Cutar korona: NOA ta bukaci ‘yan Nijeriya su ba da hadin kai game da allurar riga-kafin korona

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Wayar da Kan ‘Yan Kasa ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina yarda da ra’ayoyi mara tushe da ake yadawa dangane da allurar riga-kafin cutar korona kan cewa maganin na tattare da wasu illoli. 

Babban Daraktan hukumar, Garba Abari ne ya yi wannan kira a lokacin bayanin kore zargin da wasu ke yi cewa ana so a yi amfani da allurar ne wajen takaita yawan al’umma, lamarin da Abari ya ce ba gaskiya ba ne.

Yana mai cewa, “Babu wata allurar riga-kafin da za a bari a shigo da ita Nijeriya ko a yi wa ‘yan Nijeriya ita ba tare da gwamnati ta yi bincike don tabbatar da sahihancinta ba.”

 A cewarsa, “Hukumar Kula da Inganci Abinci da Magunguna (NAFDAC) mai hakkin kula da ingancin magunguna a Nijeriya, da Hukumar Kula da Bunkasa Sha’anin Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) mai hakkin kula da sha’anin allurar riga-kafi a kasa, ba za su taba barin a shigo da wani maganin da zai cutar da rayuwar ‘yan Nijeriya ba.

“Hasali ma, riga-kafin COVID-19 din hadin fitattun kamfanonin hada magunguna da duiya ta san da su ne, wanda galibi su ne ke samar da magaungunan da duniya kan yi amfani da su wajen yaki da cututtuka daban-daban a sassan duniya ciki har da Nijeriya.”

Ya kara da cewa, “Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta tabbatar da ingancin magungunan bayan ta gudanar da cikakken bincike a kansu.”

 Don haka Abari ya ce, ba daidai ba ne yadda wasu shugabanni a sassan kasar nan ke zargin allurar da wata mummunar manufa. Daga nan, ya yi kira ga ‘yan siyasa, shugabannin addinai da sarakuna da su iya bakinsu sannan su rika amfani da ilimi maimakon dogaro da rashin tabbas don kauce wa jefa mabiyansu cikin rudani. A karshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ba da hadin kai su yarda a yi musu wannan allura idan lokacin ya zo.