Da me matan banza suka fi na gida? (2)

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinmu na zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A makon da ya gabata mun kawo muku maudu’i kan mai matan bariki suka fi matan aure har wasu mazan suke tsallake matansu na aure suna biye wa ‘yan bariki? Mun fara kawo muku dalilai har guda 7. A yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya.

  1. Iya abinci: Matan wajen suna bai wa mazansu abinci. Wata ma a nan take wanke masa duk wani laƙani don mallake shi. Za ka ji namiji yana zancen abincin budurwarsa kamar bai taɓa cin abinci mai daɗi ba. Matan waje suna vata lokaci su koyi girki don su birge samari don a ci gaba da ba su tallafi. Kuma a mafi yawancin lokuta da kuɗinsa ake girka wannan abinci.

Toh abinda maza da yawa ba su sani ba shi ne, wani zubin, ba iya girki ne kaɗai yake sa abinci ya yi daɗi ba. Kana buƙatar kayan girki na musamman irin sukayan ƙamshi. Ni kaina matata tana sayar da kayan ƙamshi na kamfanin Herbalicious idan kana so ka saya ka kai gida, sai a tuntuɓi wannan lambar : 09128077508.

Idan kana so ka ci abinci mai daɗi, sai ka inganta cefanen gidanka. Kuma a riƙa saka wa madam data tana hawa Youtube don koyon dabarun girki da yadda ake girki.

  1. Iya magana: Matan waje sun iya magana. Duk yadda za su maka magana mai daɗi sun sani. Kai ka ce don su aka saukar da hadisin Al-kalimatul ɗayyiba as sadaƙa. Suna ƙoƙari sosai ta wannan fannin. Ɗaya daga cikin salo na matan waje shi ne, irin su voye sunan namiji kamar su ce baby, sweetheart, love, Honey, Habibi, da sauransu.

Su kuwa na cikin gida, wata idan ka ji yadda take magana da mijinta yadda ka san ta ci kashin mahaukaci. Babu ladabi, babu basira, babu ɗa’a, babu sanin fasahar zance. Hajiya dole sai kin gyara. Misali, idan za ta kira mijinta kai tsaye take cewa “Saminu gishiri ya kare”. Ko kuma ta kalle ka ta ce wa ɗan ka, zan ci ubanka, duk da ta san uban yana jin ta.

  1. Soyayya: Matan wajen kai ka ce Sharukh Khan ne ya haife su saboda iya soyayya. Za a so ka kamar ba gobe. Amma matsalar ita ce, da an yi aure, sai su ɗaga shinfiɗa su ajiye soyayyar a bakin get. Ita soyayya ita ce ginshiƙin aure. Yana da kyau ki karanci maigida don ki san wacce irin kalar soyayya yake so. Akwai wani marubuci mai suna, Gary Chapman. Ya wallafa wani littafi mai suna, “The Five Love Languages”. Yana da kyau ki karanta shi don ki koyi harshen soyayya ko yarukan soyayya. Ta hakan ne za ki koyi yadda za ki burge magida.

A ƙarshe, ina so na ja hankalin matan cikin gida da su sani cewa, matan wajen ba su fi su da komai ba. Idan kika ga matar waje ta fi ki, to ke kika so. Duk abinda take yi ke ma za ki iya. Banbancinku kawai niyya ce. Kowa da niyyarsa. Idan niyyarki ita ce ki gyara aurenki, toh tabbas za ki yi.

Sannan yana da kyau ‘yanuwana maza su sani. Duk kyan matar waje, toh ta gida ta fi ta. A gurguje, zai wuya matar cikin gida ta saka maka cutar ƙanjamau ko kuma sanyi ko kuma ciwon hanta, wanda dukka cututtuka ne masu haɗarin gaske. Sannan yana da kyau ka sani, duk sanda ka ɗauki matar banza, to hankalin ka ba ya kwanciya sai kun rabu, domin ba ka san da wa za ka haɗu ba, ko kuma me zai same ka a yayin da kake aikata wannan aikin masha’ar ba?

Sannan Matar banza sai ta karɓi kuɗinka sau ɗari ba ka ma san me za ta yi da su ba. Wata da kuɗinka take kai ka wajen boka don a lalata zaman lafiyar cikin gidanka. Wata kuma idan shu’uma ce, sai ta ajiye shaidar hotuna ko hirar da kuka yi don wata rana ta yi amfani da su a kanka. Wani zubin sai ka manta ma, ka zama wani hamshaƙin mutum ko ka shiga siyasa. Sannan za ta fito ko ta ɓata maka suna, ko kuma ta yi maka barazana tana karɓar kuɗinka, ko kuma ta kai wa maƙiyanka su biya ta. Sannan kuma duk inda ta zauna aka yi maganarka, sai ta faɗi irin yanayin mu’amalar da kake da ita.

Da wannan ne nake cewa, idan akwai wani abu da ban fada ba, za iya ku iya tuntuɓa ta don mu tattauna. Nagode.

Muhammad Ubale Kiru, baƙon marubuci ne a wannan shafi na Zamantakewa. Shi ya warware mana wannan maudu’i mai albarka. Muna godiya, Allah ya saka masa da alkhairi ya raya masa zuri’a.

MuhdKiru

Imel: [email protected] Lambar waya: 07087789463