Babban buri na kafin in bar duniya… – Aunty Bilkisu Funtua

Daga Aysha Asas

Wadanda suka dade da fara karance-karancen littattafan Adabin Kasuwar Kano tun wuraren 1993 ba shakka zan iya cewa sun sha cin karo da littattafan Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, wadda ake kira Aunty Bilki Funtua, domin ta kasance a sahun farko kuma tauraruwar da littattafanta ke ja a wancan lokacin. Saboda haka a tashin farko muka samu nasarar shigo muku da ita cikin wannan fili don jin wace ce ita, mene ne kuma burinta a halin yanzu sakamakon rashin jin duriyar littattafan ta a kasuwa na dogon lokaci. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance:

Masu karatu suna ta ji da karanta sunan ki a littattafan ki amma ba su san wace ce Aunty Bilkisu Funtua ba. A taqaice me za ki ce?

Suna na Hajiya Bilkisu Ibrahim Nabature, an haife ni a shekarar da Najeriya ta samu ‘yancin kai wato 1960, maigida na sunan shi Salisu Ahmadu, muna da yara biyu da shi Najwa da Nabila. Na yi makarantar firamare xi na a garin Funtua, sannan da na gama na tafi GGSS Malumfashi, bayan na gama a shekarar 1977 sai aka yi min aure a watan Agustan shekarar. Saboda haka ban qara ci gaba da karatu ba, sai na ci gaba da ‘yan hikimomin rayuwa irin namu na mata, wato na kama yin sana’a, domin idan kika dubi yawancin littattafaina ni mutum ce mai son mace ta dogara da kanta, ba wai ta dogara da miji ko iyayenta ba. To tun a lokacin sai in samu jarida da qyallaye in ta yankawa ina koyon dinki har na iya dinki da kaina babu wanda ya koya min. A dalilin haka a Funtua na yi suna kowa ya sanni da ‘Aunty mai dinki’ haka ‘yan mata da sabbin amare masu kawo min dinki suke kirana a lokacin.

‘Ya’yana kuma Alhamdulillahi sun yi karatun da nake ta nunawa ‘ya’ya mata masu karanta littafaina su yi, wanda ni ban samu na yi zurfi da karatun ba, sai ga shi ‘ya’yana sun yi min. Daya daga cikinsu ma tana qasar Amurka tana PhD ta kusa gamawa, dayar kuma ta gama digirin digirgir. Saboda haka na cimma wani buri a haka, ilimin da nake ba ‘ya’yan wasu ga shi na bai wa nawa. Yanzu haka dai ina zaune a garin Funtua ina dudduba takardun yara da suke kawo min don gyarawa, kuma ina haxa auratayya da sauran su.

Mutane za su so sanin lokacin da ki ka fara rubutu da kuma littafin da ki ka fara rubutawa?

Na fara rubutu a shekarar 1993 da ‘Wa Ya San Gobe?’ Lokacin da aka zo nema na in bada littafin za a kai wa Farfesa Tsiga ya dudduba domin maigida na ba ya son ya ga an rubuta shirme ko an kwaikwayi fina-finan Indiyawa, saboda haka sai na dauko labarin ‘Allura Cikin Ruwa’ da sauri saboda ban ga ‘Wa Ya San Gobe?’ ba, sai na ba shi aka tafi da shi suka duba a jami’ar Bayero, sun taimaka mana sosai kuma suka ce gaskiya rubutun ya yi ma’ana qwarai da gaske.

Menene ya ba ki sha’awa ko ya ja hankalin ki har kika tsunduma harkar rubutu?

To gaskiya babban abin da ya sa na tsunduma harkar rubutu shi ne yadda na ga a kowane fanni na rayuwa an bar ‘yan Arewa a baya musamman vangaren ilimin ‘ya’yan mata, sannan ga yawaitar rabuwar aure da ya zama ruwan dare. A kullum idan zan fita unguwa sai in ga mata masu qananan shekaru sun yi cincirindo a kusa da gidana da yake muna kusa da kotu ne, duk a tunani na masu kai talla ne, ashe duk shari’a ake yi da su akan mutuwar aure., kuma dukkanin su Hausawa ne babu Yarabawa ko Inyamurai ko wata kabila daban. Sai na yanke shawarar bari dai mu tashi tsaye mu aika da saqo cikin rubutu ko da garin Funtua kadai za a karanta dai na gode wa Allah in dai za a samu a rage wannan matsalar da ke addabar al’ummar mu, saboda a gani na babu abinda ke haifar da hakan illa rashin ilimi.

Zuwa yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?

Na rubuta littattafai 22.

Ki na karanta littafan wasu marubutan domin kwaikwayon irin salon su da hikimar da Allah ya yi musu?

E, ina yawan karanta littattafan ‘yan uwana marubuta, ba ma kamar na Hajiya Balaraba Ramat, da Bala Anas Babinlata da na Hafsat Sodangi, da kuma na Maimuna Idris Sani Beli da sauran su, domin ni ina son kalamai da maganganu masu ma’ana da gwanintar sarrafa harshe, to duk suna da baiwar hakan. Amma gaskiya ni bana kwaikwayar rubutun wani, sai dai da na karanta littafin ‘Wa Zai Auri Jahila?’ na Balaraba Ramat na dan kwaikwayi wani abun, amma ba jigon labarin ba.

Saboda haka duk lokacin da na karanta littattafan marubutan da nake sha’awar rubutun su ina qara jin qaimi da tsuma tare da qwarin gwiwar son yin rubutu, amma ba na kallon rubutun su idan zan yi nawa.

Yaya alaqar ki da sauran marubuta, shin ki na da qungiyar da ku ke dunqule waje guda domin habaka adabin Hausa da cigaban marubuta?

E, gaskiya ina da kyakkyawar alaqa tsakanina da marubuta, muna zumunci sosai da su, musamman ma Hajiya Balaraba Ramat idan muka hadu har ba mu son rabuwa saboda magana ta taru kuma an daxe ba a hadu ba; mu yi hirar duniya da zamantakewa da kuma irin cigaban da muka samu da qalubale. Kuma babu hidimar da za a gayyace ni da ta shafi rubutu da marubuta in gaza zuwa in dai babu wani uzuri a gaba na.

Ya ya za ki iya kwatanta rubutun da kuka yi a baya da kuma ire-iren rubutun marubutan mu na yanzu?

To! Kowa da zamanin sa, an so mu lokacin da muke zamanin mu, amma yanzu ma yaran suna qoqari wajen rubutu, sai dai gaggawa da suka sa a ransu, da sun yi haquri sun bi a hankali a tsanake kamar yadda muka yi a baya, domin gaskiya suna rubutu akan jigo mai ma’ana kuma a daidai lokacin da ake buqatar rubuce-rubuce irinsu.

Yawancin rubuce-rubucen ki kina yin su ne bisa jigon zamantakewar aure da rayuwar yau da kullum, kuma kina yawan nuna muhimmancin yin ilimi mai zurfi ga ‘ya’ya mata, ko hakan yana da alaqa da irin ra’ayin ki?

E, gaskiya ni Allah Ya yi ni mai tsananin kishin ‘ya mace, shi ya sa dukkanin rubuce-rubucena za ki dinga ganin ina nuna muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata, ba wai ina nufin dole sai mace ta yi karatu mai zurfi domin ta samu aikin yi ba, a’a aikin ma ina yake? Na fi son ta dogara da kanta, ta yi sana’a ta samu ‘ya’ya nagari. Matuqar uwa jaruma ce, tsayayya mai neman na kanta ba sakarya ba, to za ki ga an samu bambanci ko da a wajen ‘ya’yanta ne fiye da wadanda ba su samu ilimi da cikakkiyar tarbiyya ba.

A matsayin ki na marubuciyar littafai, kin taba sha’awar rubuta fim kamar yadda wasu marubutan suka ajiye rubutun littafi suka koma harkar fim?

