Macen da ba ta da abin yi na saurin gundurar namiji – Aisha Adamu Sadiq

“Wasu matan babu ce ke jefa su halin rashin kamun kai”

Daga AISHA ASAS

Masu azancin zance suna cewa, sana’a goma maganin mai gasa. A wannan makon shafin Gimbiya na jaridar Manhaja ta ɗauko maku matashiya mai sana’ar sarrafa fara, siyar da abayoyi, akwatuna da ma haɗa lefe bakiɗaya.

A tattaunawar Manhaja da matashiyar, ta tavo yadda sana’ar siyar da fara ke bayar da abin rufa asiri, saɓanin yadda mutane da dama suke kallonta a matsayin shiririta. Sannan kuma ta yi ƙarin haske kan yadda sana’arta ta haɗa lefe ke gudana.

Babban fatanmu dai mata su amfana da wannan shafin, ta hanyar ilimantuwa ko samun ƙwarin gwiwa ko kuma zaburarwa ga waɗanda ke zaman kashe wando. Don haka mata, idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Aisha Adamu Sadiq:

MANHAJA: Shin wacce ce Aisha Adamu Sadiq?

AISHA ADAMU: A taƙaice dai kamar yanda ki ka faɗa , sunana Aisha Adamu Sadiq wadda aka fi sani da Ayeesh Chuchu a kafafen sada zumunta. Ni haifaffiyar garin Bakori ce a Jihar Katsina. Na yi ‘primary’ da ‘secondary school’ ɗina duk a Jihar Katsina. Daga nan na tafi FCET Gusau inda na yi NCE da Degree a fannin ‘Chemistry Education’.

Mece ce sana’arki?

Ina sana’ar siyar da fara da aka yi ‘packaging’ a zamanance, sannan ina siyar da akwatuna, abayoyi da duk nau’in kayan sawa na mata. Ina kuma haɗa lefe dan sauƙaƙa ma waɗanda ba su san taya za su fara ba.

Mu fara da sana’arki ta farko, wato sana’ar fara. Wasu na kallon sana’ar kamar ta fi da a kira ta da sha’awa kawai, wai ba ta cika kawo kuɗi ba. Shin ya zancen yake?

To, ai a duniyar nan da aka samu cigaba babu ƙaramar sana’a. Sai dai ace idan mutum bai san hanyoyin da zai bi wajen inganta sana’ar ta tafi da zamani ba. Yanda kafafen sada zumunta suka yi yawa za ka iya amfani da su wajen jawo hankalin jama’a har dubban jama’a su siya. Sana’ar fara sana’a ce mai samar da riba sosai , da in ka laƙance ta, to fa ka sha kwana.

Ita sana’a dama ta na buƙatar ka san yanda za ka sanyawa abinda ka ke siyarwa farashin da ya dace. Bayan ka yi lissafin komi. Inda matsalar take da yawa da ka muke shiga sana’a shi ya sa ba ma gane samun da ke cikin wannan sana’a. A gaskiya ban ɗauki sana’ar fara a matsayin ‘side hustle’ ba. Sana’a ce mai zaman kanta da zata ma komi na rayuwa.

Kin yi maganar haɗa lefe. Shin tariya ake yi na kuɗi a wurinki, ko adashe ne ake yi na lefen, koko dai kawai ana zube kuɗin ne ke ki siyo?

Kowane ya danganta da ƙarfin kwastoma. Da yake ina da tsari na ‘packages’. Akwai ƙarami, mai bi ma shi har zuwa sama. Sannan akwai tsarin tariya, na a riqa siyen kayan kaɗan-kaɗan har a gama haɗawa. Akwai kuma waɗanda za su ce a yi masu lissafin daidai kuɗin da suke son kashewa su biya take. Wasu kuma suna bin tsarin ‘package’ da muke da shi su zaɓi dai-dai da aljihunsu, shi ma ɗin wasu su biya take, wasu ayi yarje-jeniyar biya sau biyu ko fin haka. Duka dai muna bin yadda kwastoma ke son ya yi tunda ƙarfi ba ɗaya ba.

Ba mu labarin lokacin da ki ka ɗau anniyar fara sana’a. Waɗanne irin hanyoyi ki ka bi?

Tun bamma san miye amfanin sana’a ba nake sha’awar juya taro da kobo. Da farko dai yin sana’ar nake da ka banda ilimin sana’ar. Tunda na yi sana’o’i da dama kafin na karkata akan waɗanda nake yi yanzu.

Sana’ata tafi karfi a soshiyal midiya, ita ce hanyar da na bi ta farko har mutanen da ke kusa dani suka san ina yi, saboda ni mutum ce dake son keɓewa. Na fi zama gida a duk lokuttan da bana makaranta ko wajen aiki. So na yi amfani da ‘social media’ wajen tallata sana’ata. Zan iya cewa babu ‘platform’ ɗin da ba na tallar sana’ata, daga kan su Facebook, Instagram, Twitter, LinkedIn da WhatsApp. Saboda duk wata ƙaramar ‘yar kasuwa na buƙatar ‘visibility’.

