NAHCON ta yi kwaskwarimar jigilar dawowar alhazai zuwa 3 ga Yuni, 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta fara aikin sauya tsarin jigilar alhazan 2026 yayin da masu ruwa da tsaki a Makkah suka fara shirin dawo da alhazai zuwa gida Nijeriya.

Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya yi kira agare su da su kasance masu haƙuri, haɗin-gwiwa da cigaba da inganta harkokinsu yayin da ya kuma yaba wa jami’ai bisa gudummawa ga harkokin hajji da walwalar alhazai.

Ya ce, an samu gagarumar nasara a aikin Hajjin 2026 duk da ƙalubalen da aka fuskanta na kula da walwalar mahajjata kimanin sama da miliyan 1.7 a ƙasa mai tsarki.

A cewarsa, “Hajji ibada ce da ke buƙatar sadaukarwa, juriya da haƙuri. Wajibi ne alhazai su zama cikin shirin fuskantar ƙalubalen da ba a iya kauce musu a irin wannan yanayi.”

Rahotanni sun bayyana cewa, Ambasada Yusuf ya bayyana cewa ƙalubalen gudanarwa ba dalili ba ne akan sakaci kuma NAHCON za ta yi aiki tare da hukumomin jigilar alhazai na jihohi, masu gudanar da harkokin lasisin tafiye-tafiye da sauran masu ruwa da tsaki wajen ɗaukar darasi daga aikin na bana.

Sanata Ali Ndume, wanda shi ne Shugaban ƙaramin kwamitin Majalisar Dattawa akan harkokin waje, ya bayyana Hajjin na 2026 a matsayin ɗaya daga cikin aikin hajji mafi kyau da tsari a kusan tsawon shekaru ashirin.

Ya bayyana cewa, an samu cigaba a fannonin lafiya a Mina, kula da masauki da tsaftarsa, da kuma wayar da kan mahajjatan akan kuɗaɗen waje cikin inganci.

By Babaji

Leave a Reply