An tsige Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Kevin McCarthy

A ranar Talata ‘yan Majalisar Wakilan ƙasar Amurka suka tsige Kakakin majalisar, Kevin McCarthy, bayan kaɗa ƙuri’ar jin ra’ayi.

Wannan al’amari wanda tarihin siyasar ƙasar ba zai mance da shi ba, ya jefa ‘yan Jam’iyyar Republican a majalisar cikin ruɗani.

Da wannan mataki da ‘yan majalisar suka ɗauka, yanzu ya zama wajibi su zaɓi wanda zai maye gurbin McCarthy.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan wanda za a zaɓa a matsayin sabon kakakin Majalisar.

Kodayake dai ‘yan majalisar sun naɗa Patrick McHenry na Carolina ta Arewa a matsayin muƙaddashin kakakin Majalisar ya zuwa lokacin da za a naɗa sabo.

Wannan dai shi ne karon farko da irin haka ya faru a Majalisar Wakilan Amurka inda aka tsige wani Kakakin majalisar.