NCDC: Najeriya na da kashi 59% kacal wajen shirin tunkarar Ebola

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Babban daraktan hukumar kula dake kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (Nigeria Centre for Disease Control and Prevention), Dakta Jide Idris, ya bayyana cewa Najeriya na da shirin kashi 59 cikin 100 ne kawai wajen fuskantar yiwuwar ɓullar cutar Ebola. Ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin sa ido da daƙile cututtuka, har yanzu akwai manyan giɓi musamman a filayen jiragen sama da iyakokin ƙasa masu sauƙin shiga.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi, Dakta Idris ya ce NCDC ta gudanar da bincike domin auna matakin shirin ƙasar da kuma gano wuraren da ake buƙatar gyara. Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fitar da ƙa’idoji da umarni ga hukumomi domin ƙarfafa sa ido kan matafiya masu shigowa ƙasar, musamman ta filayen jiragen sama da ke cikin jihohin da aka ware a matsayin masu haɗarin kamuwa da cutar.

Sai dai ya jaddada cewa manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta sun fi fitowa daga iyakokin ƙasa, inda mutane ke shiga ba tare da cikakken bincike ba. Ya ce darasin da aka koya lokacin da aka daƙile ɓarkewar Ebola a shekarar 2014 ya nuna cewa gano masu ɗauke da cutar da wuri, killace su, yin gwaje-gwaje cikin gaggawa da kuma bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da su na daga cikin mafi muhimmancin matakan kariya.

Shugaban NCDC ya kuma bayyana cewa a halin yanzu Najeriya na fama da ɓarkewar cututtuka bakwai zuwa takwas, ciki har da kwalara da zazzabin Lassa, waɗanda ke ci gaba da jawo asarar rayuka. Ya ce ana ƙoƙarin ƙara ƙarfin ɗakunan gwaje-gwaje, horas da ma’aikatan lafiya, samar da kayan kariya da kuma wayar da kan jama’a. Haka kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su ɗauki jagoranci wajen kare lafiyar al’umma maimakon dogaro da gwamnatin tarayya kaɗai.

By ukarofi

Leave a Reply