Shari’ar siyasar Kano: Inda jami’yyar NNPP mai mulki ta kuskure

Daga ABDULAZIZ TIJJANI BAQO

A matsayina na ɗan NNPC kuma ɗan kwankwasiyya cikakke, ga mahangata a game da hukuncin da kotu ta yanke a kan shari’ar da ake tafkawa a tsakanin jam’iyyarmu ta NNPP da kuma APC.

Bayan karanta kes ɗinmu da APC daga farko zuwa ƙarshe, ba ni da wani haufi a kan cewa lauyoyinmu su suka yi mana illa a wannan kes din. Sun yi iya bakin ƙoƙarinsu. Amma kuskuren da suka yi wurin laƙantar doka ya jawo mana matsala.

Kusan gabaɗaya kariyar da suka bayar ta dogara ne da roko kotu ta yi watsi da hujjojin da APC suka bayar. Babban abin ciwon shi ne cewa, da aka zo maganar din takardun zaɓe, sai lauyoyinmu suka dogara da cewa ai APC ba su kawo shaidun gani da ido ba (irin hukuncin da na yanke a matsayina na SAN ɗin Fesbuk).

Sai dai kuma sabuwar dokar zaɓe ta riga ta bayar da damar karɓar hujjoji na takardu ko da kuwa babu shaidun gani da ido. Ko kaɗan ban tsammanci cewa idon lauyoyinmu zai makance daga wannan ƙa’idar ba. Domin kuwa in da idonsu bai makance ba, da za su bi wasu hanyoyin na ba mu kariya.

Kotu kuma abinda ta ce za ta yi amfani da shi shi ne substantive justice, (wato ma’ana ko da akwai matsaloli a kan yadda ka shigar da ƙararka in dai har kotu ta gano kana da gaskiya, to za ta baka gaskiyarka).

Dogaron da suka yi da cewa kotu za ta yi watsi da wadannan hujjojin na takardun zaɓe, saboda rashin sanin sabuwar dokar zaɓe daga A zuwa Z.

Shi ya sa ko kafan ba su ma yi yunqurin duba waɗannan takardun zaɓe din da aka kawo ko sahihai ne ko ba sahihai ba.

Ba su yi yunƙurin duba cibiyoyin kaɗa zaɓe na abubuwan da hakan ya faru ba su gano ko akwai ƙuri’un APC da su ma babu sa hannu a jikinsu.

Da wannan nake cewa, kawai dai mu ci gaba da addu’a. Har yanzu akwai kura-kurai da kotu ta gaba za ta iya ganowa daga hukuncin da wannan kotun ta yanke.

Amma in dai magana ake ta shari’ar tushe, sai dai mu ce innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Kawai dai akwai wasu abubuwa da zamu iya sa rai cewa kura-kurai ne da kotun ta yi waɗanda kotun gaba za ta iya sokewa.

Allah ya ba mu hakurin jure wannan musiba ya kuma ƙwato wa al’ummar Kano haƙƙinsu.

Abdulaziz Tijjani Baqo, Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD, mai fashin baƙi ne a kan al’amuran yau da kullum, musamman ɓangaren siyasa. Ya rubuto ne daga Amurka.
Adireshin imel: [email protected]