Ebola: Filin jiragen sama na Legas ya ƙarfafa aikin tantance matafiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumomi a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas, sun tsaurara matakan tsaro da ayyukan tantance fasinjoji bayan sake ɓallewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kwango.

Hukumar kula da harkokin Tashoshin Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), Jami’an lafiya na gwamnatin Jihar Legas da hukumomin lafiya na tashoshin jiragen ruwa sun gudanar da ziyarar sanya ido akan shirye-shiryen filin jiragen na kula da bayar dak sriya ga yaɗuwar cutar.

A cewar wata sanarwa da FAAN ta fitar ta jami’in hulɗa da jama’arta, Henry Agbebire, an gudanar da atisaye ne domin tabbatar da inganta cibiyoyin matakan bada agajin gaggawa da ƙarfafa wasu matakan kariya akan shigo da cutar zuwa Nijeriya ta filin mafi hada-hadar al’umma.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Kwamishinan Lafiya na Legas, Emmanuel Akinola Abayomi, ya yaba wa FAAN da sauran hukumomi bisa ɗaukar matakan da suak dace akan al’amarin ɓarkewar cutar Ebola a Kwango.

Ya bayyana cewa, wannan hoɓɓasa ta nuna yadda fannin lafiya a Nijeriya ke aiki tuƙuru wajen ganin an samu kariya daga yaɗuwar cututtuka acikin Nijeriya a cikin da ma ƙasashen waje.

By Babaji

Leave a Reply