Hakan ya sa na tashi haiƙan na nemi ilimi akan yanda ake kasuwanci a kafafen sadarwa, saboda abin ya wuce wai ka yi ‘posting’ ka ce a zo a siya. Dole ka bi wasu matakai da za su sa mutane su aminta da kai har su siya kayanka.

Me ya sa ki ka zaɓi yin irin waɗannan sana’o’i?

Zan iya cewa dukka sana’o’in zaɓa ta suka yi, saboda ban taɓa tsammanin zan yi su ba. Abu ne ya faru kamar almara; hoton fara kawai na ɗora a ‘status’ na WhatsApp ɗina, shi ma mun yi ta ne a gida ta ci, shikenan mutane kamar wasa suka yi ta tambayar ko ni ke yi. Sai ƙawayena Rafee’ah da Amiera suka ban shawarar in yi.

Kamar washegari naje kasuwa na siyo duk abinda nake buƙata. Wanda a lokacin dubu uku na kashe, na yi farar dubu shida.

Haka ɓangaren abayoyi da kayan sawa ya faru a lokacin ‘lockdown’. Mutane ba su da damar zuwa kasuwa, ga shi ba daɗewa a ka shiga azumi. Mun san yanda hidimar sallah ke kasancewa. Na yi amfani da wannan damar na fara sana’ar kayan sawa na mata don sauƙaƙawa mutane. Alhamdulillah! Daga nan muka zarce, kin san dama ita sana’a daga zarar mutane sun san kana saida abu shikenan. Wasu ko wani suka ji yana nema za su turo shi wajenka.

Sana’a tana da ma’anoni da dama, kowa da irin yadda yake fassara ta. A wurinki wane gurbi ki ka ajiye neman na kai?

A wajena neman na kai na nufin neman abinda zaka rufawa kanka asiri, ka fi ƙarfin buƙatunka. Ka gujewa roƙo , maula da bambaɗanci. Neman na kai na ƙarawa mutum natsuwa da barin shiga abinda bai shafe ka ba, saboda da ka tashi tunaninka na ga yanda zaka juya biyar ta zama goma.

Mu koma ɓangaren iyali. Ko kina da aure?

A’a banda aure, amma dai muna hanya In sha Allah.

A firarmu da wata a kwanakin baya, ta faɗa cewa, yanzu samari ma sun fi son mace mai sana’a. A taki mahangar me ki ka fahimta?

Alal haƙiƙa haka ne. Saboda wasu mazan na ganin macen da bata da abin yi a matsayin nauyi. Saboda macen da ba ta da abin yi zata yi saurin gundurar namiji musamman a irin yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki. Kullum gaban shi na faɗuwa game da buqatar da za ta zo ma shi da ita. Ita ce bani kuɗin anko, data ta ƙare, kuɗin kayan shafa da sauransu. Amma idan mace na da abin hannunta ba zata tsaya sai anyi ma ta ba. Sai dai shi namiji a karan kanshi ya yi don ihsani wanda ita zamantakewa dole sai da ihsani da kyautatawa.

Wacce shawara ce za ki ba wa mata masu zaman kashe wando?

A gaskiya an bar yayin zaman kashe wando a wannan lokacin. Saboda ita sana’a ‘security’ ce ga rayuwar mace. Musamman wacce ta ke a matakin tasowa. Sana’a na taimaka wa wajen hana mace roƙo ko zubar da mutunci, da dama wasu matan babu ce ke jefa su cikin halin rashin kamun kai. Amma kina da sana’a babu wata burga da za a maki saboda kina bakin ƙoƙarin ganin Allah ya rufa ma ki asiri. Duk mace mai sana’a ta fi ƙarfin wulaƙanci, saboda da wuya ta yi abinda za a wulaƙanta ta. Da sana’ar nan zaka taimaki kanka, ‘yan’uwa da al’umma. Ba abinda ya fi hakan daɗi. Ya kamata mata su tashi tsaye su nemi na kansu don su rufawa kansu asiri. Babu wanda ya san gobe, amma sana’a babbar makami ce ga rayuwar ‘ya mace.

Wasu matan na ƙorafin rashin jari ne ke hanasu sana’a. Wacce shawara ki ke da zuwa gare su?

Wannan ba hujja ba ce, akwai sana’o’in da jari kaɗan suke buƙata ka fara su, kuma cikin ikon Allah ka ga sana’ar ta haɓaka. Kamar ni da dubu uku na fara sana’ar fara. A rana ɗaya na maida linkin kuɗin. A wata ɗaya na ajiye linkin ba linkin kuɗin a asusu na. Matsalarmu ita ce hangen na sama da mu, sai mu ce ala dole irin sana’ar da wance ke yi zan yi kuma kamar yanda take yi. Bayan ita ɗin a lokuttan baya ba haka ta ke ba.

Yanzu an samu cigaban da akwai sana’o’in da mutum baya buƙatar jari ma. Iyawarsa kawai ake buqata. Duk a soshiyal midiya ɗin nan ne. Ko ni ina wasu daga cikinsu, kuma a biya ni in kalmashe kuɗina. Shawarata anan ita ce, mace ta san miye muradinta, abinda ta ke da sha’awa, sai ta yi amfanin da shi wajen ganin ta cimma burinta a hankali. Rashin jari ba zai zama hujjar da zata hana sana’a ba. Akwai skills irin su ‘social media management’, ‘ads settings’, ‘copy writing’ da sauransu waɗanda iyawa kawai ake buƙata.

Sanar da mu ƙalubalen da ki ke cin karo da su a kasuwancin da ki ke yi.

Babban ƙalubalen da na fi cin karo da shi shine, harkar ‘delivery’, tunda mafi yawan masu siyen kayana ba kusa suke ba. Wajen tura kaya ina fuskantar matsalar vacewar kaya ko kuma a samu tsaiko wajen tura kayan. Wanda hakan na jawo saɓani tsakanina da kwastoma musamman idan ba a dace da mai fahimta ba.

Nasarori fa?

Alhamdulillah! Babbar nasara ita ce, fin ƙarfin buƙatuna. Zan kuma iya ɗaukar ta wani da yardar Allah. Ba sai na jira ko na roƙa ayi mun ba. Sannan na mallaki abubuwan da ban yi tsammanin zan mallake su ba duk a dalilin sana’a. Ka yi suna ma a sana’arka ita ma nasara ce babba. Saboda a duk lokacin da mutane suka ji wani ko wata na neman mai haɗa lefe ko saida fara ina zuwa a zukatan mutane da dama inda za su yi ta ‘recommending’ ɗina.

Menene muhimmancin ilimin ‘ya mace ga al’umma?

Ilimin mace na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban. Ance “idan mace ta samu ilimi kamar dukka al’umma ce suka samu.” Saboda ita uwa ce mai bada tarbiyya. Bada ingantacciyar tarbiyya ba ya yiwuwa sai da ilimin addini da na boko. Duk matar gidan da ke da ilimin addini da boko za ki ga tarbiyyar yaran gidan ta bambanta da ta saura, saboda tana amfani da iliminta wajen gudanar da gidanta.

Ta wacce hanya ce ilimin mace zai iya amfanar da mijinta?

Na farko wajen tafiyar da ragamar gidanta. Mace mai ilimi zata yi amfani da ilimin wajen zama abokiyar shawara ga mijinta. Za ta iya ba shi shawarwari ta hanyar amfani da iliminta.

Ta fannin tafiyar da gida, zata iya taimaka wa wajen rage ma shi wani kaso daga cikin nauyin da ya rataya wuyansa. Haka ta fannin kula da yara. Mace mai ilimi tana bada gudunmuwa sosai a rayuwar gidanta.

Wane buri ki ke da shi a wannan kasuwancin naki?

Babban burina in ga na mallaki kamfanin sarrafa fara, kamar yadda masu sana’o’i na ‘production’ ke buɗe kamfani. Saboda akwai kayan aiki na zamani da nake buƙata waɗanda za su sauƙaƙa mun wajen harkar sarrafa farar.

A yanzu shi ne babban burin da nasa a gaba. Ɗayar sana’ar ta saida kayan sawa na mata kuwa sana’a ce da ko a cikin gida zan iya ware waje in yi abu ta, saboda hakan ma na taso na ga mahaifiyata na yi.

Yaya matsayin kwalliya ta ke ga mata?

Duk inda mace ta ke dama ita ‘yar kwalliya ce, da kwalliya aka santa. Shiyasa ma za ki ga suturar mata ta fi saurin tafiya walau a yanayin bukukuwan sallah ko ba a lokacin ba. Bare kuma yanzu da muke zamanin abubuwan kwalliya na mata iri-iri. Mafi yawan mata na son shiga yayi don kar a bar su a bawa.

Wane irin kaya ki ka fi son sakawa?

Na fi son saka abaya. Saboda ina jin daɗin saka ta, babu takura. Sannan ko’ina zaka iya shiga da ita.

Wane abinci ne mafi soyuwa gare ki?

A duk cikin abinci na fi son ɗanwake. Ɗanwaken kuwa kowane iri ne indai sunanshi ɗanwake to zan ci shi.

Mun gode.

Ni ce da godiya da ku ka ba ni wannan damar ta tattaunawa da ni. Na gode ƙwarai.