Kada ki tsaya jiran dama, ki zama dalilin samuwar ta – Marie Curie 

Spread the love

“Bai kamata ka kalli abin da aka riga aka yi ba, ka mai da hankali kan abin da za ka iya yi”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS 

A cikin wannan shafi mai farin jini na Gimbiya, muna ci gaba da haskaka rayuwar mata jarumai, waɗanda suka tsallake rijiya da baya, suka fuskanci ƙalubalai masu tsanani, amma suka tsaya tsayin daka har suka zama abin koyi ga al’umma.

Kamar yadda ku ka sani wannan shafi ba kawai shafin bayar da labaran rayuwar mata ba ne, wuri ne na ilmantarwa da tunatarwa, inda ake fito da rayuwar mata domin ta zama madubi ga sauran mata masu neman hanya.

A wanna makon kamar yadda muka yi maku alƙawari za mu ɗora daga inda muka tsaya kan rayuwar jaruma kuma macen da ta kafa tarihi a harkar kimiyya da har yau ba a samu wadda ta fi ta ba, wato Marie Curie. Saidai kafin nan, za mu ɗan yi waiwaye wanda aka ce ado na tafiya. 

Idan Manhaja ta wakon baya bata wuce ku ba, za ku shaida mun kawo tarihin wannan jajirtacciyar mace da yadda ta yi gwagwarmayar rayuwa, da kuma tarin ƙalubalen da ta ci karo da su a lokacin neman ilimi, da kuma yadda duk da matsin lambar da ke akwai a zamanin ga ‘ya’ya mata a ɓangaren ilimi bai hana ta neman sa ba, hakan kuwa zai ƙara tabbatar maka da irin jajircewar da take da ita.

Marie Curie ta sha wahala mai tarin yawa a hanyarta ta neman ilimi wadda ko ɗaya bisa ɗari za ta iya zama hujja ga wasu na jingine karatun bakiɗaya.

Bari mu fara da amsar tambayar da muka kwana Shin wane irin farashi ne Marie Curie ta biya na wannan namijin aiki da ta yi?

Bayan manyan nasarorin da Marie Curie ta samu, rayuwa ba ta sauya zuwa sauƙi ba kamar yadda mutane za su yi tunani. A maimakon haka, wani sabon babi ne ya buɗe, babi mai cike da nauyin suna, nauyin alhaki, da kuma sababbin ƙalubale da ba su da alaƙa da rashin gata ko talauci.

Yayin da sunanta ke yawo a duniya, ana girmama ta a matsayin babbar masaniya, amma a bayan wannan girmamawa akwai wata rayuwa mai cike da gwagwarmaya. Domin kasancewarta mace a ƙololuwar kimiyya, har yanzu akwai waɗanda ke kallon nasararta da shakku, wasu na ƙoƙarin danganta duk abin da ta yi ga mijinta, wasu kuma na ganin matsayinta bai dace ba. Amma ta riga ta saba da irin wannan gwagwarmaya.

Ba ta tsaya ba. Ba ta waiwaya baya ba. Ta ci gaba da tafiya a kan hanyar da ta fara, wato hanyar bincike, gano gaskiya, da kuma hidimtawa al’uuma.

Bayan rasuwar Pierre Curie, duniya ta ƙara karkata hankalinta gare ta. Ta zama abin koyi, abin kallo, abin yabawa. Amma wannan girma ya zo da wani nauyi, nauyin zama mace da ke wakiltar dukan mata a fannin da maza suka mamaye.

A wasu lokuta, ana kallonta ba a matsayin Marie Curie kawai ba, ana mata kallon matsayin “mace a kimiyya.” Duk wani kuskure da za ta yi zai zama hujja ga masu cewa mata ba su dace da wannan fanni ba, duk da haka ta ɗauki wannan nauyi ba tare da ƙorafi ba.

Ta mayar da hankali kan aikinta. Ta ci gaba da bincike, ta kafa cibiyoyi, ta horas da sabbin masana kimiyya, musamman mata.

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka bambanta Marie Curie shi ne yadda ba ta takaita nasararta ga kanta ba. Domin ta buɗe ƙofofi ga sauran mata masu tasowa, ta koyar da abinda ta sani ko ta yi bincike kansa, sannan ta jagoranci wasu kan yadda za su koyi binciken. 

