09
Oct
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al'umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda a kuma dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a matsayin kwamishinar jinƙai ta jihar. Wakilin Blueprint Manhaja, MAHDI…
