Yaƙi ya dawo sabo tsakanin Amurka da Iran bayan sabbin hare-hare

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Yaƙi tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar wani sabon salo bayan Amurka ta kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a ƙarshen mako, yayin da Iran ta mayar da martani da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. Rundunar Amurka ta ce hare-haren nata sun biyo bayan zargin cewa Iran ta harbo jirgin leƙen asirin Amurka mara matuƙi da ke shawagi a sararin samaniyar ƙasa da ƙasa.

A cewar CENTCOM, jiragen yaƙin Amurka sun lalata wasu cibiyoyin kariyar sararin samaniyar Iran, cibiyar sarrafa hare-hare da kuma wasu jirage marasa matuƙi da ake zargin suna barazana ga jiragen ruwa a yankin Tekun Fasha. Sai dai rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da aka yi amfani da shi wajen kai hari kudancin Iran.

Rahotanni daga ƙasar Kuwait sun ce an ji ƙararrawar gaggawa a sassa daban-daban na ƙasar yayin da tsarin kariyar sararin samaniya ke daƙile makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi. Duk da cewa hukumomi ba su bayyana cikakken bayanin hare-haren ba, Kuwait na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke ɗauke da manyan sansanonin sojin Amurka a yankin.

Tun bayan tsagaita wuta da aka cimma a watan Afrilu, Amurka da Iran na ci gaba da musayar hare-hare lokaci zuwa lokaci yayin da tattaunawar samar da yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa ke tafiya a hankali. Yaƙin da ya fara a watan Fabrairu tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da haddasa tashin farashin makamashi a duniya, musamman bayan tasirin rikicin kan mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur na duniya.

By ukarofi

Leave a Reply