UEFA ta fitar da zakarun ’yan wasa na 2020

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA), ta fitar da jerin ’yan wasan da masoya kwallon kafa suka zaba mata, a matsayin tawagar fitattun ’yan wasan ta na shekarar 2020. UEFA ta bai wa masoya kwallon kafa damar soma kada kuri’un su wajen zaba ma ta tawagar ’yan wasa 11 daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 6 ga Janairun da muke ciki, inda ’yan wasan Bayern Munich suka fi na kowace kungiya yawa.


Tawagar ta shekarar 2020 ko kakar wasan da ta kare, ta kunshi Manuel Neuer na Bayern Munich a matsayin mai tsaron raga. Masu tsaron baya kuma sun hada da Joshua Kimmich da Alphonso Davies dukkanin su daga Bayern Munich, sai kuma Sergio Ramos na Real Madrid da Virgil van Dijk na Liverpool.


A bangaren ’yan tsakiya akwai Kevin de Bryune na Manchester City da Thiago Alcantara na Bayern Munich, yayin da kuma mahara suka hada da Lionel Messi na Barcelona, Cristiano Ronaldo na Juventus da kuma tauraron PSG wato Neymar.


Gwarzon dan wasan duniya na FIFA Robert Lewondoski masoya kwallon kafa a duniya suka zaba a matsayin lamba taran tawagar kwallon kafar hukumar ta Turai (UEFA).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *