Janar Musa ya nemi Ma’aikatar Kasafi ta bai wa ayyukan tsaro muhimmanci

Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya nemi Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare da ta bai wa ayyukan tsaro muhimmanci.

Janar Musa ya bauƙaci hakan ne yayin ziyarar aiki da ya kai wa Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ranar Talata a ofishinsa da ke Abuja.

Cikin sanarwar da ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar tsaro, Tukur Gusau, Musa ya nemi Ma’aikatar da ta ware wa rundunar sojoji kaso na musamman domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da samar da ƙarin gidaje ga sojoji da sauransu.

Daga nan Janar ɗin ya bai wa Ministan tabbacin sojoji za su ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsu wajen daƙile matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.

Da yake maida jawabi, Minista Abubakar Bagudu ya yaba da ziyarar da Janar Musa ya kai masa, tare da jinjina wa sojojin Nijeriya bisa ƙoƙarin da suke yi wajen bai wa ƙasa da al’ummarta kariya duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Bagudu ya bai wa sojojin Nijeriya tabbacin samun goyon bayan ma’aikatarsa don ci gaba da inganta yanayin aikinsu.

Kazalika, ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan himmar da Shugaba Bola Tinubu ke yi don ganin bayan matsalolin tsaron ƙasar nan.

Janar Musa ya kai ziyarar ne bisa rakiyar manyan hafsoshi daga Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.