Na ji dadin wannan tambayar. Gaskiya maganar fim na tava sa kaina, amma daga baya na haqura saboda haqqin aure ba zan yi abin da na ke so ba. Amma yanzu ni babban burina a harkar rubutu shi ne in ga na yi fim mai dogon zango, saboda yanzu babu nauyin komai a kaina, babu hidimar ‘ya’ya, babu miji, yanzu zaune nake ni kadai; zan so in je in zauna in ga an yi min abinda raina ke so, domin bana son in ga an cire min ko da kalma xaya ce cikin abinda na rubuta, saboda ina kallon duk kalmar da na rubuta mai muhimmanci ce, kin ga kuwa darakta ba zai yi min haka ba idan ba na wajen. Saboda haka burina kafin in bar duniyar nan in rubuta fim mai dogon zango, ko da daga cikin littattafai na ne.

Wadanne nasarori kika samu a harkar rubutu?

Gaskiya Asas rubutu ya yi min riga da wando, kuma duk arzikin da na ke ci yanzu ta sanadiyyar rubutu ne, na san jama’a fiye da tunani na inda duk na sauka ba na maraici a kaf jihohin nan namu, sai dai idan ban nemi masu karanta littattafai na ba wadanda muke mu’amala da su tun zamanin da na fara rubutu 1993. Ita Kano kuwa gida ce. Gaskiya alhamdu lillahi sai dai godiyar Allah.

Qalubale fa?

Kai! Gaskiya qalubale ba iyaka, domin a wancan lokacin mu ne gaba-gaba wajen rubuta littattafan kasuwar Kano, saboda haka malamai suka sako mu a gaba, gani suke yi kamar za mu bata yara, ba a bambancewa da wanda ke rubuta soyayyar batanci da sakarci da kuma ire-iren rubutun da muke yi akan zamantakewar aure. Wanda ina ganin cewa idan aure ya gyaru, to dukkan al’umma ma za ta gyaru.

A lokacin da ki ka fitar da littafin ki na farko mai suna ‘Allura Cikin Ruwa’ a 1993, to ya yanayin kasuwancin littattafai a lokacin, ya kuma za ki kwatanta shi da yanzu?

A lokacin da na yi Allura Cikin Ruwa na daya  gaskiya ya fito da gagarumar sa’a, mutane suka kama karanta littafin, saboda ban fitar da shi gaba daya ba, Farfesa Gusau suka bani shawarar yin hakan, sai mata suka dinga neman na biyun ruwa a jallo duk da na farko sharar fage ne kawai ban ma kai ga tsunduma cikin rigingimu ba, saboda rigima da harqalla ita ke riqe mai karatu, amma haka suka dinga zumudin karanta na biyun, sai na yi na biyu aka kai shi kasuwa. To fa lokacin da na ukun ya fito, sannan rigima ta kai intaha komai ya rincabe, to haka nan da nan aka kwashe littafin kamar yadda ake rubinbin gasasshen nama, a iya Kano kawai kwafi dubu uku suka qare sai da aka sake buga wasu saboda sauran jihohi, amma yanzu kasuwar littafi ai ta zama abin da ta zama.

Masu karatu da dama suna tambayar sun daina ganin sababbin littattafan ki a asuwa. To ko kin daina rubutun ne ko kuwa hutawa kike yi?

Ban daina rubutu ba, kawai dai yanzu yanayi ne kin san jiki da jini, amma ba don ba ni da abun rubutawa ba. Da a ce gwamnati ko wata hukuma za ta kirani ta ce Aunty Bilkisu muna son ki yi mana rubutu akan fyade ko almajiranci ko wani abu mai muhimmanci to da zan so hakan; musamman littafan da za a dinga koyar da yara a makarantu.

Menene fatan ki ga wannan jarida?

Fatana Allah Ubangiji Ya sa ta fito a sa’a.Ya daukaka darajar ta. ya ba ta farin jini, Ya kuma albarkaci ma’aikatanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *