Kotu ta dage shari’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga Maris

Kotu ta dage shri’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga watan Maris

Daga AISHA ASAS

A Talatar da ta gabata babbar Kotun Jihar Kaduna da ke shari’ar jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky da matarsa  Zeenat, ta dage ci gaba da shari’ar ya zuwa ranar 8 da 9 ga watan Maris mai zuwa.

Kotun ta dage shari’ar ne biyo bayan hukuncin da Alkali Gideon Kurada ya yanke dangane da neman kotu ta ba shi lokaci da lauyan El-Zakzaky Mr Femi Falana ya yi a bisa wakilcin Mr Eddie Inegedu, domin ba shi damar nazarin wani bidiyo da wasu shaidu biyu suka gabatar wa kotun.

Lauya Inegedu ya shaida wa manema labarai kotun ta yarda da daya daga cikin shaidu biyun da masu tuhuma suka gabatar mata, amma ba ta amince da gudan ba saboda bangaren da ke kare wadanda ake zargi na da bukatar lokaci don ya nazarci hoton bidyon da aka mika wa kotun.

Game da ko Hukumar Gyaran Tarbiyya ta yarda da bukatar daukar Zeenat zuwa cibiyar killacewa don kula da cutar korona, Inegedu ya ce har yanzu ba su samu wani bayani a kan batun ba.

Jaridar Manhaja ta kalato cewa, Babban Lauyan gwamnati kuma Sakataren Din-din na Ma’aikatar Shari’ar jihar, Mr Chris Umar, wanda shi ne ya jagoranci tawagar masu gabatar da kara ya bayyana cewa, sun gabatar da shaida guda ga kotu sannan an dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 8 da 9 na watan Maris mai zuwa.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 25 ga watan Janairu ne Alkali Kurada ya ba da umarnin a dauki Zeenat zuwa cibiyar killace wadanda suka harbu da COVID-19 da gwamnati ta amince da ita bayan da aka gano ita ma ta harbu da kwayar cutar.

Kawo yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar wa kotu da shaidu guda 9 ciki har da sojoji guda biyu  da sauransu.    

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *