
Rundunar Sojoji a ƙarƙashin Atisayen FANSAN YAMMA, ta yi nasarar ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su, tare da halaka ’yan ta’adda guda biyar yayin wasu atisaye a Jihar Zamfara da Katsina.
Haka kuma, sun ceto mutane 31 a yankin Bagega zuwa Kawaye da ke Ƙaramar Hukumar Anka ta Zamfara bayan harbin bom daga jiragen yaƙi a maɓoyar ’yan ta’addan a Dajin Bagega.
Rahotanni sun bayyana cewa, waɗanda aka ceton, sun shafe tsawon makonni da dama a tsare kuma ’yan asalin ƙananan hukumomin Maga, Gummi, Zuru, Wasugu, Bukuyyum, da Anka ne da ke jihohin Zamfara da Sokoto. Sannan, an duba lafiyarsu kuma za a sada su da iyalansu nan ba da daɗewa ba.
A wani samamen na daban a Zamfara, sojoji sun fafata da ’yan bindiga a yankin Maradun da Gidan Ɗan Jaja, inda suka kashe ’yan ta’adda biyu tare da rusa sansanoninsu da ƙwace bindigogi da babura huɗu.
A Katsina kuwa, sojoji sun tare wasu ’yan ta’adda da ke kan hanya domin kai hari a yankin Ruwan Godiya da hanyar Sayaya a Ƙaramar Hukumar Matazu. Bayan ƙazamin faɗa, sojoji sun kashe ’yan ta’adda uku.
Bugu da ƙari, an gano cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe na hannun daman shahararren ɗan ta’addan nan ne da ake kira Muhammad Fulani.
Kakakin rundunar sojin, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya tabbatar da cewa dakarun na FANSAN YAMMA za su cigaba da kai hare-hare domin murƙushe ta’addanci da dawo da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Yamma.
