An shiga ruɗani game da hukuncin kotu kan shari’ar zaɓen Gwamnan Kaduna

Jama’a sun shiga halin ruɗani game da shari’ar zaɓen gwamna a jihar Kaduna.

Hakan ya faru ne bayan da wani rahoto ya nuna Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe na Gwamnan Jihar ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Bayan kimanin awa guda da fitan rahoton, sai aka sake ganin wani rahoto na daban na cewa, kotun ta tabbatar da nasarar da Gwamna Uba Sani ya samu a zaɓen wanda hakan ke nuni da shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Da yake yi wa Jaridar News Point Nigeria ƙarin haske game da hukuncin ta waya, lauyan Gwamna Sani, Ibrahim H O SAN said, ya ce rahoton farko da aka yaɗa aikin masharrantan da suka halarcin zaman kotun ne, waɗanda ke burin haifar da fitina ga zaman kotun da kuma zaman lumanar da jihar ke da ita.

“Wannan ba komai ba ne face aikin nasharranta. Kotu ta ayyana wanda nake karewa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kaduna,” in ji lauyan.

Tun da fari, rahoton da aka soma yaɗawa game da shari’ar cewa ya yi, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Kaduna, ta ayyana zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ran 18 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba, wato ‘inconclusive.’

Kotun ta ayyana hakan ne a zaman yanke hukunci kan shari’ar da ta yi a ranar Alhamis.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Victor Oviawe ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta gudanar da zaɓen cike giɓi a cikin kwana 90.

Da wannan hukuncin, ana sa ran INEC ta sake shirya zaɓe a gundumomi bakwai a tsakanin ƙananan hukumomi huɗu kuma a rumfunan zaɓe 24 masu ɗauke da masu kaɗa ƙuri’a da aka yi wa rijista su 16,300.

Manhaja ta rawaito cewar, babbar am’iyyar hamayya ta PDP a jihar ce ta shigar da ƙara inda take ƙalubalantar nasarar da Gwamna Uba Sani na APC ya samu a zaɓen da ya gabata a jihar.

PDP ta yi zargin zaɓen cike yake da maguɗi da danniya, tare da iƙirarin cewar ɗan takararta, Isa Mohammed Ashiru ne ya lashe zaɓen.