Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ayyana zaɓen gwamnan Kaduna ‘Inconclusive’

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Kaduna, ta ayyana zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ran 18 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba, wato ‘inconclusive.’

Kotun ta ayyana hakan ne a zaman yanke hukunci kan shari’ar da ta yi a ranar Alhamis.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Victor Oviawe ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta gudanar da zaɓen cike giɓi a cikin kwana 90.

Da wannan hukuncin, ana sa ran INEC ta sake shirya zaɓe a gundumomi bakwai a tsakanin ƙananan hukumomi huɗu kuma a rumfunan zaɓe 24 masu ɗauke da masu kaɗa ƙuri’a da aka yi wa rijista su 16,300.

Manhaja ta rawaito cewar, babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar ce ta shigar da ƙara inda take ƙalubalantar nasarar da Gwamna Uba Sani na APC ya samu a zaɓen da ya gabata a jihar.

PDP ta yi zargin zaɓen cike yake da maguɗi da danniya, tare da iƙirarin cewar ɗan takararta, Isa Mohammed Ashiru ne ya lashe zaɓen.