Wataƙila wannan matakin ne ya sanya ta samu magajiya a cikin ‘ya’yanta 

‘Yarta Irène Joliot-Curie ta zama ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gaba da wannan tafiya, har ta kai ga samun lambar yabo ta Nobel, ma’ana dai ta bi sawun mahaifiyarta.

ɗaukar shekaru da ta yi tana tu’ammali da radiation ba tare da kariya ba sakamakon ƙoƙarin da take yi na fitar da manyan ababen da a yau muke morsa tare ceton rayuka da su, jikin Marie Curie ya haɗuwa da matsala sakamakon illar da radiation din ya yi wa jikin. Wannan ne za mu iya kira sila na mutuwar wannan jarumar mace. 

A lokacin da take aiki da radiation, duniya ba ta fahimci cikakken haɗarin da ke tattare da shi ba. Ita kanta Marie Curie ta yi aiki da waɗannan sinadarai ba tare da kariya ba.

Akwai lokutan da take ɗaukar radium a hannunta, tana kallon yadda yake haskawa a duhu, ba tare da sanin cewa wannan haske na ɗauke da haɗari mai tsanani ba.

Shekaru sun ja, yayin da ayyukanta suka fara tasiri, saidai lafiyarta ta fara rauni, jikinta ya fara gajiya, saidai har zuwa ƙarshe, ba ta daina aiki ba.

Hakan zai kai kai mu ga tambayarmu ta gaba ta shin mutuwar Marie Curie na nufin shuɗewar dukka ayyukan da ta gina?

A shekarar 1934 ne tarihi ya tabbatar da mutuwar Marie Curie, wadda ya bayyana mutuwar tata a matsayin sadaukar da rayuwa don ceton rayuwar al’uuma mai zuwa da kuma sawwaƙa harkar lafiya. Saidai wannan mutuwar tata ba ta zama ƙarshen labarinta ba.

Har kawowa yau, kowane lokaci aka yi amfani da radiation domin gano cuta, to tabbas akwai wani ɓangare na aikinta a ciki. Kuma duk lokacin da kalmar kimiyya ta halarto wani wuri, to fa dole ne a tuna da Marie Curie, kuma ba za a tuna ta a matsayin wadda ta ɗan taka rawar gani ba, za a tuna ta ne a matsayin ginshiƙi.

Marie Curie ta buɗe ƙofa ta zurfafa tunani akan yadda ake kallon mata a ɓangaren ababen da za su iya yi. Kuma ta tabbatar da cewa, babu wani aiki da aka keɓance wa maza su kaɗai, ko ina mata za su iya shiga a harka ta ƙirƙira ko dogon tunani da ilimi, saidai idan matan ba su so ba ko ba su sa juriya irin tata ba.

Rayuwar Marie Curie babbar darasi ce ga rayuwar mata bakiɗaya, kuma hanya ce da zata iya zama ƙwarin gwiwa ga mata da suke so su bar tarihi. Sannan ta ilimantar da mata cewa, duk fa wanda ya ɗauki hanyar cika wani buri, sai ya yi guzuri da haƙuri da juriya.

Marie ta rayu ba don jin daɗi ba sai don samar da abinda zata rayu har bayan mutuwarta. Ba ta yi bincike don zama wata ba, ko don neman ɗaukaka ba, maimakon haka ta yi don gano gaskiya wanda har ya kaita ga biyan farashin gaskiyar da rayuwarta. Wannan ita ake kira da Gimbiya, macen da ta shiga cikin duhu ta fito da hasken da duniya ke amfani da shi har kawowa yau.

Rayuwar Marie Curie ita kanta darasi ce. Kuma kalamanta sun kara bayyana irin tunanin da ke tare da ita.

 Ko akwai wasu kalaman hikima da take faɗa?

Akwai kalamai na hikima da dama da take faɗa waɗanda har zuwa yanzu suna tasiri kamar, “A rayuwa babu abin tsoro, saidai akwai abin fahimta.” “Ba a samun nasara ba tare da sadaukarwa ba.”

Idan akwai abu ɗaya da za a ɗauka daga wannan labari shi ne, rayuwa ba ta tambayar inda kika fito, saidai tana kallon inda kika nufa.

Marie Curie ta fito daga duhu, amma ba ta tsaya kallon duhun ba. Ta nemi haske, ta kuma zama hasken da duniya ke gani.

By ukarofi

Leave a Reply