28
Jul
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kyaftin ɗin Liverpool, Jordan Henderson ya koma Al-Ettifaq mai buga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya. Ɗan ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 33 ya amince da ƙunshin yarjejeniyar fam miliyan 12 har da ƙarin tsarabe-tsarabe. A sakon ban kwana da ya yi wa Liverpool, ya ce zai bar ƙungiyar inda ya yi kaka 12, wadda ya lashe firimiya da Champions League a ita da sauran nasarori. Henderson yana Liverpool tun bayan da ya koma Anfield daga Sunderlandn kan fam miliyan 20 a watan Yunin 2011. Ya buga karawa 492 da cin ƙwallo 33 da bayar da…
