Gwamnatin Tarayya ta kama hanyar kula da ilimin yara marasa galihu

Daga UMAR M. GOMBE a Abuja

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya wakilta Ma’aikatar Jinkai da Agaji da Kyautata Rayuwa ta Kasa, kan ta kula da shirin gwamnati na kokarin kula da yaran da suka daina tafiya makaranta a fadin kasa.

Da yake kaddamar da kwamitin mutum 18 da zai ja ragamar shirin a Talatar da ta gabata, Shugaba Buhari ya bayyana cewa ba daidai ba ne ganin yara suna gararamba a tituna da kasuwanni da sauran wurare, ba tare da suna zuwa makaranta ba.

Kwamitin zai yi aikinsa ne karkashin jagorancin Ministar Jinkai da Agaji Hajiya Sadiya Umar Farouq tare da takwaranta na ilimi, Malam Adamu Adamu.

Buhari ya ce, “Shirin zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da ya bai wa yara marasa galihu ilimin zamani.”

Shugaban ya ba da bakin cewa, “A gudanar da shirin ta hanyar ba da fifiko wajen karantar da darussan Lissafi da harshen Ingilishi da Ilimin Zamantakewa da kuma Kimiyya, ta yadda yaran za su koyi sana’o’i don amfanin rayuwarsu da kuma kasa.”

Ya ce, bisa la’akari da hasashen Majalisar Dinkin Duniya yara milyan 13 ne suka daina zuwa makaranta a fadin kasa, inda Hukumar Jinkai da Agaji ta hango bukatar da ke akwai a maida hankali wajen kula da ilimin yara marasa galihu a sassan kasa a matsayin wani bangare na kyautata rayuwar al’ummar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *