NUT a Oyo ta umarci malamai su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar malaman Nijeriya (NUT) reshen Jihar Oyo ta umarci dukkan malaman makarantun firamare da sakandare na gwamnati su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026. Matakin ya biyo bayan sace malamai da ɗalibai da aka yi a ƙaramar hukumar Orire ta jihar.

A cikin wata sanarwa da Shugaban NUT na jihar, Hassan Fatai, da sakatare, Salami Olukayode, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda waɗanda aka sace ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane. Ta ce lamarin ya jefa malamai, ɗalibai da iyayensu cikin fargaba tare da kawo cikas ga harkokin ilimi a jihar.

Ƙungiyar ta ce yajin aikin na da nufin matsa wa gwamnati da hukumomin tsaro lamba domin su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ceto malamai da ɗaliban da aka sace cikin gaggawa ba tare da wani sharaɗi ba. Ta kuma buƙaci dukkan malamai su bi umarnin yajin aikin tare da fifita tsaron rayukansu.

NUT ta nuna goyon baya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, tana mai alƙawarin ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa har sai an kuɓutar da mutanen da aka sace. Ƙungiyar ta jaddada cewa kare rayuka da tabbatar da tsaron makarantu da al’ummomin makaranta na daga cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba.

By ukarofi

Leave a Reply