“Samarin yanzu ma sun fi son mace mai sana’a”
Daga AISHA ASAS
Mai karatu yau fa mun zo da abinda ba ku yada gani ba, mace da ta tabbatar da zancen ba sana’ar da namiji zai yi da mace ba zata iya ba matuƙar ta sa wa ranta za ta iya.
A daidai wannan lokacin da mata suka miƙe, suka yi tarayya wurin kama sana’ar kayan qawa na mata da maza, kama daga tufafi, takalma zuwa huluna, gyale da sauransu, waɗanda su ne sana’oin da aka cika ganin mata na yi.
A cikin haka ne, aka samu wata matashiya da ta yi tsalle, ta fice daga inda yake na walwalar mata, ta hanyar fara sana’a da aka fi alaƙanta ta da maza, wato sana’ar kayan gwari.
A tattaunawar Manhaja da matashiyar, za ku ji dalilin da ya sa ta zaɓi wannan sana’a da kuma hanyoyin da ta ke bi wurin cin kasuwarta, bayan ta sanar da mu taƙaitaccen tarihin rayuwarta tare da wasu shawarwari ga mata da matasa bakiɗaya.
Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Basmah Sulaiman:
MANHAJA: ZA mu so jin tarihin rayuwarki.
UMMU SODEEQ: Ni dai sunana Basmah sulaiman, an haife ni a cikin garin Jos, na yi makaranta a jos, kuma yanzu haka ina aure a cikin garin Jos.
Mece ce sana’arki?
Ni ‘yar kasuwa ce, Ina saida duk wani abu da ya danganci kayan abinci, tun daga kan kayan gwari, kayan hatsi, kayan ɗanɗano da kuma kayan marmari.
Wasu za su yi mamakin irin sana’ar da ki ke yi, a matsayinki ta mace, kasancewar an fi sanin maza da irin wannan sana’a. Me ya sa ki ka zaɓi yin sana’ar?
To gaskiya tun da na taso nake matuƙar ƙaunar duk wani abinda ya shafi noma da shuke shuke, dan zan iya ce miki ko fushi nake yi indai aka ɗauke ni aka kai ni kamar lambu haka to In sha Allah kashi hamsin cikin ɗari na fushin zai sauka, to soyayya ta ga harkar noma na daga cikin abinda ya sa na tsunduma wannan kasuwanci.
Tabbas maza aka sani da sana’ar kayan gwari, dan ko a da mata sukan siyo kaɗan ne su dinga kasawa a gida, amma yanzu zamani ya sauya, sana’o’i da dama an zamanantar da su, sai kiga ana haɗaka akan sana’ar da da maza aka sani da ita ko mata.
Ba mu labarin yadda ki ka faro sana’ar?
Akwai wasu abokaina mata a kafar sada zumunta ta Facebook da suke yin irin wannan sana’ar, kasancewata mai son kayan lambu a duk lokacin da suka ɗora sai hakan ya yi ta birgeni, har na taɓa zuwa inbox ɗin wasu daga cikin su na nemi shawarwari da ƙarin bayani, to ban fara a lokacin ba gaskiya, sai wata rana da wani ɗan’uwa da yake sana’ar muka gaisa da shi kawai sai na fara tambayarsa yaya tsarin kasuwar da kuma yanayin farashin kaya, yamin bayani dalla-dallah kawai na ce ya turo min hotunan kayan, a take na fara tallatawa, to kamar wasa dai ga shi har yanzu ana yi.
Ko kin ci karo da wasu ƙalubale a sana’ar taki?
In har aka ce wannan sana’a ce to fa dole a samu ƙalubale a ciki, sai dai kowacce da irin nata, musamman sana’ar kayan gwari, tana ɗauke da ƙalubale kala-kala, saboda kaya ne da ba su ajiyuwa na tsawon lokaci, to babban ƙalubale na farko shi ne rashin tsayuwar farashi, duk wanda yasan gwari yasan ba ta da tsayayyen farashi sai yanda kasuwa ta yi, alal misali, zan iya siyan kaya da safe akan farashin dubu ɗaya, zuwa yamma farashin zai iya sauyawa, zai iya hawa ko ya sauka, to wannan shi ma qalubale ne dan za ka iya faɗawa ‘customer’ kuɗin kaya kaza ne in farashin ya sauya wasu lokutan ciko zai iya biyoka, sannan ƙalubale na biyu shi ne, matsalan direbobi, wasu lokutan akan samu matsala direba ya isa bai kira me kaya ba, ko kuma ‘park’ ba su loda maka kaya da wuri ba, sai ki ga kayan sun lalace, shiyasa ba kowacce tasha ce muke kai saƙo, muna duba wane ‘park’ ne ya fi yawaitar zirga-zirgar, wanda nan da nan suke lodi sai mukai.
Ta wacce hanya ki ke bi wurin siyar da taki sana’ar?
Ina amfani da kafafen sada zumunta irinsu Facebook, Instagram, Whatsapp da tik tok wajen tallata hajata, don gaskiya zan iya cewa 100% na ‘customers’ xina dukka ‘online’ na samo su daga garuruwa mabambanta har da na ƙasar waje.
Shin za a iya kiran sana’a a matsayin dole ga mata?
Eh gaskiya a wajena amsar eh ce, saboda sana’a tana siyawa mace mutumci, duk macen da ta dogara da kanta za ki samu duk wani yawon gulmace gulmace, qananun maganganu babu ita a ciki, saboda tana da abinda zai ɗauke hankalinta, sannan sana’a tana qarawa mace qima a idon mijinta, babu ruwanki da yawan bani-bani duk wata buƙata taki da ta taso za ki iya magance ta daidai gwargwado. Ko samarin yanzu sun fi son mai sana’a ko ba komai za ki tare wani abin.
Za mu so jin nasarorin da ki ka samu a wannan sana’ar?
To alhamdulillahi nasarori kam mun samu da dama, dan daga fara sana’a ta zuwa yanzu bazan iya ƙirga adadin mutanen da suka siya kaya a wajena ba, wanda gabakiɗayansu babu wanda ya tava gani na, suka yarda suka turo min da kuɗaɗensu, tabbas wannan babbar nasara ce a wajena, ciki kuwa har da masu muƙaman siyasa, sannan akaf faɗin Arewa babu jihar da ban tura kaya ba, sannan da wasu jihohi na kudancin ƙasar nan, sannan mun tura Amurka sau biyu, Nijar sau ɗaya.
Wane kira za ki yi ga matasa kan bin sawun da ki ka taka kan ta’ammali da kafafen sada zumunta?
Kiran da zan yi ga matasa shi ne, su sani cewa kafafen sadarwa yanzu sun wuce wajen da mutum zai je hira da ‘charting’ da samari ko ‘yan mata kawai, in har mutum yasan hanyar da zai sarrafa su to tabbas za su sanya abinci a cikin kwanonsa har da na waninsa ma, akwai arziki sosai a ‘online’, matsawar kana saka data kullum kana ‘scrolling’ a waɗannan kafafen, to fa ka sani zaman banza da rashin abin yi saidai in kai ne ka so, saboda kana da babban jari a hannunka ( wato kafafen sadarwa) saidai in baka san hanyar sarrafa su ba.
Wane alfanu mata suke samu a kasuwanci a kafafen sadarwa?
Gaskiya akwai alfanu sosai da mata suke samu a kasuwancin kafafen sadarwa, akwai mata da yawa da ta’ammuli da mutane a zahiri yakan ɗan ba su wahala, kamar ni haka gaskiya bani da saurin sabo da mutane, so yawan shiga cikinsu yana ban wahala, a saboda haka kasuwancin kafafen sadarwa ya bamu damar tallata kayanmu ba tare da mun shiga cikin jama’a ba, muna daga gida za mu tallata kayanmu in an samu ‘customer’ ayi ‘packaging’ a tura masa, sannan kasuwancin kafafen sadarwa na ba ki damar sanin mutanen da wataƙila koda kuɗi ba lallai mu’amala ta haɗaku ba, amma sanadiyyar wannan sai kiga har zumunci ya ƙullu.
Akwai mata masu zaman kashe wando, wane kira ki ke da shi gare su?
Matan da suke zaune babu wani abin yi a wannan yanayin da muke ciki na tsadar rayuwa su sani zama haka babu sana’a ba hanya ba ce mai ɓullewa, akwai ‘yan ƙananan buƙatunki da bai kamata ace ko yaushe saidai ki kaiwa miji ki ce ya miki ba, suma suna gajiya, ga buƙatun gida ga na yara, amma in ya kasance mace tana ɗan juya biyar ta zama goma to ba iya buƙatar ki kaɗai ba har na wani da ke kusa da ita zata iya ragewa. Ita sana’a rufin asiri ce.
Ko akwai abinda ya bambanta irin naki kasuwanci da sauran waɗanda mata ke yi na kayan sakawa da sauransu?
Gaskiya akwai bambanci sosai, ni sana’a ta ta kayan abinci ce, mukan ɗaure a kwali ko a buhu wanda dole sai kin ɗauki yaran aikin da za su dinga yi .iki wannan hidimar kina biyansu.
Sannan kayan mu ba kamar kayan sakawa ba ne, duk inda muka samu matsala da direba ko tasha to fa wani lokacin tunanin yin asara ne yake fara ziyartar zukatanmu saɓanin kayan sawa ko za su yi wata a hannun direba babu abinda zai same su.
Sannan masu kayan sawa kullum ‘design’ cin kayan da za su wallafa yana da bambanci da na jiya, mu kuma kayan abincin dai da aka sani su ɗin ne muke sake wallafawa.
Sannan kamar ɓangaren ‘joint delivery’, wato a haɗa kayan mutane da dama da suke gari ɗaya waje guda, masu kayan sawa za su iya haɗa na mutum goma ma waje guda, mu kuwa in har siyayyar kowanne da yawa hakan ba zai yiwu ba.
Sanar da mu irin ƙalubalen da ki ka dinga cin karo da su a sana’a ta intanet.
Daga cikin ƙalubalen da na fuskanta akwai wani lokacin da na samu ‘customer’ daga patakwal, siyayyar ta na farko kenan a wajena, lokacin gab zaɓen shugaban ƙasa ne, ta yi siyayya sosai muka kai kaya ‘park’ muka biya suka ba mu lambar direba, ya kamata ta karɓi kayanta kafin zaɓe amma har ranar zaɓe shiru, lambar direba a kashe, sai daga baya tukunna suka kirata kayan gaba ɗaya sun lalace, daga ƙarshe dai sai mayar mata da kuɗin na yi.
Sannan akwai ƙalubale na ‘scammers’ masu vata ma sauran ‘yan kasuwa suna, za ki ga wasu suna buƙatar kayan da ka ke siyarwa, amma wataƙila saboda an taɓa cutar su a kafar sadarwa da sunan kasuwanci sai kiga suna jin tsoron aika maka kuɗi.
Wane buri ki ke da shi kan sana’ar da ki ke yi?
Ko wacce sana’a akwai irin burin da ake so a cimma, ni nawa burin shi ne, ina so nan da wasu ‘yan shekaru kaɗan na ga na fara ‘exporting’ kayan abinci zuwa ƙasashen ƙetare, sannan ya zamana muna da rassa a kowacce jiha a faɗin qasar nan yanda duk masu buqatar kayayyakin mu ba za su samu wata matsala ko shan wahala wajen samu ba, za su iya samu cikin sauƙi.
A wannan lokaci da muke ciki da matsin rayuwa sai ta’azzara yake yi. Wane kira za ki yi ga mata kan taimakon mazaje a buƙatun gida?
To mata mun sani yawan bani-bani ba shi da daɗi, ko ke ce aka dama da bani-bani watarana za ki yi ƙorafi to bare wanda rayuwarsa kullum cikin ɗawainiyya da wasu yake. Kamata ya yi ace ‘yan qananun buƙatunki kina da hanyar samun kuɗin shiga wanda za ki dinga magance su, wani namijin ma in kina so ku samu matsala da shi kice masa bani, musamman in ki ka tambaya a lokacin da babu, amma in kina da ‘yan canjin ki wasu buƙatun ma saidai ya ga anyi, to shawarata dai ki ɗan samu abinyi ko kaɗan ne ya fi babu.
Wane kalar abinci ki ka fi son ci?
To gaskiya ina son abinci sosai dan bazan iya ware wanda na fi so ba, in na ce wannan sai na tuna da wancan. Amma dai ina son faten rama sosai.
Wacce irin kwalliya ki ka fi sha’awa?
Gaskiya ina matuƙar son kwalliyar atamfa, a duk sutura atamfa ce ba a dena yayinta baya ga haka ma tana da sauƙin sawa ba takura, saboda ba ta fiye zuwa da nauyi ba.
A fahimtarki mace ce matsayin kwalliya ga mata?
Kwalliya ita ce mace, mace ita ce kwalliya, macen da bata kwalliya ma ko a sahun maza baza a saka ta ba don maza ma suna kwalliya, wato matsayin kwalliya ga mace yakai idan har bata yi to za a iya cire ta a sahun mata, kwalliya bawai iya ta fuska ba ce kwalliya, kwalliya ta jiki da muhalli ita ce kwalliya.
Mun gode.
Ni ma na gode.