Daga UMAR GARBA a Katsina
Allah Ya yi wa shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Hajiya Binta Ola rasuwa.
Hajiya Binta ta rasu ne da misalin ƙarfe 3 na daren jiya Talata, a gidanta dake Sabuwar unguwa Ƙofar Ƙaura, dake jihar Katsina bayan gajeruwar rashin lafiya.
Majiyar mu ta ce za a yi jana’izar marigayiyar a wannan Laraba da misalin ƙarfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar unguwa cikin garin Katsina.