‘Janar’ Kawankwaso: Daga ina zuwa ina?

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Wani hatsabibin marubuci wato Robert Green wanda ya wallafa littafin “48 Laws Of Power” ya kawo wata saɗara mai muhimmanci da ke cewa; “The moment of victory is a moment of danger because you’re tempted to press your luck…”

Bayan zaven 2015, Kwankwaso ya bunƙasa ya tumbatsa a siyasar Jahar Kano, ya zama Sanata, ya naɗa Gwamna da mataimakinsa, ragowar Sanatoci biyu wato Gaya da Barau dole sun yi masa bai’a sun bi, kai duk wata kujera tun daga ‘yan Majalissa Jiha da na Tarayya duk nasa ne.

Ya kai siyasar gidan Shekarau gargarar mutuwa.

A qasa kuwa ga shi, shi ya yi na biyu a Primary Election, Buhari da qyar ya sha, sannan ga shi ya zarce tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Atiku, Wohoho! Duk alƙaluma na nuna cewa haƙiƙa Kwankwaso yana kan hanyar cimma babban burinsa a siyasa wato ya zama Shugaban ƙasar Najeriya ba da jimawa ba!

Sai dai wannan lokaci ya fi koyaushe hatsari a rayuwar siyasar Kwankwaso, don lokacin nasara lokaci ne na hatsari kamar yadda Green ya naƙalto.

Lokaci ne na kaffa-kaffa da kula da lura, da haƙuri da juriya, da kwantar da kai, duk don cimma babbar nasara gaba.

Sai dai kash, ba a daɗe ba, aka samu varaka a rundunar Janar Kwankwaso, husuma ta faro daga Ganduje, lamarin da ƙila da tun yana ɗanye an yi wa tufkar hanci da bai girmama ba, amma ina sai sojojin runduna su kai ta kai kawo aka yi yaƙin basasa.

Daga ƙarshe abu ya zama na ƙasa, Buhari ko ya kau da kai, kamar dai yadda halayyarsa ta ke a siyasa.

A watan Yuni (June) shekarar 2018, Janar Kwankwaso ya fice daga APC ya koma tsohon gidansa na da PDP a ra’ayi na wannan, shi ne babban kuskuren da ya tava yi a siyasa. Don da dukkan alamu PDP a garin Fatakwal ta bayyanawa duniya cewa ba ta yafe masa akan abun da ya yi mata a 2015, don ƙuri’u 158 kacal ya samu a zaɓen fidda gwani.

Ƙila da ya zauna APC sannan an yi sulhu ko da na wucin gadi ne, da tabbas za a mayar masa da takarar Sanatansa, sannan a ba wa yaransa takarar Majalissu, wa ma ya sani ko ya zama Shugaban majalisar dattawa?

Ƙila da yanzu shi ne Mataimakin Shugaban ƙasa. Sai dai hujja ɗaya ce ta barins a APC kuma dai babbar hujja ce, ita ce ba a ƙimanta shi ba kamar su Tinubu. Haka ne daman, shi ma Tinubun da wahala ya samu takara, sai da aka sha yarbanci, ita harkar jam’iya haka take, Janar Kwankwaso ya fi ni sanin haka nesa ba kusa ba.

Yanzu dai ko ya sani ko bai sani ba, Tinubu ya yi amfani da takararsa ta 2023 ya cimma abin da ya ke so, sannan ga shi sun karkato kansa da qarfi a kotu, suna neman raba shi da abu mai muhimmanci wato Kano a wajensa, da alama komawarsa APC za ta yi wuya, PDP? Eh, in ya koma PDP zai samu abin da yake so, wato takarar Shugaban qasa, ko kuwa ko zai haquri ya marawa ɗan takararsu baya, ya haqura da nasa burin?

Ko zai haƙura ya haɗa kai da Obi na LP? Ko kuma zai lalubo wata jam’iyar kamar NNPP ya shiga fagen dagar shi shi kaɗai?

Ko wanne mataki ya ɗauka nan gaba kaɗan, na da muhimmanci a tarihin siyasarsa da ta faro shekaru wajen 35 ko fiye.

Mukhtar Mudi Sipikin, gogaggen ɗan siyasa ne, kuma mai fashin baƙi a harkokin siyasa da al’umma na yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.