ga yunwa ta yi masa illa. Wasu daga cikin manya masu kishi da qaunar talakawa su na bayar da taimako ko tallafi na hannu da hannu ga mabuƙata irin su marayu da nakasassu da marasa ƙarfi. Shin ka na ganin irin wannan hanya da wasu su ke bi za ta taimaka wajen rage raɗaɗin talauci idan da yawa su ka bi wannan hanyar?

To abu na farko dai maganar kawar da talauci ba magana ce kawai ta ba mutane sadaka ba ce ko kyauta, magana ce ta Gwamnati ta yi abin da ya kamata wajen ganin cewa an yi adalci da gaskiya, kuma a fito da dabaru daban-daban na bunƙasar tattalin arziki wanda zai taimaka wa mutane don su samu aikin yi.

Taimako da tallafa wa mutane ya na da kyau domin zai ɗan rage wani zafin, amma idan ana son mutane su amfana sosai shi ne a tabbatar da cewa an tada masana’antu an taimaka wa masu harkar noma sannan a taimaka wa mutane da jari, kuma masu hoɓɓasa musamman mata su ma a taimaka masu da jari, wanda abin da mu ka sa gaba ke nan a lokacin ina Sanata. Kuma idan ana so komai ya daidaita dole sai an bi ta wannan hanyar, domin idan mutane su ka cigaba da zama cikin talauci da fatara, matasa kuma babu aikin yi, to za a zo a yi juyin juya hali a ƙasar nan fiye da wanda aka yi na #Endsars, domin idan ban manta ba wannan zanga-zanga da aka yi samari ne su ka haɗa ta, to idan ba a magance wannan talauci da fatara da yunwa da mutane su ke ciki ba to wanda ya faru a baya kamar wasan yara ne.


To ran ka ya daɗe, mun gode
To madalla. Ma’assalam