Hajjin 2026: Shugaban NAHCON ya yaba wa gidajen jarida kan rahotanni, ya bayyana canjin da aka samu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya jinjina wa ‘yan jaridar Nijeriya bisa nuna ƙwarewa da juriyar aiki wajen ruwaito labaran da suak shafi aikin Hajjin 2026 dukda ƙalubalen gudanarwa da aka fuskanta.

Da yake ganawa da manema labarai a Makkah, Ambasada Yusuf ya yaba wa sadaukarwar ‘yan jarida wajen tabbatar da bayar da rahoto na daidai kuma akan lokaci.

Haka kuma, ya bayyana ire-iren ƙalubalen da tawagarkula da alhazai ta fuskanta musamman a fannonin kayayyakin gudanarwa da sufuri, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta sake nazari akan tsarin kasafinta domin inganta agajin gudanarwa don ayyukan hajji na gaba.

Sannan, shugaban ya faɗi nasarori da dama da NAHCON ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa da suka haɗa da inganta hanyoyin gudanarwa da hukumomin Saudiyya, ƙara yaɗa adadin fasaha, bunƙasa horar da ma’aikata, inganta harkokin sadarwa da kuma faɗaɗa shirye-shiryen wayar da kan alhazai.

Kazalika, ya ce an samu ci-gaba a ɓangaren kula da lafiyar mahajjata ta samar da cibiyoyin lafiyar da aka yi wa rajista da wasu matakan inganta lamuran gudanarwa.

A cewarsa, duk da cewa an fuskanci ƙalubale yayin gudanar da aikin hajjin na bana, hakan dama ce ta amfani da darussan da aka samu don inganta harkokin hukumar a nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply