Sarautar Dan Buran Gobir da aka ba ni gadon gidanmu ce – Aminu Alan Waka

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano


A farkon shekarar nan ne ta 2021 Sarkin Gobir Alhaji Isah uhammad Bawa ya nada shahararren mawaki Alhaji Dakta Aminu Ladan Abubakar Ala, a matsayin Dan Buran Gobir, wanda aka yi wani kasaitaccen bikin nadin sarautar a can Masarautar ta Gobir, kuma jama’a da dama sun halarci bikin.Bayan kammala shagalin bikin nadin mun tattauna da Aminu Ladan Abubakar Ala, domin jin yadda ya samu sarautar da kuma alakar sa da Masarautar Gobir in da ya fara da bayyana mana cewar:


To yadda abin ya samo asali dai shi ne, ina da nasaba da Gobirawa, kuma salsalar mu ta tuke ne da Sarkin Gobir wanda ake kira Ibrahim Gwanki. Kamar yadda na fada a cikin waka ta ta Shahara. Amma wannan ya samo asali ne a lokacin da na rubuta wani Diwani, sai Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya ce, “wannan nasabar fa sai ka nemo ta cikakkiya saboda yanzu littafi za a yi wanda zai iya zama wani shaida ga al’umma, don haka ka tafi Kasar Gobir yadda za ka samo nasabar ka cikakkiya.


To a dalilin wannan littafin, sai kuma da aka bincika aka tabbatar da hakan ne, sai abin ya zamo cewar ruwa ya koma kwari, wannan shi ne silar samun wannan sarautar. Mahaifina shi ne Muhammad Sani Ladan kuma dan Abubakar, shi kuma Mijinyawa Kura ya haife shi, Mijinyawa Kura da ne ga Sarkin Baure wanda ake yi wa lakabi da Audu Sarkin Baure, shi kuma da ne ga Bawa Dan Gwanki, ba Ibrahim Dan Gwanki ba.

To Amma kafin sa, lokacin da shi Ibrahim Gwanki ya yi sarauta, an samu tazara mai tsawo kafin wani a cikin zuriyyar sa ya koma, shi ne sai aka samu Ibrahim Bawa dan Gwanki din kuma daga cikin reshen sa ne muka fita wanda a lokacin wajen yana tsuburi, amma ka san dan’uwan su wanda bai samu mulki ba ya dawo ya kafa sabon birnin Gobir wacce take yanzu a Nijeriya, Allah ya kaddara za a samu Gobir guda biyu, daya a Nijeriya daya kuma a Nijar bayan Turawa sun raba. To saboda haka nan ma gida ne, akwai gidan Gwankawa, gidan Jangwarzawa, gidan Nafatawa, gidan Yakubawa wanda a yanzu Yakubawa ne suke mulki.

To wannan shi ne dalilin da ya sa na samu sarautar Dan Buran din Gobir, kuma akwai sarautu na ’ya’ya na Masarautar Gobir wadanda aka saba ji kamar irin su Janjuna, Barzaki, to wadannan duk sarautu ne na ’ya’ya kamar su Sardauna da sauran su, ita kuma kan ta Dan Buran da Bagauda ya zo ya yi ta tun lokacin da ya kafa Kano kamar shekaru 800 tun kafin zuwan Fulani. Don zuwan Fulani a yanzu ana maganar shekaru 200 da wani abu. Don haka sarauta ce mai asali a cikin Hausawa, kuma su ne asalin Gobirawa.


To ko mene ne aikin Dan Buran a Masarautar Gobir?


Kamar yadda na fada a baya sarauta ce ta ’ya’yan Sarki, don haka tana amsa cewar Dan Sarki ne, sarauta ce da ba a bai wa kowa sai da da zai iya zama wakilin Sarki, kuma kamar a ce Yarima ko Ciroma, don haka Dan Sarki ne kamar zai iya gadon Sarki, don haka ba ta da wani aiki da yake a kan ta, saboda shi Buran din suna ne na wani daga cikin mukarraban Sarki Bagauda, kuma daga dan sa ne aka fara yin wannan sarauta ta can Buran, don haka ba wani aiki gare ta kebantacce a cikin masarautar ba, ita sarauta ce ta ’ya’ya.

Ko me ya bambanta wannan sarautar da sauran sarautun da aka ba ka a baya?

Wato ita sarauta tana da rukunnai. Akwai wanda ya gada sai a ba shi, saboda ta gidan su ce, kamar wannan ta Dan Buran din kenan. Akwai kuma ta karramawa a samu wani mutum mai amfani a cikin al’umma wanda yake kaunar masarauta, saboda kyakkyawar alaka sai masarautar ta ba shi sarauta don girmama shi, kamar irin sarautar da aka ba ni a Dutse, sarauta ce ta girmamawa da mutuntawa saboda wani aiki.


Don ka ga na yi wakar kasar Dutse da tarihin Masarautar kuma duk wani taro a masarautar ina zuwa a yi hidimar bikin da ni, har ma na kai taron ranar mawaka ta duniya aka yi taron a Dutse, wanda hakan ta sa na samu alaka da Masarautar Dutse da kuma Mai Martaba Sarkin, hakan ta sa na samu sarautar Sarkin Wakar Masarautar Dutse.


Ita kuma sarautar Dan Amana wadda na samu daga wajen Aminu Ado Bayero lokacin yana Sarkin Bichi, daman mutane sun san ni da shi tun yana Sarkin Dawakin Tsakar Gida ya zama Turaki, ya zama Wambai, duk muna tare da shi cikin soyayya, kuma ina tare da Masarautar Kano tun lokacin Marigayi Alhaji Ado Bayero ina ta yi musu waka, don na yi waka a kan kofofin Kano.

Sarakunan Kano na Fulani da sauran su, to ka ga lallai akwai alaka da ta da su tsawon lokaci, saboda haka lokacin da ya zama Sarkin Bichi babu wani mawaki da ya yi masa waka a lokacin ina Saudiyya har sai da na dawo na yi masa, da aka yi bikin babbar Sallah na je na gabatar da wakokin da na yi masa daga nan sai sauran mawaka suka biyo baya, amma kafin na yi babu wani mawaki da ya yi masa wakar ya zama Sarkin Bichi. To ai ka ga na ci Dan Amanar gidan Dabo, don haka har yanzu ’ya’yan Sarki da haka su ke kira na, Dan Amanar gidan Dabo.

To ganin an yi taron an gama lafiya, ko wane sako kake da shi ga jama’a?


Farko dai ina godiya ga Allah da Ya sa na samu wannan matsayi, wanda kuma karamci ne daga gare Shi. Sai kuma godiya ga Mai Martaba Sarkin Gobir Alhaji Isah Muhammad Bawa da ya zamar da ni dan gida a cikin Masarautar Gobir, sannan ina godiya ga dukkan jama’ar da suka halarci wannan babban taro da aka yi musamman wadanda suka je daga nesa da ma na kusa, kuma ina godiya ga dangi na da suka je daga Jega da sauran jama’a masu tarin yawa, Allah ya saka wa kowa da alheri.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *