An yanke wa dan Turkiyya shekaru 1,075 a kurkuku

Daga Umar Mohammed Gombe

Wata Kotu a Istanbul na kasar  Turkiyya ta daure shugaban wata kungiyar asiri mai suna Adnan Oktar shekaru sama da 1,000 a bisa samun sa da aikata wasu laifuka 10, a cewar wata majiyar shari’a a kasar.

An kama Adnan Oktar mai shekaru 64 ne a shekarar 2018, a wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai a daidai lokacin da suke tsaka da miyagun laifuka, inda aka kama da yawa daga mabiyan sa wadanda yawancin su mata ne.

Ana tsare da shi tun watan Yunin 2018 a matsayin wani bangare na fatattakar kungiyar sa da sashen aikata laifuka na kudi na ’yan sandan Istanbul.

Kamar yadda gidan talabijin na NTB mai zaman kansa a kasar ya ruwaito a makon da ya gabata, ya bayyana cewa an yanke masa hukuncin shekara 1,075 sakamakon samun sa da laifuka da suka hada da cin zarafin mata, lalata da kananan yara, zamba da kuma yunkurin leken asiri na siyasa da soji.

Haka kuma an gurfanar da wasu mutum 236 da ake zargi a gaban shari’ar, inda 78 daga cikin su ke tsare a hannun hukuma, a cewar kamfanin dillacin labarai na Anadolu.

An bayyana cewa mutanen sun gabatar da cikakkun bayanai na karya da kuma aikata munanan laifuka na lalata da mata. Oktar ya shaida wa alkalin kotun da ke sauraron karar a watan Disambar 2020 cewa yana da kusan ’yan mata 1,000.

“Akwai tsananin kauna a zuciya ta ga mata. Kauna kuma dabi’ar mutum ne. Kauna ce ta Musulmi,” inji shi.

Ya kara da cewa a wani lokaci, “Ina da karfi sosai.” Oktar ya fara tsayuwa a bainar jama’a ne a cikin shekarun 1990 lokacin da yake shugaban wata kungiyar darika da ta afka cikin badakalar jima’i da yawa. Yana kuma da tashar talabijin mai suna A9 da ke kan Intanet, wadda ta fara watsa shirye-shirye a shekarar 2011, tashar da ake ganin ta jawo masa tofin Allah tsine daga shugabannin addinan kasar ta Turkiyya.

Daya daga cikin matan da ake yi wa shari’ar, wacce aka bayyana sunanta da CC, ta bayyana wa kotun cewa Oktar ya sha yin lalata da ita da wasu mata. An kuma ruwaito cewa Oktar ya kasance a baya mai wa’azi kan ra’ayoyin mazan jiya, amma daga bisani ya watsar ya shiga wata kungiyar asiri, inda yake bautar da mata, tare da sauya masu halitta zuwa masu kama da maguna da ke da kamanni iri guda. Sannan yana tilasta ma su yin rawa tsirara a gaban sa. Da yawa daga cikin matan sun bayyana cewa an yi musu tiyatar sauya halittar su. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *