Ba mu yarda da danniya a APC ta Gombe ba – Buba Kwacam

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A cikin wannan kaka ta siyasa da ke ƙara ɗaukar zafi a fagen siyasar Najeriya, an samu wasu takun-saƙa da suka fi jan hankalin jama’a, musamman a ɓangaren siyasar Jihar Adamawa. Daga cikin batutuwan da suka mamaye tattaunawar siyasa akwai takarar kujerar majalisar dattawa da ke haɗa sunan Hon. Abdurrahman Buba Kwacam da kuma gwamna mai ci a yanzu, Ahmadu Umaru Fintiri.

Lamarin ya soma ɗaukar hankali ne tun bayan da ake zargin gwamnan ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. Wannan mataki ya haifar da rashin jituwa a tsakanin wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar, waɗanda suka nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira “hawan ƙawara”, suna masu cewa matsayin gwamna na iya ba shi cikakken iko da damar da za su iya mayar da sauran masu neman takara saniyar ware.

Masu wannan ra’ayi sun bayyana cewa, idan aka bar irin wannan tsari ya tabbata, waɗanda suka shafe shekaru suna wahala da jam’iyyar za su iya zama ‘yan kallo a lokacin rabon dama, alhali su ne suka gina jam’iyyar tun farko.

Wannan yanayi ne ya kai ga fara nuna wa juna yatsa tsakanin gwamna da Honarabul Buba Kwacam, musamman ganin cewa dukkansu sun fito ne daga zone guda tare da zawarcin kujera iri ɗaya.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani taron manema labarai da ya gudanar, Hon. Kwacam ya buƙaci jam’iyyar APC ta yi wa kowa adalci a tsarin zaben fidda gwani, yana mai cewa abin da suke nema kawai shi ne gaskiya da daidaito.

“Mu za mu tafi zaɓen fidda gwani, kuma muna kira ga uwar jam’iyya saboda muna ƙaunarta ta yi mana adalci, kada ta yi mana zalunci. A tafi zaɓe; idan Allah Ya ba shi, Kwacam zai taimake shi. Idan kuma Allah bai ba shi ba, shi ma ya taimaki Kwacam,” inji shi.

Yayin da aka tambaye shi ko akwai wani abu da suke hangowa wanda zai iya haddasa matsala ko kuma yake ba su tsoro, Hon. Buba Kwacam ya bayyana cewa tuni suka fara jin wasu raɗe-raɗin da ke nuna yiwuwar kauce wa tsarin zaɓe.

“Yanzu ma ba a fara ba, domin muna jin rade-radin cewa za a kawo list daga shugaban ƙasa. Kuma ka san wani lokaci jita-jita kan zama gaskiya. Wai saboda matsalar tsaro ba za a yi zaɓe ba,” inji shi.

Ya ci gaba da bayyana rashin gamsuwarsa da wannan hujja ta rashin tsaro, yana mai cewa ya zagaya wurare da dama a yankin ba tare da samun wata matsala da za ta hana gudanar da zaɓe ba.

“Ni da na je Mubi na yi sati uku, na je Madagali, na je Maiha, na je Mubi North da Mubi South. Sauran ‘yan takara ma babu wanda bai je ba, kuma babu inda ba a gudanar da harkokin siyasa. Sai yanzu ne za a fara maganar rashin tsaro?” ya tambaya.

Da aka sake tambayarsa kan irin matakin da za su ɗauka idan aka yi masu abin da suka kira “cin ƙarfi”, Honarabul Buba Kwacam ya bayyana cewa siyasa ba ta tsaya kan jam’iyya guda ba, yana mai nuni da cewa akwai hanyoyi da dama da ‘yan siyasa ke iya bi idan aka tauye musu haƙƙinsu.

“Wannan zaɓen fidda gwani ne, kuma ba jam’iyya ɗaya ce kawai take da damar tsayar da takara a Najeriya ba. Don haka dole mu faɗa wa jam’iyyarmu gaskiya duk da tana da zafi,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Ba za mu yarda da wani ɗauki-ɗora ko dibilwa ba, a kama hanya a wuce ace kawai an yi zaɓe. Mun zuba ido muna kallo, kuma za mu shawo kan lamarin. Duk wanda ya yi ba daidai ba zai ga ba daidai ba.”

Kalaman nasa sun sa manema labarai suka sake matsa masa kan ko yana yin barazana ne ko gargaɗi dangane da abin da zai iya biyo baya idan aka tauye musu haƙƙi.

Sai dai Honarabul Kwacam ya amsa cikin salon da ya sake tayar da hankali a wajen taron.

“Ka jira ka gani. Duk inda aka yi irin wannan abu ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Duk inda aka yi cin ƙarfi, idan aka yi wa mutum danniya su talakawa ba za su gyale ba, za su ɗauki mataki, kuma shi kansa wanda ya yi ba zai iya hana su ba.”

Da aka tambaye shi ko yana ganin irin wannan yanayi na iya jawo wa jam’iyyar APC matsala a babban zaɓe, Kwacam ya ce talakawa ne suke da ikon yanke hukunci na ƙarshe.

“Idan an danne mutane, talakawa masu zaɓe ba za a iya danne su ba. Akwai zaɓen da idan mutum ya ci, ba za ka iya cewa bai ci ba. Ai ana maguɗi ne a inda babu ra’ayi,” inji shi.

Da aka tunasar da shi tsarin yarjejeniya da APC ta taɓa amfani da shi wajen zaɓen shugabannin jam’iyya, Honarabul Buba Kwacam ya ce wannan yanayi ya bambanta da abin da ke gaban su yanzu.

Ya bayyana cewa, a wancan lokacin an riga an ware mukamai tun kafin fara sayen fom, amma a wannan karon an bari mutane sun kashe kuɗaɗe wajen sayen fom kafin a fara maganar a janye wa wani.

“An bar mutane sun siye fom, sannan a dawo ana cewa wane ya bari, wane ya bari. To wallahi ba a isa ba,” inji shi cikin sigar nuna rashin amincewa.

Daga nan sai ya sake jefa wata tambaya mai ɗaukar hankali:

“Shin wani matsayi ne yake da shi a wajen Allah da ya fi na kowa da za a ce a jaye masa?”

A ƙarshe, yayin da aka tambaye shi yadda yake ji kasancewar yana neman kujera iri ɗaya da gwamna mai ci, sai Hon. Buba Kwacam ya yi dariya kafin ya mayar da martani cikin salon da ya ja hankalin mahalarta wannnan taron.

“Ka na maganar Ina takara da gwamna mai barin gado? Shi ba mutum ba ne? Gwamna fa mutum ne, kuma Kwacam ma mutum ne,” inji shi.

Ya kuma tunasar da manema labarai yadda tsohon gwamna Jibrilla Bindo ya sha kaye duk da yana kan mulki a lokacin.

“Lokacin da ya kada gwamna Bindo ai yana kan mulki ne, amma shekara huɗu kawai ya yi. Wanda yake tunanin zai iya kaɗa shi, amma Allah bai ba shi mulkin ba? Don haka ba na tunanin ina tsaya wa takara da gwamna ne; Ina tunanin ina takara ne da mutum kamar ni.”

By ukarofi

Leave a Reply