Mace da kwalliya aka san ta

Daga MARYAM ABDURAHMAN

Mace da kwalliya aka san ta, wacce ba ta kwalliya ba ta cika mace a zahirin ta ba. Babu mace mummuna sai dai macen da ba ta kwalliya.

Sai dai kwalliyar ma kala-kala ce, wasu kwalliyar suna su ka tara, don ba zai yiwu a shafa ‘foundation’ a fuskar da ba ta da haske a yi tsammanin samun kwalliyar raɗau ba. In nace haske ba ina nufin farin fata ba, ina nufin ƙyalli na gyara.

Yawancin mutanen mu suna tsorata da maganar kayan gyaran jiki don tsadar su, a rashin sanin su da kuɗi ƙalilan za su sami biyan buƙata da kayan mu na gargajiya da kullum muke ta’ammali da su. Misali: riɗi, lalle, ɓawan kwai, lemon tsami da sauran su.

Inda matsalar ta ke, ya ake sarrafa waɗannan abubuwa har a sami biyan buƙata? Ku biyoni don jin sirrin.

1. Lalle
2. Ɗanyen riɗi.

A sami danyen riɗi a gyara shi, a daka sosai ya yi gari. A zuba ƙullin lalle a daka wuri guda. Bayan sun haɗe, a juye a ajiye a roba don anfanin yau da kullum.

Yanda za ki yi amfani da shi:
A ɗibi daidai yadda zai isa fuska, a kwaɓa da ruwa, a shafa. Bayan awa guda, a dirje kafin a wanke. A ranar farko za a ga canji.

Sirri na biyu:
Ɓawan ƙwai, kurkum, lemun tsami.
Duk da ba kowace fuska ce ke so ko karɓar lemun tsami ba, dan haka zan fi ba wa waɗanda ba su da matsala da lemun tsami shawarar amfani da wannan sirrin.

Ɓawan ƙwai za ki busar don ya yi sauƙin dakuwa. Ki nemi turmi ki daka ya yi luƙwi, ki haɗa da kurkum ki juye a roba don amfanin yau da kullum.

Kullum ki ɗiba daidai wanda ki ke buƙata cikin roba qarami, ki yanka lemun tsami guda ƙaya ko biyu yadda zai sami ruwa da kyau. Ki matse cikin haɗin ki, za ki ga ya yi kumfa, ki gauraya ya haɗe sannan ki shafa a fuska (fuskar da ba ta  son lemun tsami ka da a shafa a fuska) hannu, ƙafafu da ma dukkan jiki in ana bukata. A bari ya bushe, a yi wanka da ruwa mai ɗumi. Fuska za ta yi tsantsi da ƙyali tun ranar farko.

Sirrukan nan biyu kaɗai ya ishi mata gyaran jiki ba tare da kashe kuɗi ba. Duk kwalliyar da za ki yi ba tare da kin yi gyaran fuska ba za ki samu abin da ki ke so ba. Za ki iya yi sau uku a sati, ko ki jera sati ki na yin sirrin farko sai ki bari na sati biyu sannan ki sake yi. Ko ki yi sirri na biyu sau uku ko wani sati.